Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/05/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 15 ga watan Mayun, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Usman Minjibir

  1. Ana zargin Facebook da Instagram da shiga ran yara fiye da kima

    Tarayyar Turai za ta binciki kamfanin sada zumunta na Facebook da Instagram kan ko suna shiga ran yara fiye da kima ta yadda suke yin mummunar tasiri ga lafiyar jiki da tunaninsu.

    Ƙungiyar za ta tuhumi kamfanin da ya mallaki mahajojin biyu kan ko ya ɗauki matakan da suka dace wajen tabbatar da cewa masu amfani da shafukan sun kai shekarun da suka kamata, da kuma irin abubuwan da ake tura wa yara a shafukan nasu.

    Yanzu haka Tarayyar Turai ɗin na tuhmar manyan kamfanonin sada zumunta kan zargin karya ƙa'idojinta masu tsauri na harkar sadarwa ta zamani, kuma ana iya cin tarar kamfanonin kimanin kashi 6% na ribar da suke samu a shekara a faɗin duniya.

    Kamfanin Meta wanda ya mallaki shafukan na facebook da instagram ya ce ya "kwashe kimanin shekara 10 yana ƙoƙarin samar da wasu tsare-tsare 50" da za su kare yara.

  2. Afirka ta Kudu na son a dakatar da Isra'ila daga kai hare-hare a Gaza

    Afrika ta Kudu ta roki kotun duniya da ta umarci Isra'ila ta dakatar da hare-haren da take kai wa Gaza, inda ta ce wannan ce dama ta karshe ta tabbatar da rayuwar Falasdinawa.

    A korafin da ta shigar na baya-bayan nan a gaban babbar kotun MDD, Afrika ta Kudu ta ce Falasdinawa na bukatar kariya daga kisan kiyashi.

    Lauyan Afrika ta Kudu ya ce Rafah ne wurin na karshe da ya rage idan kuma babu Rafah to babu sauran rayuwar Falasdinawa da za a yi magana a kai.

    A gobe Juma'a ne aka tsara Isra'ila za ta gabatar da bayani a gaban kotun. Ta kuma kafe kan cewa hare-haren da take kai wa Gaza ba su saba da dokokin duniya.

  3. Tinubu ya gana da sabon shugaban Senegal

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gana da sabon shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye, a ziyarar farko da sabon shugaban ƙasar ya kai Najeriya.

    A ranar biyu ga watan Afrilu ne aka rantsar da Bassirou Faye a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa mafi ƙarancin shekaru a Afirka bayan nasarar da ya yi a zaɓen ƙasar da aka gudanar.

    Faye ya lashe zaɓe ne bisa alƙawurra da ya yi na kawo gagarumin sauyi a ƙasar.

    Matsalar ƙarancin aikin yi da rashin kyawun tattalin arziƙi ne manyan matsalolin da ke addabar ƙasar ta Senegal.

  4. An yi watsi da ƙorafin maguɗi a zaɓen shugaban ƙasar Chadi

    Majalisar Kundin tsarin mulkin Chadi ta yi watsi da kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a wannan wata, wanda Janar Mahamat Deby ya lashe.

    Majalisar ta ce biyu daga cikin 'yan takarar sun gaza gabatar da hujjar cewa an yi magudi a zaben.

    Daya daga cikin su da ake kira Succes Masra ya ce ya gabatar da wani bidiyo da ya nuna yadda ake ta cike takardun zaben ana zubawa a akwati.

    Janar Deby ya fara jagorantar kasar ne bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Deby shekaru uku baya.

  5. Halilu Buzu: Ɗan Nijar ɗin da sojojin Najeriya ke nema ruwa-a-jallo

  6. An gano mutumin da maƙwafcinsa ya yi garkuwa da shi bayan shekara 30

    Kafafen yada labaran Algeria sun ce an gano wani mutum da ya bata kusan shekara 30 a wani dakin karkashin kasa na makocinsu.

    An sace Omar Ben Omran wanda ke wani gari mai nisan kilomita 200 daga kudancin Algiers babban birnin kasar tun yana shekara 17, a 1998.

    Iyayensa sun yi tsammanin an kashe shi ne a yankin basasar kasar ta Aljeriya.

    Ya ce ya kasa neman taimako ne saboda mutumin da ya sace shi ya masa sihiri.

    A yanzu haka dai ana can ana yi masa magani. Shi kuma maigadin da ya sace shi dan shekara 61 an kama shi da zargin sace mutum.

  7. Tankokin Isra'ila sun kashe sojojin ƙasar biyar a arewacin Gaza

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce sojojinta biyar sun mutu sakamakon harin tankar yaƙi da sojojin ƙasar suka kai arewacin Gaza, a ɗaya daga cikin munanan hare-haren da Isra'ila ta kai yankin tun bayan fara yaƙin.

    Binciken farko ya nuna cewa tankokin Isra'ila biyu sun kai hari kan wani gini a sansanin 'yan gudun hijirar Jabalia inda sojojin ƙasar suka taru.

    A wannan makon ne sojojin Isra'ilar suka koma arewacin Gaza, bayan da suka yi zargin cewa mayaƙan Hamas na sake taruwa a yankin.

    Dubban Falasɗinawa ne suka fice daga yankin sakamakon luguden boma-boman Isra'ila.

    To sai dai a ranar Laraba sojojin Isra'ila da mayaƙan Hamas suka ce faɗa ya sake tsananta a garin Jabalia da kewayensa.

    Haka kuma ana ci gaba da yaƙi a birnin Rafah da ke kudancin Gaza, inda kusan mutum 600,000 suka fice daga yankin tun bayan da Isra'ila ta fara kai hare-hare yankin kwanaki 10 da suka gabata.

    Fiye da mutum miliyan guda ne da suka rasa muhallansu sakamakon yaƙin ke samun mafaka a Rafah.

  8. 'Yan sanda sun bayar da belin mawaƙi Portable

    Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta ce an bayar da belin fitaccen mawaƙin nan ɗan Najeriya mai suna, Habeeb Okikiola, da aka fi sani da Portable.

    Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana haka ga manema labarai.

    Mai magana da rundunar 'yan sandan ƙasar, Olumuyiwa Adejobi ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar ya ce zai binciki lamarin kamun da aka yi wa fitaccen mawa.ƙin.

    Mista Adejobi ya ce 'yan sanda sun gano wasu abubuwa kan lamarin tare da gabatar da su ga kwamishin 'yan sandan.

    Mai magana da yawun 'yan sandan Legas ya ce zai tattauna batutuwan da kwamishinan 'yan sandan, yana mai tabbatar da cewe rundunar za ta ɗauki matakin da ya dace.

    An kama mawaƙin ne kan zargin ƙin biyan bashin da ake binsa a lokacin da ya sayi wata mota a hannun wani dilan motoci a jihar.

    Rahotonni sun ce ya biya naira miliyan 13 daga cikin kudin motar miliyan 27, tare da yarjejeniyar biyar ragowar naira miliyan 14 daga baya.

    To sai dai daga bisani mawaƙin ya ƙi biyan ragowar kuɗin sakamkon ƙorafin da ya yi cewa motar ta fara ba shi matsala.

    Daga nan ne dilan motocin ya kai ƙararsa wajen 'yan sanda, lamarin da ya sa aka kama Portable.

  9. Coppa Italia ne kofin farko da Juventus ta ci a shekara uku

  10. Emirates zai koma zirga-zirga a Najeriya

    Kamfanin sufurin jiragen sama na Emirates ya bayyana cewa zai koma zirga-zirga zuwa Dubai daga Legas a Najeriya, shekara biyu bayan dakatar da jigilarsa a ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da kamfanin mallakin ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya fitar, ya ce zai fara jigilar fasinja tsakanin ƙasashen biyu sau ɗaya a kowace rana daga ranar 1 ga watan Oktoba.

    “Jigila tsakanin Legas-Dubai ya kasance mafi shahara tsakanin kwastomominmu na Najeriya, don haka muna fatan dawo da wannan jigila domin kyautata wa kwastomominmu don inganta harkokin kasuwancinsu da tafiye-tafiyensu'', in ji mataimakin shugaban kamfanin Emirates Adnan Kazim.

    A watan Satumban 2022, kamfanin ya dakatar da jigila zuwa Najeriya, sakamakon tangarɗa da ta shiga tsakanin kamfanin da gwamnatin ƙasar, kan mayar wa kamfanin kuɗinsa da ya kai kimanin dala miliyan 85.

    Najeriya - wadda ta fi kowace ƙasa yawan al'umma a nahiyar Afirka - na fama da ƙarancin kuɗin waje, lamarin da ya tilasta wa ƙasar taƙaita kuɗaɗen wajen ƙasar da take bai wa masu zuba jari a ƙasar don kwashe ribarsu.

    A watan Maris ne Babban Bankin Ƙasar, CBN ya ce ya warware duka basukan waje da ake bin ƙasar da ya kai dala biliyan bakwai.

  11. 'Yan Boko Haram da na ISWAP 47 sun miƙa wuya ga sojoji

    'Yan Boko Haram da na ƙungiyar Iswap 47 ne suka muƙa wuya ga sojojin haɗin gwiwa da ke yaƙi da Boko Haram a ƙasashen yankin Tafkin Chadi.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce mutanen da suka haɗa da maza bakwai da mata 9 da ƙananan yara 31, sun miƙa kansu ne a garin Kwatan Turare da ke Doron Baga a ƙaramar hukumar Kukawa na jihar Borno.

    Sojojin sun ce binciken farko ya nuna cewa, mutanen sun tsere ne daga wani gari da ake kira Sharama da ke tsakiyar tsibirin Tafkin Chadi.

    Daga cikin mutanen da suka miƙa wuya akwai, Mallam Muazu Adamu wani fitaccen mayaƙin ƙungiyar Boko Haram ɓangaren Shekau, da ya yi aiki ƙarƙashin kwamanda Alai Gana.

    Mutanen sun shaida wa sojojin cewa suna gudanar da sana'ar noma a garin da suke kafin su yanke shawarar miƙa kansu.

    Mallam Muazu Adamu ya miƙa kansa ga sojojin tare da iyalansa

    Sojojin sun ce suna zurfafa bincike kan mutanen domin samun wasu ƙarin bayanai daga gare su.

  12. Abin da muka gaya wa masu kunna kiɗa a gidajen biki - Hisba

    Darakta Janar na hukumar Hisbah ta jihar Kano, Abba Sa'id Sufi ya ce hukumar shawarci maza masu kunna kiɗa a gidajen biki da su daian cuɗanya maza da mata a wuraren taruwar bukuwa a faɗin jihar.

    Hakan ya ci karo da wasu rahotonni da ke cewa hukumar ta haramta wa maza masu sana'ar DJn halartar bukukuwan mata a faɗin jihar.

    Abba Sa'id Sufi ya shaida wa BBC cewa shugaban hukumar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana haka, yayin wani taro da wakilan ƙungiyar masu DJn a jihar inda ya ce matakin ya zama dole a ƙoƙarin da hukumar ke yi na daƙile cuɗanya tsakanin mata da maza a wuraren taruka.

    Shugaban na Hisba ya ce ''a matsayin jihar nan ta musulunci, ba za mu bari a dinga cuɗanya tsakanin mata da maza ba a wurin taro. Saboda hakan zai kawo ƙaruwa da kuma yaɗuwar baɗala''.

    Ya ƙara da cewa a baya an yi wani taron da masu wuraren biki a jihar domin a wayar musu da kai kan dokokin da suka jiɓanci tafiyar da sana'artasu.

    Jagoran wakilan ƙungiyar masu DJ, Ibrahim Farawa wanda aka fi sani da DJ Farawa ya jinjina wa Hukumar kan gayyatarsu da kuma ba su shawarwari kan sabbin tsare-tsare da hukumar ta fitar don lura da al'amuran sana'ar tasu waɗanda suka haɗa da kiyaye lokutan sallah da kuma buƙatar hana cuɗanya tsakanin mata da maza yayin taruka.

    DJ Farawa ya yi ƙira ga dukkan masu DJ da ke jihar da su bi dokokin da hukumar ta gabatar domin guje wa aikata laifi.

    Sannan ya ƙara kira ga dukkan sana'ar da ke jihar da su yi rijista ƙarƙashin ƙungiyar domin amfana da tsare-tsaren da aka fitar.

    Ya kuma gargaɗi waɗanda suka ƙi yin hakan da cewa ƙungiyar ba za ta kare duk wanda aka kama da laifin take dokokin Hisbah ba.

  13. An ci gaba da gwabza ƙazamin faɗa a El Fasher

    Ana cigaba da gwabza ƙazamin faɗa a birnin El Fasher, mai cike da ɗimbin jama'a - tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF.

    Ƙungiyar likitoci ta 'Doctors Without Borders' ta ce tana da labarin mutuwar mutum 60 tare da raunata kusan mutum 500 tun bayan ɓarkewar rikicin a Juma'ar da ta gabata, sai dai adadin waɗanda suka mutun ka iya ƙaruwa.

    Dakarun RSF na ƙoƙarin kwace birnin wanda ya kasance ragowa kuma na ƙarshe dake hannun sojoji a yankin Darfur.

    Birnin na El Fasher yana cike da jama'a wanda mafi yawansu yaƙi ya ɗaiɗaita a wasu wuraren.

    Rahotanni na cewa RSF na cigaba da harba makamai zuwa wurare cike da jama'a daga idan suke a yankin yammacin birnin.

    Kungiyoyin agaji sun ce hukumomin Sudan sun katse intanet a yankin.

    Dakarun RSF na ƙoƙorin kwace birnin wanda shi kaɗai ne ya rage a hannun sojoji a yankin Darfur.

    Birnin na El Fasher yana cike da jama'a wanda mafi yawansu yaƙi ya ɗaiɗaita a wasu wuraren.

    Rahotanni na cewa RSF na cigaba da harba makamai zuwa wurare cike da jama'a daga idan suke a yankin yammacin birnin.

    Kungiyoyin agaji sun ce hukumomin Sudan sun katse intanet a yankin.

    Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa komai ya lafa zuwa safiyar yau duk da an kashe farar hula tare da raunata wasu.

    Asibiti ɗaya tilo da ya rage a yankin, cike yake da majinyata.

    Amurka ta ƙaƙaba wa manyan kwamandojin RSF biyu takunkumi kan zargin su da hannu a hare-haren da aka kai El Fasher.

  14. Abin da ya sa na bayar da gudummowar likkafani da tukwane - Sanata Hanga

    Sanatan da ke wakiltar mazaɓar Kano ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Rufa’i Sani Hanga ya yi ƙarin haske kan tallafin likkafani da tukwanen ƙasa da ya yi wa al’ummar mazaɓarsa.

    Cikin tattaunawarsa da BBC, Sanata Hanga ya ce abin da ya yi sadaka ce kasancewar hatta likkafanin ma yana yi wa jama’a wahala idan aka yi mutuwa.

    "Abin da ya ja hankalina shi ne, za a yi mutuwa a unguwa a zo ana neman likkafi a rasa, sai an yi karo-karo kafin a samu kuɗin sayen likkafanin, saboda talaucin da ake ciki a unguwanar'', in ji sanatan

    Ya kuma ce dama a gidansu an saba bayar da gudunmowar irin waɗanna abubuwa, irin su ƙasar burji domin toshe ƙaburbura.

    Sanatan ya ƙara da cewa ''Sai na ga yanzu yadda ake cikin wannan hali na matsin rayuwa, sai na yi tunanin cewa a baya ma ana wahalar likkafani, ina ga yanzu, sadaka ce ba wai aikin mazaɓa ba ne''.

    Al’amarin dai ya janyo zazzafar muhawara a tsakanin al’umma da ‘yan siyasa musamman a shafukan sada zumunta.

  15. Adadin waɗanda suka rasu a hari kan masallaci a Kano ya kai 11

    Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce adadin mutanen da suka mutu a harin da wani matashi ya kai wa wasu masallata a wani masallaci a Kano ya kai mutum 11.

    An yi zargin cewa matashin ya watsa fetur a masallacin tare da cinna wuta, sannan kuma ya kulle ƙofar masallacin, tare damutum kusan 40 a ciki.

    Rahotonnin sun ce matashin ya kai harin ne sakamakon rigima kan rabon gado

    Tuni dai 'yan sanda suka ce sun kama maharin mai shekara 38.

    Lamarin ya faru ranar Laraba lokacinj da mutane ke gabatar da sallar asuba a garin Larabar Abasawa da ke cikin yankin ƙaramar hukumar Gezawa a jihar.

    'Yan sanda sun ce wanda ake zargin ya shaida musu cewa ya aikata hakan ne da nufin ƙona wasu 'yan uwansa da ke cikin masallacin waɗanda rigimar rabon gado ta shiga tsakaninsu.

    “Abin da ya faru ba shi da alaƙa da ta'addanci, rigima ce da ta faru sakamakon rikicin rabon gado," in ji Baturen 'yan sandan yankin, Umar Sanda.

  16. Rashin adalci ne ya sa na fice daga PDP - Shema

    Tsohon gwamnan jihar Katsina, Barr Ibrahim Shehu Shema, ya ce rashin adalcin da ka yi masa ne ya sanya shi ficewa daga jam'iyyarsa ta PDP.

    Cikin wata tattaunawa da BBC, tsohon gwamnan ya ce ya fice daga jam'iyyar ne tun shekarar da ta gabata, bayan ta dakatar da shi tare da Ayo Fayose da Anyim Pios Ayim ba tare da bayyana musu dalilin hakan ba.

    ''Amma kuma abin haushin shi ne ni kaɗai ne a ciki aka ce an dakatar da zaɓaɓɓun shugabannin jam'iyyar daga mazaɓata'', in ji tsohon gwamnan.

    ''Kan hakan ne na rubuta takarda zuwa ga Party Chaiman na ce ba a bi ƙa'ida ba wajen dakatar da ni tare da shugabannin jam'iiyar mazaɓar tawa ba, saboda a matsayina na jigo a jam'iyyar wanda ya taɓa riƙe mukamin mataimakin jam'iyyar mai kula da jihohin arewa 19, na riƙe muƙamin shugaban kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar a lokacin, hasalima ni na bijiro da hanyoyi da dabarun ladabtarwa na jam'iyyar, amma aka wayi gari da dakatar da ni ba tare da bayyana min laifin da na aikata ba'', in ji Shema.

    ''Shi ya sa a cikin takardar da na rubuta na bayar da wa'adin sa'o'i 48 da cewa a bayyana min laifin da na aikata, ni da zaɓaɓɓun shugabannin jam'iyyar na mazaɓar har aka ɗauki matakin dakatarwar, idan ba a yi ba to zan fice daga jam'iyyar'', in ji tsohon gwamnan

    Toshon gwamnan na Katsina ya ce bayan kwana uku ne sai jam'iyyar ta ce ta janye dakatarwar da ta yi masa tare da Ayo Fayose da Anyim Pios Ayim, amma kuma ban da sauran zaɓaɓɓun shugabannin jam'iyyar da aka dakatar ɗin ba.

    Barister Shema ya ce rashin mayar da su zaɓaɓɓun shugannin jam'iyyar mazaɓar ne ya sa ya fice daga jam'iyyar.

    A baya-bayan nan ne dai, Shema ya yanki katin jam’iyyar APC a mazaɓarsa ta Shema cikin ƙaramar hukumar Dutsin-ma.

    Barr Ibrahim Shehu Shema ya mulki jihar na tsawon wa'adi biyu ƙarƙashin jam'iyyar ta PDP.

  17. Firaiministan Slovakia na ci gaba da samun kulawa a asibiti bayan kai masa hari

    An yi wa Firaiministan Slovakia, Robert Fico, aiki inda yake ci gaba da zama asibiti sa'o'i bayan da aka yi yunƙurin kashe shi.

    Mataimakin Firaiministan, Tomas Taraba ya shaida wa BBC cewa anyi aiki cikin nasara kuma ana sa ran mista Fico zai warware.

    Kafofin watsa labaran ƙasar sun ruwaito cewa firaiministan ya farfado.

    Wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda wani mutum ya yi iƙirarin kai harin.

  18. Afrika ta Kudu na son Kotun Duniya ta hana Isra'ila kai hare-hare zuwa Rafah

    A yau ne ƙasar Afrika ta Kudu za ta buƙaci kotun hukunta manyan laifuka da ke Hague da ta dakatar da Isra'ila daga kai hare-hare a Rafah.

    Afrika ta Kudu ta gurfanar da Isra'ila a gaban kotun, inda take zarginta da aikata kisan kiyashi a Gaza.

    Afirka ta Kudun ta kuma zargi Isra'ila da azabtar da Falasdinawa da yunwa ta hanyar hana shigar da kayan agaji yankin.

  19. Shugabannin ƙasashen Larabawa za su yi taro a Bahrain

    Za a fara taron ƙasashen Larabawa a Bahrain inda batun yaƙi a Gaza zai kasance mafi mahimmanci.

    Shugabannin yankin za su yi kira da a tsagaita wuta a yaƙin Gaza da aka kwashe watanni ana gwambzawa.

    Ana kuma sa ran shugabannin za su duba yiyuwar kafa ƙasar Falasdinawa, matakin da firaiminista Netanyahu ya yi fatali da shi.

    Shugabannin ƙasashen Larabawa 22 ne za su yi kira da a tsagaita wuta nan take a Gaza.

    Ƙasashen Masar da Qatar da Saudiyya sun ce taimakon da za su bayar bayan yaƙin Gaza na da alaƙa da kafa kasar Falasdinawa.

  20. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku halin da duniya ke ciki, za mu mayar da hankali kan Najeriya da makwabtanta.

    Kar ku manta manya kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.