Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah Ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Mamakon ruwan sama ya tafi da gidaje da dama a Kwara

    Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya tafi da gidaje aƙalla 35 a yankin al’ummar Igbonna da ke karamar hukumar Oyun a jihar Kwara a ranar Alhamis.

    Wannan dai na zuwa ne kwanaki uku bayan da sama da mutane 1,000 suka rasa matsugunansu sakamakon ruwan sama da aka yi a unguwar Iyara, hedikwatar karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi.

    Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle, ya tabbatarwa manema labarai afkuwar lamarin a ranar Juma’a, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.

    Adekunle ya bayyana cewa ruwan saman ya ɗaiɗaita mutane da dama wanda ya sa kuma suka rasa matsugunansu.

    Ya ce "Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a yankin Ogbonna da ke karamar hukumar Oyun ya yi mummunar illa ga al’umma. Abin ya shafi gidaje 35."

  3. Muhimmancin azumin Sitta Shawwal a Musulunci

    Malam Muhammad Mashhud, malamin addinin Musulunci a Najeriya ya ce ya kamata duk wanda ya yi azumin watan Ramadan to ya cika sa da azumin Sitta Shawwal.

    Shehin malamin ya kuma lissafa irin falalar da ke tattare da azumin na Sitta Shawwal.

  4. Sojin ruwan Najeriya sun kama waɗanda ake zargi da satar ɗanyen man fetur

    Rundunar sojin ruwan Najeriya ta kama wasu mutane biyu da ake zargin ɓarayin ɗanyen man fetur ne a jihar Bayelsa tare da kama wata babbar mota da kuma wata kirar Mazda ɗauke da lita 1,300 na mai da aka tace ba bisa ka'ida ba.

    Wani kwamandan rundunar sojin ruwan ta Najeriya, Commodore Sunday Lakan, yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a Yenagoa a ranar Alhamis, ya bayyana cewa an samu nasarar cafke mutanen ne bayan samun bayanai na sirri.

    "Nan da muka aika jami'anmu zuwa yankin, kuma da isar su ne suka kama motar da ake zargi na ɗauke da ɗanyen mai da aka sace,” inji shi.

    Sai dai ya ce lokacin da mutanen suka ga isoar jami'ansu, suka bar suka gudu, inda ya ce sun ɗauki motar zuwa ofishinsu don ci gaba da bincike.

    "Don haka, yayin da muke ci gaba da sintiri, mun kama wata mota kirar Mazda 323 ɗauke da ɗanyen mai na sata da dizel da kananzir mai kimanin lita 1,300," in ji Sunday.

    Ya kuma ce sun kama wasu mutane biyu mace da namiji waɗanda ke jigilar ɗanyen mai ɗin, inda aka tafi da su domin bincike.

  5. Harbe-harbe tsakanin ƴan sandan Ethiopia da 'yan tawayen Fano ya yi ajalin mutum uku

    'Yan sanda a Addis Ababa, babban birnin ƙasar Habasha sun ce mutum uku sun mutu bayan wani harbe-harbe tsakanin ƴan sandan da 'yan tawayen Fano masu ɗauke da makamai.

    Ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe farar hula ne yayin da sauran biyun kuma na daga cikin ƴa tawayen ne a cewar wata sanarwa da 'yan sandan suka fitar.

    ‘Yan sanda biyu sun samu raunuka.

    Lamarin ya faru ne da safiyar Juma'a a wata unguwa da ke kusa da filin jirgin saman birnin.

    Ƴan tawayen da ke dauke da makamai sun fi gudanar da ayyukansu ne a yankin Amhara na kasar inda suke fafatawa da sojoji tun watan Agustan bara.

    Wannan shi ne tashin hankali na farko da aka ruwaito a Addis Ababa dangane da tawayen Fano.

  6. Yadda ambaliyar ruwa a Rasha ta kusan nutsar da gidaje

    Ambaliyar ruwa ta afka wa birnin Orenburg na kasar Rasha, lamarin da ya sa saura ƙiris gidaje su nutse a cikin ruwa.

    Magajin garin Orenburg ya buƙaci mazauna birnin da su ƙaurace ma gidajensu saboda gudun samun rauni ko mutuwa.

    Jami'ai sun yi hasashen cewa ruwan sama a Orenburg zai kai ƙololuwa a ranar Juma'a, inda ake sa ran ambaliyar za ta yaɗu zuwa yankunan da ke maƙwabtaka da ita a cikin kwanaki da makonni masu zuwa.

    Ambaliyar ta kuma shafi Kazakhstan, inda aka kwashe mutane 100,000 daga gidajensu a cikin makon da ya gabata.

    Ambaliyar wadda aka bayyana a matsayin mafi muni cikin shekaru 80 da suka gabata, ana alaƙanta ta da cikan koguna da dama da suka haɗa da Ural, na uku mafi girma a Turai.

    Waɗannan koguna suna gudana tsakanin Rasha da Kazakhstan.

    Saurin narkewar dusar ƙanƙara tare da ruwan sama mai yawa da kuma yanayin zafi ya ƙara ta'azzara lamarin.

    Magajin garin Sergei Salmin ya yi kira da a ƙara kwashe jama'a a wasu gundumomi.

  7. Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano

    Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta fara gudanar da bincike kan al’amarin da ya biyo bayan zargin fille kan wani karamin yaro ɗan shekara shida da wani almajiri ya yi a kauyen Kanwa da ke karamar hukumar Madobi.

    Rahotanni dai sun nuna cewa almajirin mai shekaru 22 ya kashe yaron ne a kusa da wata makarantar firamare kafin ya cire kansa.

    Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Usaini Gumel ya shaida wa BBC cewa almajirin bayan ya yanke wa yaron kai ya jefa da kan a cikin wani masai.

    "A jiya ne aka wayi gari da wannan labari da ke cewa wasu masu ruwa da tsaki suka lura da cewa sun ga wani yaro a wannan ƙauye da wuƙa wanda suka ga alamun jini a jikin wuƙar kamar jinin ɗan Adam ne, Hakan ne ya sa suka zarge abin da ya sa 'yan unguwa suka cafke shi, suka tasa shi gaba, sai suka ga gangar jikin mutum inda ya amsa shi ne ya kashe shi.

    Bayan da ƴan sanda suka je, shi ne ya ja su ya kai su inda ya wurgar da kan, inda suka ga kan yaron." In ji kwamishinan 'yan sanda na Kano.

    Da BBC ta tambayi kwamishinan inda iyayen yaron da aka kashe suke, ya ce "Iyayen wannan yaron da aka kashe suna nan a cikin garin Kanwa kuma ba yadda za su yi face su rungumi ƙaddara kuma fatanmu shi ne muna yi musu ta'azziya kuma Allah ya ƙara musu hakuri."

    Ƙwamishinan ya ce almajin ya ya kashe yaron amma sai ya zama kamar kurma, ba ya amsa tambayoyin da ake yi masa ballantana su gano waɗanda ke da alaƙa da laifin da ya aikata.

    "Lokacin da aka kama almajirin da cewa asirinsa ya tonu, ba ya iya magana ko kuma ba ya iya kammala magana saboda dukan da aka yi masa kafin zuwan ƴan sanda.

    Allah ya sa a lokacin da ƴanda suka je wurin, ba a riga an kashe yaron ba, sai muka kai shi asibiti, inda likitoci suka fara aikin ceton ransa sakamakon haka ya sa ba mu iya ƙarasa masa tamboyoyi ba daga bisani kuma sai rai yayi halinsa." in ji kwamishinan.

    Kwamishinan ya ƙara da cewa damuwar ƴan sanda jihar Kano shi ne ɗaukar doka a hannu da mutane ke yi wanda hakan ke hana su samun bayanan da ya dace kuma da suke buƙata wajen binciken laifuka.

  8. An kama waɗanda ake zargi da kisan babban ɗan siyasa a Ethiopia

    An cafke mutum 13 da ake zargi da hannu a kisan fitaccen ɗan siyasar hamayya a Ethiopia Bate Urgessa kamar yadda ƴan sanda a yankin Oromia mai fama da rikici suka bayyana.

    Ƴan sandan ba su bayar da bayanai game da sunayen mutanen da ake zargi ba amma sun ce an ƙaddamar da bincike a kan kisan.

    An harbi mista Bate, wani fitaccen ɗan siyasa a jam'iyyar OLF a farkon makon nan.

    An gano gawarsa da safiyar Laraba a gefen titi a garinsu na Meki.

    Ƴan uwansa sun faɗa wa ƴan jarida cewa wasu mutane da suka yi kama da jami'an tsaron gwamnati sun ɗauke shi daga ɗakinsa na otal ranar Talata da dare.

    Gwamnati a yankin Oromia ta musanta cewa jami'anta na da hannu a kisan ɗan siyasar.

    Majiyoyi daga asibiti sun shaida wa BBC cewa akwai alamun ciwuka sanadin harbin bindiga jikin gawar mista Bate.

    An yi jana'izar sa ranar Alhamis amma ana ci gaba da neman sanin ko an gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

    Gwamnatin Amurka da Birtaniya sun nemi a gudanar da bincike mai zaman kansa game da kisan da aka yi.

    • Abin da ya sa yaƙin Ethiopia ya sake zama sabo a Tigray da Amhara
  9. Nafdac ta haramta samfurin wani maganin tari na yara a Najeriya

    Hukumar kula da inganci abinci da magunguna a Najeriya, Nafdac ta haramta amfani da maganin tari na yara da ake kira Benylin wanda kamfanin Johnson & Johnson saboda yadda gwajin da aka yi ya gano illar da ke tattare da maganin.

    Wata sanarwa da aka wallafa a shafin hukumar na intanet, Nafdac ta ce gwajin da aka yi kan maganin ya nuna cewa yana ɗauke da sinadrin Diethylene glycol da aka gano yana haddasa cututtuka a bakin dabbobin da ake gwaji a kan su.

    Ana amfani da Benylin Paediatric ne domin maganin tari da cushewar ƙirji da kuma maganin zazzaɓi da sauran matsaloli a yara ƴan shekara biyu zuwa 12.

    Sinadarin Diethylene glycol na da illa ga bil adama idan aka sha kuma yana iya janyo asarar rai. Illar shan sinadarin ya haɗa da ciwon ciki da amai da gudawa da rashin fitar da fitsari da ciwon kai da matsalar ƙwaƙwalwa da ciwon ƙoda da ka iya kai wa ga rasa rai.

    Bayanan da ke jikin maganin sun nuna maganin na kamfanin Johnson & Johnson ne, wanda yake Cape Town a Afirka ta Kudu.

    • Mene ne maganin pregabalin kuma me ya sa shansa zai iya zama hatsari?
    • 'Abin da ya sa na tuba da shan miyagun ƙwayoyi'
  10. Ana bincike kan fallasa takardun kadarorin George Weah a Laberiya

    Majalisar Wakilan ƙasar Laberiya na gudanar da bincike kan fallasa takardun bayyana kadarorin tsohon shugaban kasar George Weah ga jama'a ba tare da izininsa ba.

    Ana bukatar dukkan manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da shugabannin kasar da su bayyana dukiyar su ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Laberiya (LACC) da zarar sun hau karagar mulki.

    Ana son tabbatar da cewa jami’an gwamnati sun kauce wa rikice-rikice na son rai da tara dukiyar haram.

    Amma ba wajibi ba ne a bayyana irin waɗannan abubuwan a bai nar jama'a.

    Frank Saah Foko, wani dan majalisa a yankin ya ce "Bayyana kadarorin tsohon shugaban kasar ga bainar jama'a ba tare da izininsa ba haramun ne.

    A watan Fabrairu ne shugaba Joseph Boakai, wanda ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a watan Nuwamba inda ya kayar da Mr Weah, ya bayyana kadarorinsa a matsayin wani bangare na kudurinsa na yaƙi da cin hanci da rashawa.

    Fadar shugaban kasar ta Weah na fama da zarge-zargen cin hanci da rashawa da kuma fuskantar suka kan wuce gona da iri na manyan jami'ai.

    Bayan rantsar da Boakai a watan Janairu ne ya bukaci tsoffin jami'an da su dawo da kadarorin gwamnati da ke hannunsu "ba tare da bata lokaci ba".

    • George Weah na neman ƙarin lokaci duk da fitintinun da ke damun Liberia
    • Pandora Papers: An tona asirin wasu manyan shugabanni da attajiran duniya
  11. Mutum fiye da 2000 sun mutu a wata uku a Najeriya - Rahoto

    Wani rahoton da kamfanin tsaro na Beacon Consulting da ke Abuja ya fitar a makon nan ya nuna yadda 'yan Najeriya 2,200 suka mutu sakamakon matsalolin tsaro sannan aka yi garkuwa da mutum 2,270.

    Rahoton ya alakanta kisan jama'a da hare-haren 'yan ta'adda da masu satar jama'a da kuma ayyukan dakarun tsaro na gwamnati da na sa-kai.

    Shugaban kamfanin, Malam Kabiru Adamu ya shaida wa BBC cewa kaso fiye da 90 na alkaluman na mace-macen da sace-sacen duka a arewacin Najeriya musamman arewa maso yammaci.

    Ya kara da cewa a watan janairun wannan shekarar mun samu mutum fiye da 1000 da aka kashe, inda a watan biyu kuma aka samu fiye da 700 sannan a Maris din da ya gabata aka samu fiye da 800.

    "Mun sami wadanda suka mutum mutum 855 a watan farko, a watan biyu kuma 747 ka ga kenan an samu karin 8.71 a cikin 100. Ka ga kenan mun samu mutum dubu biyu da dan wani abu a kai kenan."

    Dangane kuma da wadanda aka yi garkuwa da su Malam Kabiru ya ce "idan kuma ka zo batun garkuwa domin kudin fansa mun samu mutum 2270."

    To sai dai ya bayar da hanyoyin da idan aka bi su to za a kai ga gaci.

    "Dole ne a samu hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnoni musamman na arewa." In ji Malam Kabiru.

    • 'Matsalar tsaro ta karu matuka a Najeriya'
    • Mutum 8,372 aka kashe kuma satar mutane ta ƙaru a 2021 a Najeriya - Rahoto
  12. Hukumar zaɓen Afrika ta Kudu ta ƙalubalanci hukuncin bai wa Zuma damar tsayawa takara

    Hukumar zaɓen ƙasar Afrika ta Kudu ta ɗaukaka ƙara zuwa kotun tsarin mulkin ƙasar bayan da alƙalan ƙasar suka yi watsi da matakin haramta wa tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma tsayawa takara a zaɓen da ke tafe a wannan makon.

    Hukumar dai ta hana shi tsayawa takarar ne bisa hujjar cewa kundin tsarin mulkin ƙasar ya haramta wa mutanen da aka yankewa hukuncin ɗaurin sama da watanni 12 a gidan yari takarar shugabancin ƙasar.

    An bai wa Zuma wa’adin watanni 15 a gidan yari bisa laifin wulaƙanta kotu a shekarar 2021, duk da cewa ya shafe watanni uku a gidan yari.

    A farkon makon nan ne, kotun zaɓen ƙasar Afirka ta Kudu ta yi watsi da hukuncin amma ba ta bayyana dalilinta ba.

    Yanzu haka dai hukumar zaɓen ta buƙaci babbar kotun ƙasar da ta bayar da ƙarin haske kan batun.

    • Jacob Zuma: Tsohon shugaban Afirka Ta Kudu ya soma zaman gidan yari na wata 15
    • An kammala kada kuri'a a babban zaben Afirka ta Kudu
  13. Jam'iyyun siyasar Mali sun yi Allah wadai da dakatar da harkokin siyasar ƙasar

    Jam'iyyun siyasa da dama da ƙungiyoyin fararen hula a ƙasar Mali sun yi Allah-wadai da umarnin da gwamnatin mulkin sojan ƙasar ta bayar na dakatar da harkokin siyasa, inda suka sha alwashin gudanar da zanga-zanga a fadin ƙasar.

    Shugaban jam'iyyar African Social Democratic Party (PSDA), Ismael Sacko, ya ce "matakin ya saɓawa kundin tsarin mulkin kasar ta Mali."

    Majalisar 'yan jaridu ta ƙasar ta bayyana damuwarta kan umarnin da hukumar kula da harkokin yaɗa labarai ta bayar na hana bayar da rahoto kan ayyukan jam'iyyun siyasa, ta kuma bukaci kafafen yada labarai da su bijirewa wannan umarni.

    A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai hukumar kula da harkokin yada labaran ƙasar ta bukaci kafafen yada labarai na kasar da su daina bayar da rahotanni kan harkokin jam’iyyun siyasa da kungiyoyi.

    Wanna na zuwa ne kwana guda bayan da hukumomin kasar suka fitar da sanarwar dakatar da duk wasu ayyuka na jam’iyyun siyasa da kungiyoyi a kan dalilan da suka sa a gaba.

    Matakin da gwamnatin mulkin sojan ta ɗauka na dakile rahotanni masu mahimmanci kan sauyin siyasa da yanayin tsaro ya janyo suka tun bayan hawanta mulki a shekarar 2020.

    Sama da jam'iyyun siyasa 80 da kungiyoyin farar hula ne suka yi kira da a gudanar da zaɓen shugaban kasa da kawo ƙarshen mulkin soja bayan ƙarewar wa'adin mika mulki da aka tsawaita a watan da ya gabata.

  14. Ukraine ta buɗe ofishin jakadanci a Congo da Ivory Coast

    Ƙasar Ukraine ta ƙara faɗada huldar diflomasiyyarta a Afirka tare da ƙaddamar da ofishin jakadancinta a Ivory Coast, bayan buɗe irin wannan ofishin a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

    Wannan matakin wani ɓangare ne na dabarun Kyiv don inganta hulɗa da tasirinta a faɗin nahiyar.

    A yayin bikin ƙaddamar da ofishin jakadanci a Abidjan, babban birnin Ivory Coast, kamfanin dillancin labaran Faransa na RFI ya ruwaito jakada na musamman na Ukraine a Afirka da Gabas ta Tsakiya Maksym Subkh, inda yake jaddada muhimmancin wannan ci gaba ga dangantakar Ukraine da Afirka.

    "An ƙara wani sabon babi mai haske a tarihin dangantakar Ukraine da Afirka da kuma Ukraine da Ivory Coast." a ranar Alhamis.

    Ya kuma yaba wa Ivory Coast bisa tsayin daka da take bai wa 'yancin kai da 'yancinta na Ukraine, musamman goyon bayan da take bai wa muhimman ƙudurori na Majalisar Ɗinkin Duniya a daidai lokacin da Rasha ke ci gaba da mamayarta a Ukraine.

    Ziyarar da jakada na musamman na Ukraine ya kai na ƙara jaddada ƙoƙarin da Kyiv ke yi na daƙile tasirin Rasha a Afirka.

    A wani mataki na mayar da martani, a baya-bayan nan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta kafa ofishin ƙaramin ofishin jakadancinta a yankin Uzhhorod na ƙasar Ukraine, wanda ya ƙara ƙulla huldar diplomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

  15. 'An sako ɗaliban jami'ar da aka sace a Taraba'

    Ɗalibai biyu daga jami'ar gwamnatin tarayya ta Wukari da ke jihar Taraba da ake zargin masu garkuwa sun sace su sun shaƙi iskar ƴanci.

    Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa an saki ɗaliban ranar Alhamis da daddare a kusa da ƙauyen Chinkai da ke ƙaramar hukumar Wukari.

    Shugabar sashen yaɗa labarai na jami'ar, Ashu Agya ce ta bayyana hakan ga Channels ta wayar tarho.

    A cewarta an biya kuɗin fansa kafin sakin ɗaliban.

    Tun farko kafar yaɗa labaran ta ruwaito cewa an sace ɗaliban da ƙarfe 10 na dare ranar 1 ga watan Afrilu a wani wajen cin abinci da ke wajen harabar makarantar.

    A ranar da lamarin ya faru, masu garkuwar sun yi ƙoƙarin sace wasu ɗaliban sai dai ba su yi nasara ba abin da ya janyo suka lakaɗawa ɗaliban da masu shagon duka tare da sace kayansu.

    Kashi 90 cikin 100 na malamai da ɗaliban makarantar na zama ne a wajen jami'ar kamar yadda shugaban jami'ar ya faɗa a bikin yaye ɗalibai da aka yi a baya-bayan nan.

    • Hatsarin yin garkuwa da matasa 'yan hidimar ƙasa a Najeriya
    • 'Yadda na tsere daga hannun su Dogo Gide bayan na haihu da su'
  16. An tura Bobrisky gidan maza har na tsawon wata shida

    Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta ɗaure Idris Olanrewaju Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky a gidan yari ba tare da wani zaɓin biyan tara ba.

    Mai shari’a Abimbola Awogboro ya yanke wa Bobrisky hukuncin watanni shida, wanda ke tsare tun bayan kama shi a makon jiya.

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC dai ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhume-tuhume shida.

    An yi watsi da tuhume-tuhume biyu, yayin da ya amsa laifin cin zarafin Naira, amma ya nemi a yi masa afuwa a matsayinsa na wanda ya fara aikata laifi.

  17. Yadda aka yi hawan Daushe a Kano

  18. Kotu ta ba da belin Emefiele kan naira miliyan 50

    Babbar kotu a Legas da ke zamanta a Ikeja ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

    Mai shari'ah Rahman Oshodi ya bayar da belin tsohon jami'in gwamnatin kan kuɗi naira miliyan 50 tare da gabatar da masu tsaya masa biyu kan irin yawan kuɗin.

    Kotun ta kuma ce dole ne mutanen biyu su zama ma'aikata sannan kuma ya zama suna da shedar biyan haraji ta shekara uku tare da gwamnatin jihar Legas.

    Alkali Oshodi ya ce dole ne mutanen da za su tsaya masa su nuna cikakkun takardun shaida sannan kuma sole ne su yi rajista ƙarƙashin tsarin karɓar beli na gwamnatin jihar Legas.

    Alƙalin ya kuma ce ya gamsu da ƙa'idar cika belin ta naira miliyan ɗaya da tun farko aka bai wa Henry Isioma-Omoli wanda shi ma yake fuskantar shari'a kan wata tuhuma gaban alƙali Olufunke Sule-Hamzat na babbar kotun Legas da ke zamanta a Yaba.

    A cewar kotun, dole ne a miƙa takardun belin ga kotun da ke sauraron laifuffuka na musamman kuma dole ne a yi rajistarsu a ƙarƙashin tsarin karɓar beli na gwamnatin jihar Legas.

    A ranar Litinin da ta gabata ne, hukumar EFCC da ke yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa zagon ƙasa ta gurfanar da Emefiele gaban kotu kan zargin tafka laifuka 26 da ke da nasaba da aikata ba daidai ba da kuma karya ƙa'ida wajen fitar da kuɗi da ya kai dala biliyan 4.5 da kuma naira biliyan 2.8.

    • Abin da ya kamata ku sani game da kama Emefiele
  19. Ɗan takarar shugaban ƙasar Ghana na adawa da masu ɗabi'ar neman jinsi

    Mataimakin shugaban Ghana, wanda kuma ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarkashin jam'iyya mai mulki ya soki masu halayyar neman jinsi inda ya ce sun saɓawa addini da kuma al'adun ƙasar.

    Wannan ne karon farko da Mahamudu Bawumia ya fito ƙarara ya bayyana matsayarsa kan masu neman jinsi - batun da a yanzu ya rarraba kan ƴan ƙasar da ke yammacin Afirka.

    A watan Fabarairu, majalisar dokokin Ghana ta amince da wani ƙudiri na haramta neman jinsi wanda ya janyo cece-kuce.

    Ƙungiyoyi da dama sun yi ta matsa wa shugaba Nana Akufo Addo lamba inda suke neman ya sa hannu kan dokar inda wasu kuma ce gargaɗin sa hannu kan dokar na iya janyo ƙasar ta rasa tallafin da take samu daga ƙasashen duniya.

    Mista Bawumia ya kuma faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa zai ci gaba da nuna adawa da masu halayyar neman jinsi idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

    Tsohon shugaban Ghana kuma babban abokin karawar mista Bawumia a zaɓen watan Disamba, John Dramani Mahama shi ma a watana Fabarairu ya soki lamarin masu neman jinsi inda ya ce ayyukansu ya ci karo da tsarin addinin mabiya addinin kirista.

    • An tanadi hukuncin ɗaurin rai da rai ga duk mutumin da ya ce mai neman jinsi ne a Uganda
    • Yadda 'yan daudu a Najeriya suka fada cikin fargaba kan ƙudirin dokar da zai sa a fara ɗaure su
  20. Ƙwararrun sojojin Rasha sun isa Nijar don horas da dakarun ƙasar

    Ƙwararrun sojin Rasha sun isa jamhuriyar Nijar domin horas da sojojin kasar, a daidai lokacin da Moscow ke ci gaba da ƙarfafa tasirinta a yankin Sahel na yammacin Afirka da ke fama da rikici.

    Ƙwararrun sojojin da suka isa Yamai, babban birnin Nijar a ranar Laraba, an gan su suna sauke kaya daga wani jirgin dakon kaya.

    “Mun zo nan ne domin horas da sojojin Nijar da kuma bunƙasa haɗin gwiwar sojoji tsakanin Rasha da Nijar,” ɗaya daga cikin ƙwararrun sojin ya shaida wa gidan talabijin na ƙasar RTN.

    Masu horas da sojojin za kuma su kawo tsarin tsaro na jirgin sama, a cewar kafar yaɗa labaran.

    Isar su Nijar ya zo ne bayan wata yarjejeniyar baya-bayan nan da aka ƙulla tsakanin sojojin Nijar da ke mulki da Rasha domin haɓaka ƙawancen tsaro.

    Nijar ta karkata ga Rasha tun bayan da sojoji suka ƙwace mulki a shekarar da ta gabata.

    Nijar ta soke daɗaɗɗiyar alaƙar diflomasiyya da tsaro da Faransa kuma kamar Mali da Burkina Faso, tana kusanta kanta ga Rasha domin samun tallafi wajen yaƙar masu iƙirarin jihadi.

    • Gwamnatin Nijar ta soke yarjejeniyar soji da Amurka
    • Me tattaunawar Putin na Rasha da shugaban Nijar ke nufi?
    • Me soke yarjejeniyar sojin Amurka da Nijar ta yi ke nufi?