Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir and Abdullahi Bello Diginza

  1. Najeriya da wasu kasashen Afirka sun fuskanci matsalar katsewar internet

    Wasu kasashen Afirka biyar ciki har da Najeriya sun fuskanci matsalar katsewar intanet.

    An samu rahotonnin katsewar intanet din a kasashen Afirka ta Kudu da Najeriya da Ivory Coast da Laberiya da Ghana da kuma Burkina Faso.

    To sai har ya zuwa yanzu ba a bayyana dalilin katsewar intanet din ba

    "An samu bambanci dangane da lokacin katsewar intanet din, wanda ya faro daga arewa zuwa kudancin Afirka'', in ji Cloudflare Radar, wani da ke samar da bayanai kan sadarwar intanet.

    Sadarwar intanet a kasar Ivory Coast ya ragu da kashi hudu da safiyar ranar Alhamis, kamar yadda kamfanin Netblocks, wanda ke lura da tsaron intanet da sadarwar intanet.

    A Laberiya kuma an samu raguwar da kashi 17, yayin da a Benin ya ragu da kashi 14, Ghana kuma 25, kamar yadda Netblocks ya bayyana.

    A Afirka ta Kudu, Vodacom ya ce "Abokan huldarmu na fuskantar matsalar katsewar intanet sakamakon matsalar wani kebul da ke karkasin teku".

    Shi ma kamfanin Cloudflare ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa yana fuskantar babbar matsalar katsewar intanet a Gambiya da Guinea da Liberia da Ivory Coast da Ghana da Benin da kuma Jamhuriyar Nijar.

    Kamfanin Microsoft, ya ce za a dauki tsawon sa'o'i 12 kafin ya iya dawo da zirga-zirgar intanet ga abokan cinikinsa.

    A watan da ya gabata, an sami yanke igiyoyi da yawa a cikin Bahar Maliya wanda ya shafi kusan kashi 25% na bayanan da ke gudana tsakanin Asiya da Turai.

    An nuna damuwa game da igiyoyin da mayakan Houthi da ke aiki a tekun Bahar Maliya ke kaiwa hari. Sai dai sun musanta kai hari kan layin.

    An sha samun katsewar wayoyin sadarwar Internet na karkashin ruwa a baya, amma da alama a wannan karon lamarin babba ne, inji Isik Mater, daraktan bincike na cibiyar ta Netblocks.

  2. Yadda ake sarrafa kayan kwalam na “quesadilla”

    Wannan shiri ne da BBC Hausa take kawo muku tsawon watan azumin Ramadan, don bai wa mutane damar gwangwaje basirarsu ta girki.

    A wannan bidiyo, za ku ga yadda ake sarrafa kayan kwalam na 'quesadilla' wanda ake yi da burodin 'Totilla' da kaza.

    Wannan nau'in abincin dai an fi sanin sa a tsakanin mutanen kasar Mexico.

  3. Yar’Adua ya zama sabon shugaban kungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya

    Kungiyar sanatocin arewacin Najeriya ta nada Sanata Abdulaziz Musa Yar'adua da ke wakiltar Katsina ta tsakiya a zauren majalisar dattawan kasar a matsayin sabon shugaban kungiyar.

    Yar’Adua, wanda dan jam'iyyar APC ne - ya zama sabon shugaban kungiyar kwanaki biyu bayan saukar Sanata Abdul Ahmed Ningi - wanda dan jam'iyyar hamayya ta PDP ne - daga shugabancin kungiyar bayan da majalisar ta dakatar da shi wata uku.

    Sanata Ningi, wanda ke wakiltar Bauchi ta Tsakiya a majalisar dattawan kasar, ya zargi gwamnatin kasar da yin cushen naira tiriliyan 3.7 a kasafin kudin kasar.

    Haka kuma kungiyar sanatocin arewacin kasar ta kuma nada Sanata Tahir Munguno daga jihar Borno a matsayin mai magana da yawun kungiyar.

    Sanata Munguno -wanda dan jam'iyyar APC ne - ya maye gurbin Sanata Kawu Sumaila na jam'iyyar NNPP daga jihar Kano.

    A lokacin da majalisar ta dakatar da Sanata Ningi dai, ta gargadi sanata Kawu Sumaila da dakatar da yada sakonnin da za su iya haddasa fitina a kasar.

    • Jam'iyyun hamayyar Najeriya na martani kan dakatar da Sanata Ningi
    • Dalilin da ya sa majalisa ta dakatar da Sanata Abdul Ningi
  4. Majalisa ta yi karatu na biyu ga kudirin bai wa daliban Najeriya bashin karatu

    Majalisar wakilan Najeriya ta yi karatu na biyu ga kudirin bai wa daliban kasar rancen kudi domin karatu.

    Majalisar wadda ta yi hakan a zamanta na ranar Alhamis, ta ce kudirin na son samar da wata hukuma wadda za ta rinka bai wa dalibai rancen kudi domin karatun makarantun gaba da sakandare .

    Kafin dai tattaunawa kan kudirin, sai da shugaban majalisar wakilan, Abbas Tajuddeen ya fara da karanta wasikar da shugaba Tinubu ya aikewa da majalisar da ke neman goyon bayan majalisar wajen tabbatar da inganta rayuwar daliban Najeriya.

    Kafin nan dai shugabannin kungiyar daliban Najeriya sun fara kun far baki wajen neman dalilin da ya sa har yanzu ba a tabbatar da kudirin ba, inda suke kwatanta al'amarin da sun gaji da gafara sa ba su ga kaho ba.

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya saka wa dokar bai wa daliban kasar na manyan makaratun da suka fito daga gidajen masu karamin karfi damar samun rancen karatu maras ruwa daga gidauniyar bayar da bashin karatu ta kasar.

    • Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya
    • Ko bashin karatu na gwamnatin Najeriya zai magance matsalar ilimi?
  5. 'Yan ci-rani 60 sun mutu bayan kifewar jirginsu a tekun Mediterranean

    Akalla 'yan cirani 60 ne suka mutu bayan kifewar jirgin ruwa a tekun mediterranean, kamar yadda wadanda suka kubuta a jirgin suka bayyana.

    Jirgin agaji da kungiyar agaji ta SOS a tekun Méditerranée ya debo ragowar mutane 25 da suka rayu.

    Mutanen sun shaida wa masu ceton cewa sun taso ne daga Zawiya a gabar tekun Libya kwana bakwai da suka gabata.

    Injin jirgin ruwan ya samu matsala ne kwana uku bayan jirgin ya tashi inda ya rika garari a kan ruwa ba tare da an sarrafa shi ba kuma babu abinci ko abin sha.

    Cikin wadanda suka mutu akwai mata da kuma akalla yaro daya.

    Kungiyar agajin ta SOS Méditerranée ta ce a ranar Laraba tawagar masu ceton sun gano jirgin ne bayan amfani da na'ura mai hangen nesa sannan sun tsara kwashe mutanen tare da hadin gwiwa da masu kula da gabar tekun Italiya.

    Ta kuma kara da cewa an samu mutanen cikin mawuyacin hali kuma yanzu haka suna karkashin kulawar lafiya.

    Kungiyar ta kara da cewa helikofta ya zo ya dauki mutum biyu da suka fita hayyacinsu daga cikin marasa lafiyar domin basu kulawa sosai.

    A satin daya gabata kungiyar shiga da fice ta duniya-IOM ta ce shekarar 2023 ta kasance wadda aka fi samun mutuwar masu hijira a gomman shekaru inda aka samu mutuwar akalla mutane 8,565 a hanyoyin hijira dake fadin duniya.

    Rahoton IOM ya nuna cewa hanyar Mediterranean ta kasance hanya mafi hadari tare da samun mace-mace akalla 3,129 a shekarar 2023.

  6. 'An ce in kashe ɗana saboda na haife shi babu hannu'

  7. Hukumar Shige da Ficen Najeriya ta bayar da umarnin bude iyakokin kasar da Nijar

    Shugabar hukumar shige da fice ta Najeriya, Kemi Nanna Nandap ya bayar da umarni da duka jami'an hukumar da ke kan iyakokin jihohin kasa da suka yi iyaka da jamhuriyar Nijar su tabbatar da bin umarnin shugaban kasar na bude kan iyakokin kasar da jamhuriyar Nijar.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, ACI Kenneth Kure ta fitar, ya ce umarnin biyayya ce ga umarnin shugaban kasar Bola Tinubu na budekan iyakokin kasar da Jamhuriyar Nijar, a wani mataki na dage wa Nijar din takukuman ta kungiyar Ecowas ta kakaba mata.

    ACI Kenneth Kure ya yaba wa jami'an hukumar shige da ficen kasar dangane da sadaukarwar da suke yi wajen tsare martabar iyakokin kasar

    A ranar Laraba ne shugaban kasar Bola Tinubu ya bayar da umarnin bude kan iyakokin kasar, da jamhuriyar Nijar tare da agewa Nijar din takunkuman da Najeriya ta kakaba mata sakamkon juyin mulkin da sojojinkasar suka yi.

  8. Matan Darfur sun zargi dakarun RSF da yi masu fyaɗe – Rahoto

    Mata a Geneina da ke Yammacin Darfur a Sudan sun ce mayaƙan da ke da alaƙa da dakarun RSF sun ci zarafinsu ta hanyar lalata saboda ƙabilarsu, kamar yadda jaridar Guardian ta Birtaniya ta ruwaito.

    An shafe kusan shekara ɗaya ana gwabza yaƙi tsakanin dakarun RSF da sojojin Sudan lamarin da ya jefa al'ummar ƙasar cikin matsalar jin ƙai.

    Yaƙin ya soma ne a Khartoum amma ya bazu zuwa sassan ƙasar har da yankin Darfur.

    An soma cin zarafin ne a Geneina bayan samamen da aka kai wa tawagar sojojin a watan Nuwamba.

    Akasarin waɗanda aka yi wa fyaɗen sun fito ne daga yankin Masalit, in ji ƴarjarida Zeinab Mohammed.

    Ta bayyana su a matsayin ƙabilar da ke da launin fata baƙi.

    Ana zargin waɗanda suka yi aika-aikar larabawa ne mayaƙa amma sarakunan gargajiya sun musanta hakan, a cewar Guardian.

  9. Likitocin Kenya sun fara yajin aikin mako ɗaya

    Likitocin Kenya sun shiga yajin aiki na tsawon mako ɗaya saboda jinkirin da gwamnati ta yi na tura likitoci masu neman sanin makamar aiki.

    Suna kuma kokawa kan mummunan yanayin aikinsu da suka ce suna aiki a cikinsa.

    Kotun ma'aikata ta bayar da umarnin a dakatar da yajin aikin domin bayar da ƙofar tattaunawa. Alƙali ya buƙaci minsitan ƙwadago ya tattauna da ƙungiyar likitocin domin nemo maslaha.

    Sai dai ƙungiyar ta ce ba ta samu umarnin kotun ba. Kenya dai na fuskantar gagarumar matsala a ɓangaren kula da lafiyar al'umma.

    Da wannan yanayi na yajin aikin likitoci, marasa lafiyar da ke buƙatar kulawa za su shiga wani hali.

    Tun watan Janairu dai ba a tura likitoci masu neman sanin makamar aiki wuraren da za su yi aiki ba. Likitocin su ne waɗanda suka gama samun horo da kuma buƙatar su yi aiki tsawon shekara ɗaya kafin su samu lasisin aiki.

    Ma'aikatar lafiya ta ce ba ta da isassun kuɗin da za ta biya su.

  10. Za a kama 'yan Afrika ta Kudu da ke yaƙi a Isra'ila - minista

    Ministar harkokin wajen kasar Afirka ta Kudu Naledi Pandor ta bayyana cewa, za a kame 'yan kasarta da ke yaki a zirin Gaza tare da Dakarun tsaron Isra'ila yayin da suka koma kasar, in ji kamfanin dillancin labaran AP.

    "Na riga na fitar da sanarwar gargadi ga yan Afrika ta kudu da suke yaki... a shirye mu ke. In kuka zo gida zamu kama ku", ta fadi hakan ne yayin taron nuna goyon baya ga Falasdinawa a farkon makon nan.

    Ba a bayyana adadin mutane nawa wannan zai iya shafa ba.

    Afrika ta kudu ta riga tayi gargadi a shekarar da ta gabata kan cewa yan kasar zasu iya fuskantar hukunci in suka yi fada tare da sojin Isra'ila.

    Jaridar Haaretz a ranar Larabar da ta gabata ta nakalto sanarwar sojojin tana cewa "Dakarun sojin Isra'ila na kokarin samar da tsaro da kuma cika dukkanin wasu ka'idoji da ya kamata ace an cika su a lokacin da sojoji ke tafiya zuwa ƙasashen waje.

    Dakarun tsaron Isra'ila na sa ido kan lamarin a kai a kai, tare da hadin gwiwar hukumomin gwamnatin da abin ya shafa."

    Afrika ta kudu dai na kan gaba cikin kasashe masu sukar yakin da isra'ila ke yi a Gaza wanda ya samo asali sakamakon kisan mutane sama da 1,200 tare da yin garkuwa da wasu fiye da 200 a watan Oktoba.

    Kasar ta shigar da kara a kotun duniya domin duba ko Isra'ila na aikata kisan kiyashi kan Falasdinawa a Gaza.

  11. An sace mutane sama da 600 cikin mako ɗaya a Najeriya

    • Ƴan Boko Haram sun sace gwamman mutane a Ngala na jihar Borno
    • 'Rashin haɗin kan gwamnatoci dama ce ga 'yan bindiga'
  12. Hukumar kwastam a Sokoto da Zamfara ta saki motoci 15 na hatsi da aka kama

    Hukumar Kwastam shiyyar Sokoto da Zamfara, bisa bin umarnin da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayar na inganta samar da abinci, ta bayar da izinin sakin manyan motoci 15 da aka kama maƙare da hatsi ga masu su a ranar 12 ga Maris, 2024.

    Wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami'in hulɗa da jama'a na Hukumar a shiyyar, ta buƙaci ‘yan kasuwa da su gaggauta sayar da hatsin a kasuwannin Najeriya, yana mai jaddada ƙudurin hukumar na yaki da ayyukan fasa-kwauri.

    Bugu da kari, Kwanturola Kamal ya sanar da kokarin hadin gwiwa tare da hukumar tattara bayanan sirri na Kwastam (CIU) da kuma kungiyar hadin gwiwa (JBPT) domin sanya ido kan yadda ake rarraba wadannan hatsi a kasuwannin cikin gida, tare da tabbatar da cewa ba za su samu hanyar fita daga ƙasar ta hanyoyin fasakwauri ba.

    A nasa ɓangaren, sakataren kungiyar masu sayar da hatsi ta Sokoto Dahiru Ladan, ya nuna jin dadinsa ga shugaba Tinubu bisa tausayawar da ya yi, ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa ƙungiyar za ta tabbatar da cewa an sayar da hatsin a kasuwannin Najeriya kadai.

    • 'Farashin kayan abinci zai ci gaba da tashi a Najeriya'
    • Hukumar Kwastam: 'Al'umma ke taimaka wa ɓata gari wurin shigo da kwayoyi'
  13. Daga ina TikTok ya samo asali kuma me ya sa yake haifar da cece-ku-ce?

  14. Haɗakar jam'iyyun siyasar Sudan na shirin ƙulla yarjejeniya da sojoji

    Wata gamayyar jam'iyyun siyasa ta Sudan mai suna National Forces Coordination (NFC) karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar mulkin kasar Malik Agar, na shirin rattaba hannu kan wata yarjejeniya da sojojin kasar bayan ƙwace hedikwatar gidan talabijin da gidan rediyon gwamnati da ke Omdurman daga hannun dakarun RSF.

    NFC ta ƙunshi tsofaffin ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da jam'iyyun siyasa da ƙungiyoyin jama'a, da ƙungiyoyin siyasa, da nufin warware rikicin siyasar da rikici tsakanin sojoji da RSF ya haifar da kuma kafa gwamnatin riƙon ƙwarya

    Wannan matakin dai ya biyo bayan wata yarjejeniya a baya da wata gamayyar kungiyar hadin gwiwa ta Civil Democratic Forces (Taqaddum) karkashin jagorancin tsohon firaminista Abdalla Hamdok, ta kulla da kungiyar RSF.

    Kakakin NFC Mustafa Tambour ya tabbatar da goyon bayan kungiyar ga sojojin ƙasar a yaƙin da suke yi da RSF a wata ganawa da shugaban kasar Sudan Abdel Fattah Burhan.

    • Abun da ya kamata ku sani kan yarjejeniyar Isra'ila da Masar wadda ke fuskantar barazana
    • Rikicin Sudan: Ana jin harbe-harbe duk da yarjejeniyar tsagaita wuta
  15. Al-Shabab ta nesanta kanta da kamfanonin da Amurka ta ƙaƙabawa takunkumi

    Ƙungiyar Al-Shabab da ke Somaliya ta musanta alaƙa da mutane da kamfanonin da baitul malin Amurka ya ƙaƙabawa takunkumi saboda zarge-zargen cewa suna almundahanar kuɗi domin ɗaukan nauyin ƙungiyar mai alaƙa da al-Qaeda.

    Baitul malin Amurkan a ranar 11 ga watan Maris ya sanar da takunkuman kan kamfanoni 16 da mutanen da ake zargi da tallafa wa ƙungiyar mayaƙan ta hanyoyi da dama.

    Cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar 13 ga watan Maris, al-Shabab ta musanta sanarwar ta baitulmalin Amurka inda ta yi zargin cewa wasu mutane da kamfanoni da aka bayyana su a matsayin masu almundahana a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da gabashin Afirka suna aiki bisa buƙatun ƙungiyar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa ƙungiyar har yanzu tana musantawa tare da nanata cewa ba za ta bari a yi amfani da sunanta ba wajen cin zarafin musulmin da ba su ji ba su gani ba tare da kwashe dukiyoyinsu.

    Al-Shabab ba ta cika fitowa ta yi magana ba kan takunkuman da Amurka ta ƙaƙaba kan kamfanonin da ke da alaƙa da ita.

    A shekarar da ta gabata, baitulmalin Amurkan ya saka takunkumi akan mutane da kamfanoni aƙalla 26 da ta zarga da tallafa wa ƙungiyar da kuɗi.

    • Masu mayafi da ke yaƙar mayaƙan al-Qaeda da al-Shabab a Somaliya
    • Harin bam ya kashe mutum tara ƴan gida ɗaya
  16. An ƙayyade wuraren sayar da burodi da man fetur a Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya rattaba hannu kan dokar haramta sayar da biredin da ba shi da sunan kamfani da wanda ake naɗewa cikin leda da kuma sayar da fiye da lita 50 na man fetur da kuma amfani da gilashin mota mai duhu a jihar Zamfara.

    Gwamna Lawal ya sa hannu kan dokar ranar Laraba a gidan gwamnati da ke Gusau.

    Wata sanarwa da kakakin gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce dokar ta yi maganin matsalolin da aka bayyana suna janyo ƙalubalen tsaro a jihar.

    Ya ce an yi dokar ne saboda hare-haren baya-bayan nan da aka kai kan wasu yankuna a sassan jihar.

    Sanarwar ta bayyana cewa "sakamakon hare-haren da aka kai a baya-bayan nan a wasu yankuna da ke sassan wasu ƙananan hukumomin jihar musamman Zurmi da Shinkafi da Ƙaura Namoda da Talata Mafara da kuma dawowar ayyukan ƴanbindiga da sace-sacen mutane a wasu yankuna da wasu manyan tituna a jihar.

    Gwamnan ya kuma haramta wa masu motoci a jihar Zamfara amfani da gilashi mai duhu sannan kuma an haramta musu rufe lambar motocinsu a lokacin tuƙi.

    Abin da dokar ta ce:

    • Daga yanzu dole ne duk wani gidan burodi ya sanya cikakken suna da adireshi da duk wani bayani kan kamfanin.
    • An ƙayyade wauraren da za a sayar da burodi a fadin jihar, inda za a sayar kawai a cibiyoyin ƙananan hukumomi kawai.
    • A Gusau za a sayar da burodi ne a Damba-Zaria Road; Gada Biyu Sokoto Rod; Command Guest House kan hanyar Kaura Namoda; Gusau Garage-Dansadau Road.
    • Babu wani gidan sayar da mai wanda zai sayar da man fetur sama da lita 50 ga mota ɗaya a lokaci guda.
    • Gidajen sayar da man fetur za su yi aiki ne daga ƙarfe shida na safe zuwa shida na yamma.
    • An haramta rufe lambar mota a lokacin tuƙi.
    • Dole ne kowane mai mota ya mallaki cikakkun takardun rajista.

    Zamfara na daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro a Najeriya, inda ƴan fashin daji ke shiga ƙauyuka suna sace-sace tare da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

    • Masu gidajen burodi za su fara yajin aiki a Najeriya
    • Matsalar hare-haren ƴan bindiga ta ɗauki sabon salo a jihar Zamfara
  17. Har yanzu akwai shirin tura jami'an tsaron Kenya zuwa Haiti - Ruto

    Shugaban Kenya William Ruto ya tabbatar da shirin tura jami'an 'yan sanda zuwa Haiti da zarar an kafa majalisar shugaban kasa ta rikon ƙwarya.

    Duk da jinkirin da aka samu tun farko sakamakon murabus din Firaministan Haiti, tattaunawa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya mayar da hankali kan gaggauta tura sojojin.

    Ruto ya jaddada aniyar Kenya na jagorantar tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Haiti domin maido da zaman lafiya da tsaro.

    Sai dai kuma kafa majalisar na fuskantar adawa daga wasu jam'iyyun siyasa, lamarin da zai iya tsawaita tsarin

    Idan aka kafa majalisar za ta nada firaminista na rikon kwarya tare da haɗa kai da rundunar 'yan sandan kasashen duniya da Kenya ke jagoranta domin magance tashe-tashen hankulan gungun jama'a.

    • Haiti : An bankaɗo wanda ya bada umarnin kisan shugaban ƙasar
    • Abin da ya sa tasirin ƙabilanci a zaɓen Kenya ke raguwa
  18. An kama shugaban ƙungiyar addini da ake zargin tana bautar da ƙananan yara

    Ƴansanda a Zimbabwe sun ce sun kama shugaban wata ƙungiyar addini da ake zargi da tsafi a Lardin Mashonaland West da ke arewacin ƙasar tare da kuɓutar da gomman mata da yara ƙanana.

    An kama Ishmael Chokurongerwa mai shekara 56 wanda ke jagorantar ƙungiyar ta Gore Jena Penyeranyika tare da wasu manyan jami'an ƙungiyar bakwai a ranar Talata, kamar yadda mai magana da yawun rundunar Paul Nyathi ya faɗa cikin wata sanarwa.

    Ƴansanda sun ce kusan yaran 251 da aka gano a gonar Mista Chokurongerwa da ke Nyabira, kusan kilomita 34 daga Harare, ba su da takardar shaidar haihuwa sannan ba a barin su zuwa makaranta.

    Ƴansanda sun kuma gano wata maƙabarta cikin gonar inda a ɓoye aka binne mutum 16, har da yara bakwai da hukumomi ba su san da mutuwarsu ba.

    Yaran da aka kuɓutar "ana amfani da su wajen gudanar da wasu ayyuka domin amfanin shugabancin ƙungiyar, kamar yadda sanarwar ƴansandan ta ce.

    "Ƴansanda sun kuma bayyana cewa duka yaran an ci zarafinsu kamar saka su aikace-aikace da sana'ar hannu da sunan koya musu sana'ar hannu," in ji sanarwar.

    Mr Chokurongerwa, wanda yake kiran kansa a matsayin manzo ya shaida wa ƴanjaridar ƙasar cewa ba shi da masaniya game da haƙƙoƙin mata da yara.

    Ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar ya shaida wa ƴanjarida cewa ubangiji ba ya buƙatar ilimin zamani a makarantu saboda abin da ake koya wa yara a can ya saɓa wa koyarwar ubangiji.

    • Zimbabwe: An kama wanda ake zargi da hannu a mutuwar wata yarinya yayin haihuwa a coci
    • Yadda ake cinikin takardun kuɗi don kauce wa tsadar rayuwa a Zimbabwe
  19. Shugaban kamfanin TikTok ya gargaɗi Amurka kan haramta shafin

    Shugaban shafin sada zumunta da muhawara na TikTok ya ce, kamfanin zai yi duk abin da zai iya domin kare kansa, bayan da majalisar wakilan Amurka ta amince da wani ƙudurin doka, da zai iya kaiwa ga haramta amfani da shafin a Amurka.

    Fadar Gwamnatin Amurka, White House, ta yi kira ga 'yan majalisar dattawa da su gaggauta amincewa da ƙudurin, wanda 'yan majalisa suka ce zai kare Amurkawa daga barazanar alakar TikTok ɗin da gwamnatin China.

    A wani bidiyo da ya sanya a shafin na TikTok, shugaban kamfanin Shou Zi Chew ya yi gargaɗin cewa muddin aka zartar da wannan doka, to dokar za ta kai ga hana amfani da shafin gaba ɗaya a Amurka.

    A don haka ya ce, kamfanin zai yi amfani da dama da ƴancin da yake da shi na doka ya kare shafin da kuma Amurkawa miliyan 170 da suke amfani da shi.

    Mista Chew ya ce manufar matakin kawai haramta amfani da manhajar ne.

    Ya ce: ''Wannan dokar, idan aka amince da ita za ta kai ga hana amfani da TikTok ne a Amurka. Hatta ma waɗanda suka kawo ƙudurin sun yadda cewa burinsu ke nan. Wannan ƙudurin doka ya bayar da ƙarin iko ga wasu kamfanonin shafukan sada zumunta da muhawara ƴan kaɗan. Haka kuma zai raba masu ƙirƙira da masu ƙananan harkokin kasuwanci biliyoyin dala. Zai kuma jefa aikin Amurkawa sama da dubu 300 cikin ha dari, kuma zai ɗauke TikTok dinku.''

    Fadar gwamnatin Amurka, White House ta ce tana goyon bayan ƙudurin dokar, da zai bai wa masu shafin ƴan China damar kusan wata shida ta ko dai su sayar da shafin ko kuma su fuskanci haramcin amfani da shi a wayoyi.

    Ƴan majalisar na ɗaukar shafin a matsayin wata barazana ga tsaron Amurka.

    Kamfanin na TikTok ya musanta alaƙa da gwamnatin China, ya kuma buƙaci masu amfani da shafin a Amurka, da su yi ta kiran wayoyin ƴan majalisar, su buƙace su da su yi watsi da wannan doka.

    • Ko kun san wanene shugaban kamfanin TikTok?
    • Ko ya kamata gwamnatocin Afirka su dakatar da TikTok?
  20. 'Za a kai Falasɗinawa cibiyoyin jin-ƙai kafin ƙaddamar da hari a Rafah'

    Sojojin Isra'ila sun ce sun shirya kai Falasɗinawan da suka rasa muhallansu a Gaza zuwa abin da suka kira cibiyoyin jin-ƙai a tsakiyar zirin gabanin ƙaddamar da ƙudurinsu na kai hari ta ƙasa.

    Sun ce za ta kwashe mutanen ne daga Rafah a kudancin Gaza zuwa tsibiran sannan kuma za su ba su kayan jin ƙai da kuma muhalli na wucen gadi duk da wurin da ake shawarar kai su ya lalace sakamakon yawan hare-haren da aka kai ta sama da ƙasa.

    Rafah dai ta cunkushe da fiye da Falasɗinawa miliyan ɗaya waɗanda hare-haren Isra'ila suka tilasta masu tserewa daga gidajensu a Gaza.

    Duk da gargaɗin da ƙasashen duniya suka yi, Isra'ila ta dage cewa kai hari ta ƙasa kan birnin ne hanya tilo ta murƙushe Hamas.

    Amurka ta ce dole ne Isra'ila ta nuna tana da wani tsari na kare farar hula kafin kai irin wannan hari a Rafah.