Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, Usman Minjibir and Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabin labarai
Usman Minjibir tare da Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
Masallata sun cika Harami a Juma'ar farko ta Ramadan
Masallacin Harami ya fuskanci tururuwar masu ibada a ranar Juma'ar farko ta watan azumin Ramadan.
Jaridar Saudi Gazzet ta ruwaito cewa, tun da asubahin yau ne hukumomin masallacin suka riƙa shiri da gyaran harabar masallacin a shirye-shiryen gudana da sallar Juma'ar.
Da safiyar ne kuma masallata suka rika tururUwa zuwa masallacin tare da hawa sahu, inda daga baya masallacin ya cika tare da batsewa.
Domin taimaka wa masallatan hukumomi masallacin tun samar da wadatattun qur'anai da fassarar harsuna da dama ga masu buƙatar karatun qur'ani.
An kuma sanya na'urorin fassara huɗubar Juma'ar zuwa harsuna daban-daban domin masallatan su fahimci abin da ta ƙunsa
'Rikicin Sudan na bazaranar maido da masu ikirarin jihadi a ƙasar'
Sabon jakadan Amurka a Sudan ya ce ya damu game da yadda rikicin ƙasar ke barazanar dawo da ayyukan masu iƙirarin jihadi a yankin.
Tom Perriello na ziyara a ƙasashen Afirka da yanki gabas ta tsakiya, inda yake neman hanyar kawo ƙarshen yakin da ake yi a ƙasar, tare da gaggauta samar da ayyukan jin kai don tallafa wa mutanen ƙasar.
Kusan shekara guda bayan ɓarkewar yaƙi a Sudan, yaƙin ya rba mutane masu yawa da muhallansu, inda ma'aikatan agaji suka yi gargaɗin aukuwar yunwa a ƙasar.
Tom Perriello ya yi gargaɗin cewa yakin da ake yi tsakanin sojojin sudan da dakarun RSF na barazanar jefa ƙasar cikin yakin ɓangaranci, lamarin da ya ce ka iya haifar da dawowar asu ikirarin jihadi a ƙasar.
Jakadan na ziyarar ne a daidai lokacin da ake cewa Iran ta fara kai wa Sudan makamai.
A baya an sha bayar da rahoton cewa ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa na bai wa dakarun RFS makamai, wani abu da UAE din ta sha musantawa.
Sojojin Najeriya na son EFCC ta bibiyi masu ɗaukar nauyin ta'addanci
Rundunar sojin Najeriya ta bukaci Hukumar Yaki da cin Hanci da Rashawa ta Kasar EFCC, ta rika bubiyar mutanen da ta kira makiya ƙasar da ke ɗaukar nauyin ta'adanci a ƙasar.
Babban hafsan sojin ƙasar, Janar Christopher Musa, ne ya yi kiran a shalkwatar tsaro ƙasar da ke Abuja a lokacin da ya karbi baƙuncin shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede.
Janar Christopher Musa ya ce bibiyar waɗanda ke ɗaukar nauyin ta'addanci don gano su, hanya ce ƙwaƙƙwara ta yaƙi da ta'addanci a faɗin duniya, wadda sojoji ne suka gano ta.
Babban hafsan sojin ya buƙaci EFCC ta ƙarfafa wa masu riƙe da mukamai gwiwa wajen gudanar da ingantaccen shugabanci don inganta harkokin tatalin arziki da tsaron ƙasar.
Ya ƙara da cewa rundunar sojin ƙasar na aiki tare da baban kamfani mai na ƙasar NNPCL da sauran masu ruwa da tsaki a kowace rana don yaƙi da masu satar mai a ƙasar.
Wane zabi ya rage wa Najeriya wajen ceto daliban Kuriga?
Isra'ila ta rage fatan tsagaita wuta bayan martanin Hamas
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na ganin fatan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ba abu ne mai yiwuwa ba, bayan da Hamas ta bayar da abin da ta kira ''cikakken sharadinta'' ga masu shiga tsakanin.
Ofishin Mista Netanyahu na cewa buƙatar Hamas din ba abu ne mai yiwuwa ba.
Hamas na bukatar kawo karshen yakin na dindindin tare da ficewar dakarun Israila daga Gaza.
A ranar Alhamis da daddare ma'aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce kimanin mutum 20 ne aka kashe yayin da suke jiran tallafin abinci.
Sai dai Isra'ila ta musanta hannu a harin, inda ta zargi Falasdinawa masu ɗauke da makamai da kai wa dandazon jama'ar hari.
Lamarin ya faru ne a shataletalen Kuwaiti da ke wajen kudancin Zirin Gaza, wurin da ake jefa wa Falasdinawan kayan tallafin abincin da ya isa arewacin Gaza, inda MDD ta ce kananan yara na mutuwa sakamakon yunwa da rashin abinci.
Alkaluman baya-bayan nan da ma'aikatar lafiyar ta fitar, sun nuna cewa mutum 155 ne suka samu raunuka a lamarin.
Mutanen da suka jikkatan na kwance a kasa a asibitin Shifa da ke birnin Gaza, inda likitoci ke kokawa da wadanda suka samu raunuka.
Cikin wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar, ta ce ita ta bai wa manyan motocin agaji 31 damar wucewa zuwa yankin arewacin Gaza.
'Yan sanda sun kama 'ƙasurgumin' dan fashi a Legas
Rundunar ƴansandan Najeriya ta kama wani mutum da ake zargi da fashi da sace mutane a Isokoko da ke jihar Legas wanda yake ɓad-da-kama a matsayin mai matsalar ƙwaƙwala.
Cikin wata sanarwa, mai magana da yawun rundunar ƴansanda ACP Olumuyiwa Adejobi ya ce an kuma kama wani mutum a gadar Dolphin lokacin da ƴansanda ke shawagi a yankin.
An sami mutumin ɗauke da bindiga ƙirar gargajiya da wasu kayan tsubbu.
A Abuja, babban birnin Najeriya kuwa ƴansanda a wani shingen bincike a yankin Tax Park sun kama wani babur ɗauke da fasinjoji uku wanɗanɗa aka same su da bindiga da ƙunshin alburusai.
Sanarwar ta ce binciken da aka yi kuma ya sa an gano dala 5,800 na bogi da wasu kayayyaki.
Ghana za ta sake naɗa Otto Addo a matsayin kocin Black Stars
Ƴansanda sun kashe mayaƙan da suka kai hari kan otal a Somaliya
Ƴansandan Somaliya sun ce sojoji uku sun mutu a harin da ƴanbindiga suka kai kan wani otal a ƙasar.
Sun ce mutane 27 ne suka ji rauni ciki har da ƴanmajalisa uku da kakakin gwamnati.
Ƴansanda sun ce ƴanbindiga biyar ne suka kai harin kuma dukkansu an kashe su.
Hauhawar farashi ta kai kashi 31.7 a Fabarairu
Hauhawar farashin kaya a Najeriya ta kai kashi 31.7 cikin 100 kamar yadda hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta bayyana yau Juma'a.
Ƙididdigar ta kai kusan ƙarin kashi 2 cikin 100 na alƙaluman watan Jnairu.
A watan na Fabarairu, farashin abinci ne ke gaba-gaba a abubuwan da farashinsu ya yi tashin gwauron zabo kamar burodi da kifi da nama da doya da kayan itatuwa, in ji NBS.
Najeriya mai tattalin arziki mafi girma a Afirka na fuskantar ƙalubale lamarin da ya jefa mutane da dama cikin talauci saboda tsadar farashin kaya.
A watan da ya gabata, babban bankin ƙasar ya ƙara kuɗin ruwa da kashi huɗu, lamarin da ya rage hanyar riƙe tsabar kuɗi. Matakin da take ganin zai magance hauhawar farashin tare da daidaita tattalin arzikin ƙasar.
A ƴan makonnin da suka gabata ne aka gudanar da zanga-zanga a sassan ƙasar har da ƙungiyoyin ƙwadago inda suke neman ƙarin albashi mafi ƙanƙanta na naira dubu 30 da kuma sake mayar da tallafin mai da shugaba Bola Tinubu ya yi.
An bayar da rahoton fasa rumbunan abinci da motocin dakon abinci da dama a sssan ƙasar cikin watan da ya gabata yayin da mutane da dama suka yi awon gaba da masara da shinkafa da taliya.
Darajar naira ta yi ƙasa da kusan kashi 70 cikin 100, abin da ya rage wa mutane ƙarfin siyayya da kuma rashin yin tanadi.
An sami tsohon da ya fito a fim ɗin Squid Game da laifin lalata
Wata kotu a Koriya ta Kudu ta yanke wa, O Yeong-Su - mutumin da ya fito a fim ɗin Squid Game hukuncin ɗaurin tsawon wata takwas idan aka sake samun shi da yin lalata, bayan kama shi da laifin cin zarafi mai nasaba da lalata a kan wata mata.
A shekarar 2022 ne aka tuhumi ɗan fim ɗin mai shekara 79 da cin zarafin wata mata har sau biyu.
Cin zarafin ya faru ne shekara biyar da suka gabata, lokacin da O yake zama a wani yankin karkara domin shirin dirama a 2017.
O ya ce zai ɗaukaka ƙara kuma yana da mako ɗaya domin yin hakan.
Zarge-zargen su ne na rungumar matar tare da sumbatar ta a kumatu ba tare da amincewarta ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Yonhap ya bayyana.
An kuma umarci O ya halarci ajujuwa kan cin zarafi ta hanyar lalata, in ji Yonhap.
A cewar AFP, alƙali Jeong Yeon-ju ya ce shaidun matar da kuma iƙirarinta sun zamo ɗaya... kuma da alama bayanai ne da ba za ka ƙirƙira ba, ba tare da ya faru da kai ba".
O ya musanta iƙirarin wanda a cewar kotun yankin Suwon, ya faru a kan hanya kuma a gaban maƙwabtan matar.
Ɗan fim ɗin ya yi suna ne a duniya bayan da ya fito a fim ɗin Squid Game inda mutane ke shiga wasannin yara na gargajiya da mutum ke rasa ransa idan bai yi nasara ba.
Fim ne da ya yi tashe sosai a Netflix - inda fiye da mutum miliyan 100 suka kalla a faɗin duniya cikin makonni bayan fitar da shi a 2021.
Abin da ya sa aka samu katsewar intanet a sassan Afirka
Lalacewar wayoyin ƙarƙashin teku a sassan gabashi da yammacin Afirka lamarin ya sa ƙasashen Afirka da dama fuskantar gagarumar matsalar katsewar sadarwar intanet a ranar Alhamis.
Afirka ta Kudu da Najeriya da Ivory Coast da Laberiya da Ghana da Burkina Faso na cikin ƙasashen da suka fuskanci yankewar intanet ɗin.
Hukumar sadarwa ta Najeriya ta tabbatar da katsewar. Cikin wata sanarwa, NCC ta ce wayoyin da abin ya shafa sun taso ne daga Turai suka bi ta Gaɓar ruwan gashin Afirka.
Sun yanke ne a tekun maliya lamarin da ya shafi sauran wayoyin da ke haɗe da su a ƙarƙashin tekun.
"Kamfanonin wayoyin - WACS da ACE a gaɓar ruwan yammacin Afirka daga Turai sun fuskanci matsala.
NCC ta ƙara da cewa yankewar wayoyin ta sa an samu matsalar katsewar intanet a Najeriya da wasu ƙasashen yammacin Afirka sannan ƙarfin network na kamfanonin sadarwa ma ya fuskanci targarɗa a ƙasashen.
Shugaban ƙungiyar kamfanonin sadarwa a Najeriya Gbenga Adebayo ya tabbatar da matsalar da wayoyin ƙarƙashin tekun suka samu a tekun maliya.
MTN, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin sadarwa a Najeriya ya fitar da sanarwa inda ya nemi afuwar abokan hulɗarsa saboda rashin ƙarfin network da suke fuskanta.
Shi ma ya ce hakan ta faru sakamakon lalacewar wasu sayoyin ƙarƙashin teku a sassan gabashi da yammacin Afirka.
Wasu bankuna a Najeriya suma sun nemi afuwar abokan hulɗarsu saboda matsalar da suka fuskanta.
A Ivory Coast, ƙarfin sadarwar intanet ya ragu zuwa kashi huɗu cikin ɗari da safiyar ranar Alhamis a cewar Netblocks, kamfanin da ke bibiyar ƙarfin intanet.
A Laberiya ma ƙarfin intanet ɗin ya ragu zuwa kashi 17 cikin 100, a Benin kuma ya tsaya kan kashi 14 sai Ghana da kashi 25 kamar yadda Netblocks ya nuna.
Labarai da dumi-dumi, Jadawalin gasar Europa
Zagayen kwata fainal
- AC Milan v Roma
- Liverpool v Atalanta
- Bayer Leverkusen v West Ham
- Benfica v Marseille
Zagayen kusa da ƙarshe
- Benfica ko Marseille v Liverpool ko Atalanta
- AC Milan ko Roma v Bayer Leverkusen ko West Ham
Jadawalin gasar Champions League
Zagayen kwata fainal
- Arsenal v Bayern Munich
- Atletico Madrid v Dortmund
- Paris St-Germain v Barcelona
- Real Madrid v Manchester City
Zagayen kusa da ƙarshe
- Atletico Madrid ko Borussia Dortmund v Paris St-Germain ko Barcelona
- Arsenal ko Bayern Munich v Real Madrid ko Manchester City
Al-Shabab ta kai hari kan otal kusa da fadar shugaban ƙasa
Mayaƙan ƙungiyar al-Shabab sun kai hari wani otal kusa da fadar shugaban ƙasar Somaliya da ke Mogadishu, babban birnin ƙasar.
Ƙungiyar da ke iƙirarin jihadi ta taɓa kai hari otal ɗin na Syl wanda fitaccen wuri ne ga jami'an gwamnati.
Shaidu sun ce sun ji ƙarar fashe-fashe da harbe-harbe daga otal ɗin, kamar yadda suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Kafafen yaɗa labarai da ke da alaƙa da ƙungiyar sun ce ƴanmajalisar dokokin Somaliya huɗu sun ji rauni. Gwamnati ba ta ce komai ba.
Al-Shabab yun farko ta ce mayaƙa sun ƙwace iko da otal ɗin kuma suna harbin "ma'aikata da jami'an gwamnati".
Wani mazaunin babban birnin Farah Ali, wanda ke zama kusa da fadar shugaban ƙasar ya faɗa wa Reuters cewa; "Da farko mun soma jin wata ƙara sai kuma aka fara musayar bindiga. Mun san mayaƙan suna cikin otal ɗin saboda mun ji musayar wuta."
Hassan Nur wanda ya tsere ta hanyar haura katanga, ya ce; "Ban san yawan mutanen da suka mutu ba amma akwai mutane da yawa a ciki lokacin da aka fara kai harin."
A shekarar 2022, ƙungiyar ta mamaye otal ɗin Villa Rays da ke babban birnin ƙasar inda ta kashe aƙalla mutum 14.
Shekara uku kafin kai hari a otal din na Villa Rays, kimanin mutum 26 har da sanannen ɗan jarida da ƴan ƙasar waje da dama aka kashe a wani hari kan otal ɗin Asasey da ke yankin Kismayo, mai tashar jirgin ruwa a kudancin Somaliya.
- Masu mayafi da ke yaƙar mayaƙan al-Qaeda da al-Shabab a Somaliya
- Mummunar ambaliyar da ta shafe wani gari a tsakiyar Somaliya
An kama sojin haya 14 da ke yi wa dakarun RSF aiki a Sudan
Sojojin Sudan sun kama mutum 14 ƴan Sudan ta Kudu da ke cikin dakarun RSF a birnin Omdurman, kamar yadda jaridar Sudan Tribune ta bayyana.
An kama su ne a ranar 12 ga watan Maris a wani samame da ya kai ga sojoji ƙwace iko da hedikwatar kafafen yaɗa labaran ƙasar.
"Wata majiyar tsaro ta sanar da Sudan Tribune cewa a lokacin samamen ƙwace kafafen yaɗa labaran, wadda ta zama babbar cibiyar RSF a Omdurman, sojoji sun kama sojojin haya 14 daga Sudan ta Kudu.
Gwamnatin soji a Sudan ta zargi RSF da hayar mayaƙa daga wasu yankunan Afirka, zargin da ƙungiyar ta musanta.
An soma zaɓen shugaban ƙasa a Rasha
An fara zaɓen shugaban ƙasa a Rasha wanda ake ganin Vladmir Putin ka iya sake lashewa don mulkar ƙasar tsawon ƙarin shekara shida.
Za a yi kwanaki uku ana kaɗa ƙuri'a duk da cewa babu wata tantama kasancewar Putin ba shi da wani abokin hamayya da ke masa barazana.
An buɗe rumfunan zaɓe a Kamchatka Peninsula da ke gabashin Rasha da ƙarfe 8 na safe agogon can kuma za a rufe a Kaliningrad da ke yammacin ƙasar da ƙarfe 8 na dare a ranar Lahadi.
A wani taron karrama sojoji da aka yi a watan Disambar bara ne Vladmir Putin mai shekara 71 ya shaida wa al'ummar Rasha cewa zai sake neman takarar shugaban ƙasa karo na biyar.
Sojoji sun kashe ƴan bindiga a jihar Taraba
Sojojin Najeriya daga runduna ta shida sun kashe ƴanbindiga biyu a wani samame da suka kai a ƙaramar hukumar Bali da ke jihar Taraba.
Rundunar ta ce sojojinta ne suka kai samamen bayan samun bayanan sirri game da kasancewar ƙungiyoyin ƴanbindiga a yankunan Nayinaya da Garin Daniel da Garbatau.
A cewar rundunar, sojojin sun yi fito na fito da ƙungiyoyin ƴanbindigar inda suka yi nasarar kashe biyu daga cikin su tare fa ƙwato muggan makamai - bindigogi da kuma alburusai.
Rundunar ta ce tana ci gaba da gudanar da aiki tuƙuru domin fatattakar ƴanbindiga da masu aikata miyagun laifuka a jihar har sai an samar da zaman lafiya da tsaro a yankin.
Kwamandan runduna ta shidan ya yaba wa sojojin bisa ƙoƙarin da suka yi inda kuma ya yi kira ga jama'a da su samar da bayanai a-kai-a-kai da za su kai ga murƙushe miyagu.
Gwamnati na ƙoƙarin ƙara yawan jami'an tsaro a Najeriya – Sanata Ƴar'adua
Sanata Abdulaziz Yar'adua ya ce gwamnatin Najeriya ta ce tana aiki domin ara yawan jami'an tsaro domin ƙara murƙushe ayyukan miyagu da ke ƙaruwa a ƙasar.
Najeriya dai na fama da ayyukan ƴanbindiga da sace-sacen jama'a da kuma satar mai da sauran laifuka.
Sanata Yar'adua mai wakiltar Katsina ta tsakiya ya koka kan adadin jami'an tsaron da ke Najeriya wanda a jumulla ba su kai ko miliyan ɗaya ba a ƙasar da ke da yawan mutum miliyan 220.
Ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan Talabijin na Channels inda ya ce gwamnati tana ƙoƙari domin gyara hakan.
Sanata Yar'adua wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sojoji ya ce "dole mu gane cewa muna da matsala da ƙarfin yansanda da sojoji da sauran jami'an tsaron da muke da su."
A cewarsa, baya ga rashin isassun jami'an tsaro, rashin ci gaba shi me wani abu ne da ke janyo ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya.
- Shin tallafin Amurka zai iya magance matsalar tsaro a Najeriya?
- Sace-sacen ɗalibai a makarantu 10 da suka girgiza Najeriya