Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. 'An raunata masu goyon bayan Iran a Iraƙi'

    Gamayyar ƙungiyoyi masu goyon bayan Iran a Iraki sun ce membobinsu da dama sun jikkata sakamakon harin da aka kai sansaninta da bama-bamai.

    Hotunan bidiyo internet sun nuna tashin wata mummunar gobara a yankin da ke makwabtaka da Iskandariya.

    Majiyoyin tsaron Iraqi sun bayyana lamarin a matsayin wani harin bam da ya rutsa da makamai da motoci. Ya yinda ake ci gaba da laluben wadanda suka samu muggan raunuka.

    A baya-bayan wasu 'kungiyar dakarun sa kai ta kaiwa jami'an Amurka hari, sai dai cibiyar tsaro ta Pentagon ta ce ba ta da hannu a harin da ba wanda ya ɗauki alhakin kaddamar da shi.

  2. Iran ta ce za ta mayar da mummunan martani idan Isra'ila ta takaleta

    Ministan harkokin wajen Iran, Hossein Amirabdollahian, ya yi gargaɗin cewa ƙasarsa za mayar da mummunan martani cikin gaggawa idan Isra'ila ta yi abin da ya saɓa wa muradunta.

    Mista Amirabdollahian ya shaida wa kafar yaɗa labaran NBC ta Amurka kasa da kwana guda bayan wani harin da ake kyautata zaton jiragen yakin Isra'ila ne suka kai Isfahan da ke tsakiyar kasar Iran.

    Wakiliyar BBC ta ce takaitaccen harin isra'ila, wanda ba ta ɗauki alhaki ba a hukumance, ya ba Iran damar sassautawa kafin daukar mataki.

    Martanin da Tehran ta yi a ranar Juma'a - wanda ta yi watsi da al'amuran da suka faru a safiyar Juma'a - ya nuna alamun za a iya kwantar da tarzoma tsakanin ɓangarorin biyu masu rikici da juna

  3. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa, barkamu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kun wayi gari lafiya, don kawo muku irin labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta da muhawara