Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 31/05/2024.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, A'isha Babangida and Rabiatu Kabir Runka

  1. Tsananin zafi na ci gaba da kashe mutane a Indiya

    Rahotanni na cewa an samu mutuwar mutane da dama sakamakon tsananin zafi a Indiya. Hukumomin jihohin gabashin ƙasar, Odisha da Bihar sun ce mutane 15 ne suka rasu a ranar Alhamis, kuma suna ci gaba da bincike kan lamarin.

    An haramtawa ma'aikata zirga-zirga a tsakiyar rana.

    Ana hasashen cewa za a ci gaba da fuskantar tsananin zafi a gabashi yayin da ake hasashen za a samu sauƙin zafin a Arewa maso Yamma da kuma tsakiyar Indiya.

    • An yi rana mafi tsananin zafi a tsawon shekara 60 a China
    • Yadda Kanawa ke gudanar da sana’o’insu a yanayin tsananin zafi
  2. Aminu Ado Bayero ba zai yi sallar Juma'a a Ƙofar Kudu ba - Ƴansanda

    Rundunar ƴansanda a jihar Kano ta gargaɗi al'umma su guji yaɗa 'labaran ƙarya' da ke cewa sarkin Kano da aka sauke Aminu Ado Bayero zai halarci sallar Juma'a a babban masallacin fadar sarki da ke Ƙofar Kudu.

    Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da rundunar ƴansandar ta fitar yau Juma'a, wadda ta samu sa hannun mai magana da yawun rundunar a jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa.

    A cewar sanarwar ya kamata al'ummar jihar su yi watsi da labaran da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke cewa sarkin wanda aka sauke zai halarci sallar Juma'ar a Ƙofar Kudu kasancewar ba gaskiya ba ne.

    Haka nan rundunar ta tabbatar da cewa za ta samar da wadataccen tsaro faɗin jihar.

    Ana cikin halin ɗar-ɗar a jihar ta Kano tun bayan da Aminu Ado Bayero, wanda gwamnatin jihar ta sauke ya koma birnin na Kano bayan miƙa wa Muhammadu Sanusi II takardar kama aiki a matsayin sarkin Kano na 16.

    A ranar Juma'a 24 ga watan Mayu, 2024 Sarki Muhammdu Sanusi II ya karɓi takardar kama aiki a matsayin sarkin Kano na 16, kwana ɗaya bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar masarautar Kano ta 2024, wadda ta soke masarautu biyar na jihar.

    A shekarar 2019 ne majalisar dokokin jihar Kano ta yi dokar da ta samar da masarautun Kano, Rano, Bichi, Gaya da kuma Ƙaraye, sannan kuma daga bisani gwamnatin jihar ta sauke Muhammadu Sanusi II a msatyin sarkin Kano na 14 bayan zargin shi da rashin biyayya da kuma almundahana da kuɗi.

    • Aminu Ado Bayero ya koma Kano, gwamna ya bayar da umurnin a kama shi
    • Me zaman fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado ke nufi?
  3. An samu lauyan da zai kare mutumin da ya cinna wa masallaci wuta a Kano

    Babbar kotun shari'ar Musulunci da ke zama a Kano ta ɗage sauraron ƙarar da take yi kan wani matashi da ya cinna wa masallaci wuta a jihar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da jikkatar wasu.

    A ranar 15 ga watan Mayu ne mutumin da ake zargi a watsa fetur tare da cinna wa masallaci wuta sa'ilin da ake sallar Asuba a ƙaramar hukumar Gezawa ta jiharn Kano.

    Ya zuwa yanzu lamarin ya haifar da asarar ran mutum 19, yayin da wasu ke ci gaba da samun kulawa a asibiti.

    A lokacin zaman kotun na yau, alƙali ya bayyana cewa an samu lauyan da zai kare wanda ake zargi, inda ya buƙaci a tattara duk wasu bayanai da hujjoji da suka kamata domin miƙa wa lauyan.

    Kotun ta ɗage shari'ar ne zuwa ranar huɗu ga watan Yulin 2024.

    A zaman da kotun ta yi na farko, mutumin ɗan shekara 38 ya amsa laifin da ake tuhumar sa da shi a lokacin da kotu ta karanto masa su.

    Kimanin mutum 40 ne aka yi ƙiyasin suna cikin masallacin a lokacin da lamarin ya faru.

    Rudunar ƴansandan Najeriya a jihar Kano ta ce binciken da ta yi na farko-farko sun tabbatar mata cewa wanda ake zargin ya kai hari a masallacin ne sanadiyyar rikici game da rabon gado.

    • Yadda matashi ya cinna wa masu sallah wuta a Kano
    • 'An cinna wa masallaci wuta' a Afirka ta Kudu
  4. Harin Amurka da Birtaniya ya kashe mutum 14 cikin dare a Yemen

    Gidan talabijin na Yemen da ke ƙarƙashin jagorancin ƴan Houthi ya ruwaito cewa an kashe mutum 14 ckin dare, yayin da aka jikkata mutum sama da 30 a lokacin wani hari ta sama da dakarun hadin gwiwa na Amurka da Birtaniya suka ƙaddamar.

    Cibiyar da ke bai wa dakarun Amurka umurni ta tabbatar da kai harin wanda ta ce na ramuwar gayya ne kan mayaƙan Houthi da ke kai hare-hare a kan jiragen ruwa masu sufuri ta tekun Bahar-maliya, lamarin da ke haifar da tsaiko wajen shigi da ficen kaya a duniya.

    Cibiyar ta ce makaman da ta harba sun faɗa kan inda suka ƙuduri kai harin guda 13, yayin da aka daƙile harin jiragensu marasa matuƙa takwas.

    A ƴan watannin nan mayaƙan Houthi na kai hare-hare cikin tekun Bahar-maliya, tekun da ake amfani da shi wajen jigilar kaya a fadin duniya, harin da suka ce na nuna goyon baya ne ga Falasdinawa a Gaza.

    • Amurka ta kai harin ramuwa a kan Iraqi da Syria
    • Harin 11 ga Satumba: Abu biyar da aka koya daga hare-haren al-Qaeda na Amurka
  5. Jam'iyyar ANC ta Afirka ta Kudu na dab da rasa rinjaye a majalisar dokokin ƙasar

    Sakamakon wani ɓangare na zaben ƴan majalisar dokokin ƙasar Afirka ta Kudu ya nuna cewa jam'iyyar ANC mai mulkin ƙasar tun a shekaru 30 da suka gabata, na dab da rasa rinjaye a majalisar dokokin kasar a karon farko.

    Yayin da aka ƙidaya kashi 56 cikin 100 na gundumomin zabe, jam'iyyar ANC ce ke kan gaba da kashi 42 cikin 100, sai kuma Democratic Alliance (DA) da kashi 24 cikin 100.

    Jam'iyyar MK ta tsohon shugaban kasar Jacob Zuma ta uMkhonto weSizwe Party (MK) ta samu kashi 11 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da jam'iyyar Economic Freedom Fighters ke mara baya da kusan kaso 10.

    Ana sa ran sakamakon ƙarshe na zaɓen a karshen wannan mako.

    Sai dai na'urar da ke nuna sakamakon zaben kai tsaye ta samu cikas da safiyar Juma'a, inda ta nuna babu sakamako.

    Hukumar zaɓen dai ta nemi afuwar cikas ɗin da aka samu, daga bisani kuma na'urar ta dawo aiki, tare da tabbatar wa jama’a cewa sahihancin sakamakon zaben yana nan daram.

    Yawancin masu kada kuri'a na danganta rashin gamsuwarsu da jam'iyyar ANC da batutuwan da suka hada da cin hanci da rashawa, da laifuka, da rashin aikin yi da suka addabi kasar.

    • Manyan kalubale a zaɓen Afirka ta Kudu
    • Ƙasashen Afirka biyar masu ƙarfin tattalin arziƙi da al'ummarsu ke wahala
  6. Al'umma na tserewa daga ƙauye a Borno saboda barazanar ISWAP

    Mayaƙan ISWAP sun bai wa mazauna Kukawa lga sanarwar su bar kauyensu ko kuma su fuskanci kisa kwanaki huɗu da kashe masunta goma sha biyar a yankin Tumbun Rogo.

    Wani mazaunin garin da ya gudu daga al’ummarsa zuwa Maiduguri sa’o’i uku da samun wannan barazana, ya bayyana hakan ga gidan talabijin na Channels.

    A yayin da ya ke bayar da labarin yadda lamarin yake, mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa mayakan sun tara jama’ar al’umma daban-daban a ƙaramar hukumar da sanyin safiyar Alhamis, inda suka ce su bar gidajensu kafin ranar Asabar, in ba haka ba za a kashe su.

    A cewarsa, bayan da suka samu barazanar ‘yan ISWAP din, al’ummomin suka fara barin yankunansu, yayin da wasu suka tafi Kross Kauwa, wasu kuma suka tafi Monguno.

    Kukawa lga ƙaramar hukuma ce a gefen tafkin Chadi wadda ta shahara wajen kamun kifi da noma, kuma akwai dakarun sojojin Najeriya da na ruwa.

    Duk da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, mayaƙan Boko Haram/ISWAP na ci gaba da kai hare-hare a cikin al'ummomin.

    • Mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da mutum 160 a garin Kuchi da ke jihar Neja
    • Boko Haram da ISWAP na ƙara samun fasahohin zamani don ayyukansu
  7. Assalamu alaikum

    Barka da safiya da fatan mun wayi gari lafiya.

    Muna fatan kasancewa tare da ku a wannan safiya ta Juma'a.

    Za mu kawo muku labarai da rahotanni masu ƙayatarwa daga ko ina a sassan duniya musamman Najeriya da ƙasashe maƙwabta.

    Akwai shafukanmu na sada zumunta da za ku iya duba ƙarin labarai da kallon bidiyo.