Rufewa
To duka a nan muka kawo karshen shirin namu na kai tsaye. Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da BBC Hausa. Sai da safe. BARKA DA SALLAH!
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Ahmad Tijjani Bawage and Usman Minjibir
To duka a nan muka kawo karshen shirin namu na kai tsaye. Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da BBC Hausa. Sai da safe. BARKA DA SALLAH!
Rundunar yan sanda a jihar Adamawa ta ce ta kama wani mahauci mai shekara 33, mai suna Ibrahim Abubakar, mazaunin karamar hukumar Girei, da zargin kashe matarsa yar shekara 25, mai suna Hajara Sa’adu.
Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, SP Suleiman Yahya Nguroje ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.
Nguroje ya ce bayan samun korafi daga wajen mahaifin marigayiyar ce kan abin da ya faru, nan take suka kama mijin nata.
Nguroje ya ce wanda ake zargin ya tabbatar da aikata laifin da ake zarginsa da shi, kuma ya ce ya kashe matar tasa ne bayan daukar wayarsa da ta yi.
“An same ta kwance cikin jini, sai aka tafi da ita zuwa asibiti inda likitoci suka tabbatar da rasuwarta,” in ji Nguroje.
Ya kara da cewa suna ci gaba da gudanar da bincike da kuma tattara hujjoji, kafin gurfanar da shi gaban kotu.
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya gwangwaje fursunoni da ke faɗin gidajen yarin jihar da shanu da kuma kayan abinci domin su samu damar gudanar da bukukuwan karamar Sallah cikin annashuwa.
Shugabar kwamitin yin afuwa ta jihar, Azumi Namadi Bebeji wadda ta wakilci gwamnan wajen raba kayan tallafin, ta faɗa wa fursunonin cewa su ma kamar sauran al’umma suke, kada su ɗauka an yi watsi da su.
Bebeji ta tabbatar wa fursunonin cewa gwamnatin jihar ba za ta nuna gajiyawa ba wajen ci gaba da tallafa musu.
Ta yi kira ga fursunonin da su yi wa gwamnatin Abba Kabir addu’a domin ta ci gaba da samarwa jama'a ribar dimokraɗiyya.
Kwanturola na gidajen gyaran hali na jihar ta Kano, Salaiman M Inuwa ya yaba wa gwamnatin jihar bisa wannan tallafi, inda ya ce hukumar a shirye take wajen haɗa gwiwa da gwamnati a kodayaushe domin inganta tsarin yanke hukunci a jihar.
Ya ce tallafin da gwamnan ya bayar zai zaburar da fursunonin wajen bin doka da oda bayan sallamar su.
Wata babbar kotu a Kano ta saka ranar 17 ga watan Afrilu, 2024, a matsayin ranar da za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, da matarsa, da kuma wasu mutane shida kan zargin almubazzaranci.
Waɗanda ake tuhumar za a gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhume-tuhume takwas da suka haɗa da zargin karɓar cin hanci na kuɗin dala, karkatar da kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da dukiyar al'umma da kadarorin gwamnati.
A cikin takardar sammacin, sauran waɗanda ake karar sun haɗa da Abdullahi Umar Ganduje, Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd da kuma Lesage General Enterprises.
A karar da gwamnatin jihar ta Kano ta shigar a kan waɗanda ake zargi su takwas, ta ce ta haɗa shaidu 15 da za su bayyana a gaban kotu.
An tsayar da ranar 17 ga Afrilun domin fara sauraron shari'ar wanda mai shari’a Usman Na’aba na babbar kotun jiha mai lamba huɗu zai jagoranta.
Babban Lauyan gwamnatin jihar wanda kuma shi ne kwamishinan shari’a, Haruna Isah Dederi, ya tabbatar da cewa Ganduje, matarsa da wasu mutane shida za a gurfanar da Ganduje, matarsa da kuma wasu mutum huɗu a ranar da aka bayyana.
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC, ta ce ta gano Naira biliyan 30 a binciken badakalar kuɗaɗe a ma'aikatar jin kai.
Haka kuma ta ce tana gudanar da bincike kan wasu asussan banki 50 duka a cikin binciken da take yi.
Shugaban hukumar ta EFCC, Ola Olukoyede, ne ya bayyana haka, inda ya ce akwai buƙatar a kafa kotuna na musamman waɗanda za su lura da shari'oin zargin cin hanci.
Olukoyode ya ce kuɗaɗen da aka kwato na cikin asusun gwamnatin tarayya a halin yanzu.
EFCC dai na gudanar da binciken badakalar da aka samu a ma’aikatar jin kai da ta shafi ministar da aka dakatar, Betta Edu, da tsohuwar ministar ma'aikatar, Sadiya Umar-Farouq, da kuma Halima Shehu, shugabar hukumar ba da tallafin dogaro da kai ta ƙasa NSIPA.
A watan Janairu ne dai shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Edu sakamakon badakalar kuɗaɗe a ma'aikatar.
Daga nan ne EFCC ta kira ta domin amsa tambayoyi bayan fitar wata takarda da ta nuna cewa Betta ta ba da umarnin biyan sama da naira miliyan 585 cikin asusun ajiyar wani mutum, lamarin da ya saɓa da ƙa'idar aiki.
A cikin wata wasiƙa da aka yi zargin ministar ta sanya hannu, Betta ta umarci babbar akantar Najeriya, Oluwatoyin Madein ta zuba kuɗi cikin asusun wata mai suna Oniyelu Bridget, a matsayin tallafi ga ƙungiyoyin mutane masu rauni a jihohin Akwa Ibom da Cross River da Lagos da kuma Ogun.
Sai dai babbar akantar ta yi bayanin cewa, ko da yake ofishinta ya karɓi wannan buƙata daga ma'aikatar jin ƙai, amma bai yi abin da aka nema ba.
Betta Edu, 'yar shekara 37, wadda ita ce matashiya mafi ƙaranci shekaru a jerin ministocin Tinubu, daga bisani ta ce ƙulle-ƙulle ne kawai ake yi don a ɓata mata suna, ta ƙara da cewa ba za ta yi almundahana da duniyar gwamnati ba.
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta da ke aikin dakile ayyukan ta’addanci sun kai samame tare da tartwatsa sansanin wani kasurgumin dan fashin daji mai suna Yellow Janbros a kauyen Dangunu da ke karamar hukumar Maru na jihar Zamfara.
Sanarwar da sojojin suka fitar a shafin X, ta ce sun samu nasarar kashe wani da suka kira ɗan ta’adda yayin samamen.
Sojojin sun ce ɗan fashin dajin ya kware wajen yin garkuwa da mutane da kuma aikata ta’addanci a sassan arewa maso yamma yayin samamen da suka kai ranar Litinin, 8 ga watan Afrilun 2024.
“Sojojin sun ci karfin ‘yan fashin dajin inda suka samu nasarar kashe daya daga cikinsu,” in ji sanarwar sojojin.
Sun kuma ce sun kwato makamai da suka haɗa da bindigar AK-47 guda ɗaya, da harsasai da kuma buhunan hatsi 150 da ‘yan bindigar suka sace.
Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Cameron ya isa Amurka domin ƙoƙarin ganin cewa ƴan majalisar ƙasar sun amince da ƙarin tallafin dala biliyan sittin ga Ukraine.
Mista Cameron ya roƙi ƴan majalisar jam'iyyar Republican da kada su toshe tallafin sojin na Ukraine, inda ya ce tallafin na da muhimmanci ga ƙasashen yamma da tsaron Amurka.
Ana sa ran zai tattauna da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken kan batun yaƙin Ukraine da na Isra'ila da Hamas.
Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta ce mutane fiye da 3500 ne ke mutuwa a kowacce rana saboda cutar hanta, a fadin duniya, al'amarin da WHO ta ce abin tsoro ne domin adadin na karuwa.
Hukumar lafiya ta duniyar ta yi kiran da a dauki matakin da ya dace domin yaki da cutar wadda ke shafar hanta.
Ana ganin cutar da aka fi sani Hepatitis a matsayin ta biyu a cikin jerin cutuka mafi muni da saurin kisa a duniya.
Wakiliyar BBC ta ce fiye da mutum miliyan dari uku da hamsin ne a duniya ke fama da nau'in cutar hanta nau'in B ko C, wadda ke janyo kamuwa da mummunar cuta da kuma kansar hanta.
WHO ta ce kashi biyu bisa uku na masu dauke da cutar a kasashen Bangladesh da China da Ehiopia da India da Pakistan da Indonesia da Nigeria da kuma Rasha suke.
Akwai dai magunguna masu kyau da saukin kudi da ake amfani da su wajen maganin cutar, to amma har yanzu kashi uku cikin 100 masu dauke da cutar nau'in B ne kadai ke samu maganinta.
Allah ya yi wa fitacciyar 'yar Kannywood, Saratu Gidado da aka fi sani da Daso rasuwa a daren ranar Talata.
Alhassan Kwalli wanda shi ne shugaban jarumai na Kannywood ya shaida wa BBC cewa marigayiyar ta yi rasuwar fuju'a ne bayan da ta shiga daki ba ta fito ba.
"Tana zaune da iyalanta sai ta fada wa mutane cewa kowa ya je ya kwanta domin a ci gaba da ibada domin neman yardar Allah. To amma da safe ba a ga fitowarta ba har zuwa karfe daya na ranar nan ta Talata, to shi ne 'yan uwanta suka yi ta kwankwasa kofar har ta kai ga an balle kofar, inda kuma aka gan ta rai ya yi halinsa." In ji Alhassan Kwalli.
Alhassan ya kuma shaida wa BBC cewa za a yi jana'izar fitacciyar jarumar da misalin karfe huɗu na yamma, bayan yin gwaje-gwaje a asibiti.
Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta sake kashe wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne a karamar hukumar Ahoada ta Yamma da ke jihar.
Ana kyautata zaton cewa shugaban ƙungiyar mai suna Ikem Thankgod wanda aka fi sani da General 2man, na da hannu a kisan DSP Bako Angbashim.
Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta fitar a ranar Litinin, ta ce 2man da yaran gidansa sun yi artabu da ‘yan sandan dabarun yaƙi.
Ƴan sandan sun ce Thankgod ya salwantar da rayukan mutane da dama a jihar, inda ya kuma binne mutane da dama da ransu a watan da ya gabata.
"Ya yi garkuwa da mutane da dama a ciki da wajen karamar hukumar Ahoada ta Yamma. Yana fashi da makami da lalata kayyaki," in ji sanarwar ƴan sandan.
Sun kuma ce ya ɗauki kansa a matsayin hukuma, abin da ya sa ma yake far wa wuraren bukukuwan aure da kuma taron bizina da sauransu.
Masana kimiyya a Turai sun ce watan Maris ɗin da ya wuce shi ne watan da aka fi fuskantar tsananin zafi.
Masanan sun ce duniya ta kai matakin ne cikin watanni goma da aka kwashe ana samun ƙaruwar zafi.
Sun ce yawan iskar da ke ɗumama yanayi da ake fitarwa ne ke ƙara tsananta yanayin.
Ɗaya daga cikin masanan, Samantha Bajes ya ce halin da ake ciki na nuna cewa ana samun karuwar ɗumamar yanayi cikin sauri.
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ayyana ranar Alhamis 11 ga watan Afrilu, a matsayin ranar hutun Sallah a Najeriya.
Wata sanarwa da ta fito daga ma'aikatar harkokin cikin gidan ƙasar, ta kuma yi wa al'ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan.
Jami’an tsaro na musamman da ke kula da Masallacin Harami da ke birnin Makkah sun fara gudanar da bincike kan mutum da ya yi yunkurin halaka kansa, inda ya hau bene na sama na Masallacin domin ya faɗo ƙasa.
An garzaya da mutumin zuwa asibiti domin samun kulawar da ta dace, sai dai ba a bayyana ƙasar da ya fito ba.
Rundunar ta musamman mai kula da tsaron masallacin Harami ta bayyana a shafinta na X cewa “an kammala binciken da ya kamata,” amma babu wani ƙarin bayani kan lamarin.
A shekarar 2018, wani mahajjaci mai shekaru 26 ya kashe kansa a Masallacin Harami, lamarin da ya haifar da firgici da fargaba a tsakanin alhazai da masu ibada a Masallacin.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Makkah ya bayyana a watan Yunin 2018 cewa jami’an tsaro sun fara gudanar da bincike kan wani lamari, inda wani mahajjaci ya yi tsalle daga kan wani rufi a unguwar Mas’a ya kuma faɗo ƙasa, abin da ya yi sanadiyyar rasa ransa.
Shugaban Majalisar Mulkin Sojin Nijar, Janar Abdouramane Tchiani ya halarci Sallar Idi tare da tsoffin shugabannin ƙasar Mahamadou Issoufou da kuma Mahamane Ousmane.
A yau Talata ne, al'ummar Jamhuriyar Nijar suka gudanar da idin karamar sallah, abin da ya kawo karshen watan azumin Ramadan na bana.
A filin idi da ke Zone Industrielle a Yamai, babban birni ƙasr, mutane ne suka cika domin yin sallar.
Bikin sallah a ƙasar na zuwa ne bayan da hukumomi suka sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a faɗin jihohi biyar na ƙasar.
Amurka ta sake yin kira ga Isra'ila da kada ta kai farmaki birnin Rafah da ke cunkushe da ƴan gudun hijirar Falasdinawa da dama a gabashin Gaza.
Hakan na zuwa ne bayan da firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa sun fitar da ranar da za su ƙaddamar da yaƙi kan Hamas a Rafah, sai dai bai bayyana haƙiƙanin ranar da za su kai farmakin ba.
Mai magana da yawun fadar White House Matthew Miller ya ce matakin da Isra'ila ke shirin ɗauka zai cutar da farar hula.
Gwamnatin Israila da sojojinta sun ce za su yi na'am da batun tsagaita wuta, sai dai kada ya wuce mako shida.
Masu bibiyar mu a wannan shafi barkan mu da hantsin Talata.
Ku kasance da mu domin kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da mawakbtanta da kuma sauran sassan duniya.
Ahmad Tijjani Bawage ne zai kasance da ku a wannan lokaci, kafin daga bisani in miƙa ku ga abokin aikina Usman Minjibir.