Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Habiba Adamu, Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Rufewa

    Jama'a a nan muke cewa Allah Ya ba mu alkhairinsa.

    Da fatan kun ji daɗin labaran da muka kawo muku a yau. Sai kuma gobe cikin yardar Allah.

    Fatan mun sha ruwa lafiya, Allah kuma ya karɓi ibadunmu.

    Nabeela Mukhtar Uba da Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.

  2. An karrama sabuwar wakar Kizz Daniel 'Thankz Alot'

    An karrama sabuwar wakar tauraron Najeriya Kizz Daniel mai suna 'Thankz Alot' domin girmama masoyansa.

    Wakar wanda aka saki ranar Litinin, na ɗauke da sako mai ma'ana:

    "Ina matukar godiya ga kauna da goyon bayan da nake samu daga masoyana a tsawon rayuwata," in mawakin.

    "Wakar Thankz Alot ita ce hanyata ta nuna godiyakan irin goyon bayan da al'umma ke ba ni."

    Kizz Daniel na kuma da wasu sabbin waƙoƙi da ya rera tare da Davido.

  3. Ba ɗabi'ata ba ce ɗora laifi kan gwamnatoci da suka gabata - Tinubu

    Shugaba Bola Tinubu ya ce ba halinsa ba ne ya ɗora wa gwamnatocin da suka shuɗe laifi kan taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma rashin tsaro tsaro da Najeriya ke fama da shi, inda ya ce ya himmatu wajen ɗaukar matakan da suka dace na sake farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar da kuma tsayawa kan turbar da ta dace don samun ci gaba.

    Shugaban ya bayyana haka ne a jawabi a wani biki kan magance ƙarancin abinci ranar Litinin a Minna, babban birnin jihar Neja.

    Da yawa daga cikin mukarraban gwamnatin Tinubu ciki har da ministan kuɗi Wale Edun, sun ɗora laifin matsalolin tattalin arziki da kuma tsaro da ƙasar ke fuskanta a kan gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

    Sai dai Tinubu, wanda ya karɓi ragamar mulki daga hannun Buhari a watan Mayun bara, ya ce damuwarsa ba wai ya zargi gwamnatocin da suka gabata ba, illa ɓullo da tsare-tsaren da suka dace domin ɗora ƙasar kan turbar ci gaba.

    Najeriya dai na fama da matsalar garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, hauhawar farashin kayayyaki, tashin farashin dala, matsalar tattalin arziki da kuma tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur, lamarin da ya janyo zanga-zanga a sassan ƙasar.

  4. An bayar da sammacin kama wani lauyan bogi a Kenya

    Kungiyar lauyoyin a Kenya ta ce an bayar da sammacin kama wani ɗan ƙasar Kenya da ake zargi lauyan bogi ne wanda kuma ke aiki ba tare da shaidar kwarewa ba.

    Shari’ar da ake yi masa dai ta ja hankalin ‘yan ƙasar Kenya tun bayan da aka kore shi a matsayin lauya da ke aiki ba bisa ka'ida ba a watan Oktoban bara.

    Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a faɗin ƙasar.

    A lokacin, jami'an shari'a a Kenya sun buƙaci 'yan sanda da su kama mutumin, wanda ke aiki da sunan "Brian Mwenda".

    Sun ce mutumin ya sace ainihin sunan wani lauya ne mai suna Brian Mwenda Ntwiga.

    Ya mika kansa ga ‘yan sanda jim kaɗan bayan haka.

    Daga nan ne aka tuhume shi da laifuka shida, amma ya ki amsa laifinsa.

  5. Yara miliyan ɗaya na mutuwa duk shekara a Najeriya – Ministan Lafiya

    Ministan Lafiya a Najeriya, Farfesa Ali Muhammad Pate ya ce kimanin yara ƴan ƙasa da shekara biyar na mutuwa duk shekara sakamakon cututtuka ciki har da waɗanda rigakafi ke samar da kariya daga kamuwa da su.

    Ministan ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan Talabijin na Channels kamar yadda Daily Trust ya ruwaito, inda ya ce kashi 70 cikin 100 na mace-macen ana iya kare su.

    "Bari mu yi bayani, akwai kimanin mace-macen yara miliyan ƴan ƙasa da shekara biyar duk shekara a ƙasar nan, kashi 70 na mace-macen sakamakon cututtuka kamar mashaƙo da ƙaynda da nimoniya da ake iya kandagarkinsu ta hanyar yin rigakafi da kuma sauran rigakafi da ake da su wadanda ba su da tsada.

    Farfesa Pate ya ce gwamnatin shugaba Tinubu ya bijiro da tsare-tsare da za su shafi rayuwar talaka inda ya ce zuba hannun jari a ɓangaren lafiya na daga cikinsu.

    Ya ce ana samar da matakai da dama na magance zazzabin cizon sauro a Najeriya ciki har da amfani da gidan sauro da rigakafi.

    A cewarsa, Najeriya a shirye take ta samar da alluran rigakafin zazzabin cizon sauro a ƙasar ba da daɗewa ba.

  6. Trump ba zai bai wa Ukraine ko kobo ba idan ya ci zaɓe - Firaiministan Hungary

    Firaiministan ƙasar Hungary Viktor Orban ya ce tsohon shugaban Amurka ba zai bai wa Ukraine ko da sisin kobo ba idan aka sake zaɓarsa.

    Kalamansa na zuwa ne bayan wani zama da ƴan siyasar biyu suka yi a Florida a ranar Juma'a.

    Mr Orban ya ce ya yi imanin cewa yaƙin Ukraine zai zo karshe bayan sake zaɓar Trump saboda Turai ba za ta iya bai wa sojojin Ukraine kuɗi ba a kashin kanta.

    Duk da mamayar da Rasha ta yi Ukraine da ta kasance makwabta ga Hungary, Mr Orban ya ci gaba da kulla alaƙa da shugaba Vladimir Putin.

  7. Tsawa ta kashe mutum huɗu a Mozambique

    Tsawa ta kashe wasu mutum huɗu tare da jikkata uku a Mozambique, inda wata guguwa mai karfin gaske ta tinkari ƙasar.

    Lamarin ya faru ne a garin Mogincual, da ke lardin Nampula.

    A halin da ake ciki kuma, an sanya lardunan kudanci da tsakiyar Gaza da Inhambane da Sofala da kuma Zambézia a cikin shirin ko-ta-kwana saboda tsawa da ake sa ran nan gaba a yau litinin.

    A yanzu, Guguwar ta Filipo ta isa gaɓar tekun Mozambique kuma tana iya rikiɗewa zuwa guguwa mai tsanani, kafin ta koma teku.

    An riga an samu karuwar ruwan sama kuma ana fargabar zaftarewar laka.

    Hukumar Kula da Yanayi a Ƙasar ta Mozambique ta gargaɗi jiragen ruwa da su yi taka tsantsan.

    Afkuwar bala'o'i a Mozambique ba sabon abu bane, musamman a lokacin damina da kuma guguwa da ke gudana tsakanin Oktoba da Afrilu.

  8. Gwamnatin Tinubu ta musanta coge a kasafin kuɗin ƙasar

    Fadar shugaban Najeriya ta musanta zargin yin coge a kasafin kudin 2024 wanda Shugaban kasar ya sanyawa hannu a watan Janairu.

    Ɓangaren zartarwar ta mayar da martani ne kan wata hira da BBC ta yi da shugaban ƙungiyar ƴanmajalisar dattawan ƙasar na yankin arewa, Sanata Abdul Ningi wanda ya yi zargin cewa kasafin kuɗin da bangaren zartarwa ke aiki da shi ba shi ne majalisun dokokin kasar suka rattabawa hannu ba.

    Sai dai mataimaki na musamman ga shugaban kan watsa labarai, Abdulaziz Abdulaziz ya ce ba kamshin gaskiya a zargin.

    Ga tattaunawarsa da Zulaihat Kibiya.

  9. An buɗe zaman tattaunawa tsakanin Habasha da hukumomin Tigray

    Wakilai daga gwamnatin ƙasar Habasha da kuma na yankin Tigray sun fara zaman tattaunawa a Addis Ababa, babban birnin ƙasar, domin kawo karshen tsaikon da ake samu wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya.

    Yarjejeniyar wanda ɓangarorin biyu suka cimma a watan Nuwamban 2022 a Afrika Ta Kudu, na da zimmar dawo da zaman lafiya a yankin bayan rikici tsakanin ƙungiyar Tigray People's Liberation Front (TPLF da kuma gwamnatin tarayya da ya ɗaiɗaita yankin wanda aka fara tun watan Nuwamban 2020.

    Matsaloli wajen aiwatar da yarjejeniyar ya janyo zaman fargaba, abin da ya sa ƙungiyar Tarayyar Afrika shiga tsakani domin laluɓo hanyar mafita.

    Yarjejeniyar ta amince da batun raba iko, samar da ƴancin gashin kai na yankin da iko da albarkatu, duka da zimmar warware rikicin.

    Shugaban rikon kwarya na yankin Tigray, Getachew Reda, ya sanar da cewa babu wani ƙarin zama tattaunawa da za a gudanar tsakaninsu da gwamnatin tarayya har sai an warware dukkan batutuwa da ke kasa.

    Tsohon shugaban ƙasar Kenya Uhuru Kenyatta da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo na cikin waɗanda ke shiga tsakani a tattaunawar.

  10. Al-Qa'ida ta sanar da mutuwar shugabanta a Yemen

    Reshen Al-Qa'ida na ƙasar Yemen ya sanar da mutuwar shugabansa, a wani yanayi da ba a fayyace ba.

    A wani bidiyon da aka wallafa a shafin intanet da ƙungiyar a yankin Larabawa ta (AQAP) ta yi, ya nuna gawar Khalid Batarfi' an yi mata sutura ajiye a gaban tutar ƙungiyar.

    A wata sanarwa da wani ƙusa a ƙungiyar ya karanta, ba a bayyana musabbabin mutuwarsa ba, sai dai ta yi amfani da kalmar cewa Allah ne ya karɓi ransa, abin da ke nuna cewa ba kashe shi aka yi ba kamar wanda ya gabace shi.

    Batarfi, ɗan asalin Saudi Arabia na cikin shekarunsa na 40 a lokacin da ya karɓi jagorancin AQAP a shekarar 2020.

    Amurka ta ayyana shi a matsayin ɗanta'adda a shekarar 2018 kuma ta sanya kuɗi dalar Amurka miliyan biyar a kansa.

    Jami'in AQAP wanda ya karanta sanarwar, Abu Khubaib al-Sudani ya sanar da cewa majalisar shura ta ƙungiyar ta zaɓi Saad bin Atef al-Awlaki a matsayin sabon shugaban ƙungiyar.

    An taɓa ɗaukar AQAP a matsayin reshe mafi ƙarfi da tasiri kuma mafi hatsari na ƙungiyar al-Qa'ida.

    AQAP ta kai munanan hare-hare a cikin Yemen da kuma Saudi Arabia da kuma yunkurin kai wani harin bam kan jirgin saman Amurka, harin da aka daƙile.

  11. Jirgin ruwa ɗauke da kayan agajin Gaza ya kasa barin Cyprus

    Wani jirgin ruwa ɗauke da kayan agajin da aka shirya kai wa Gaza na tashar jiragen ruwa ta Cyprus, kwana ɗaya bayan lokacin da ya kamata ace ya ɗauki hanya.

    Wata ƙungiyar agaji wadda ke jagorantar shirin ta shaida wa BBC cewa 'yanayin na da sarƙaƙiya", amma suna fatan nan ba da jimawa ba jirgin zai fara tafiya.

    Da maraicen ranar Lahadi ne aka ga watan Ramalana, abin da ya sa musulmi a fadin duniya suka fara azumtar watan mai tsarki ciki har da waɗanda ke Gaza.

    Batun cimma tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas, lamari ne da kawo yanzu aka gagara samun nasara akai.

    Shirin kai kayan agajin a jirgin mai suna 'Open Arms' ba ya cikin shirin Amurka na kai kayan agaji ta ruwa zuwa Gaza.

    Jirgin wanda ke birnin Larnaca na wata ƙungiyar agaji ce da ke da suna iri ɗaya da jirgin ruwan.

    Jirgin zai ja wani abin ɗaukar kaya ɗauke da tan 200 na kayan abinci da suka haɗa da shinkafa da fulawa da kifi da naman gwangwani, waɗanda wata ƙungiyar agaji da Amurka World Central Kitchen (WCK) ta haɗa.

    Zai kuma ɗauki tafiyar kwanaki biyu ne kafin kayan su isa nesa da gaɓar tekun Gazan da ba a bayyana ba, ta bin wata sabuwar hanyar teku da ƙungiyar tarayyar Turai ta ce za a buɗe a ƙarshen mako.

    Inda ƙungiyar ta bayyana cewa akwai wasu tan 500 na kayan abincin da aka riga ta shirya don kai wa Gaza a nan gaba.

    Kai kayayyakin agaji Gaza na ci-gaba da zama wani abu mai wuya da kuma hatsari, a cewar hukumar abinci ta duniya WFP.

    A watan jiya hukumar ta dakatar da kai agaji arewacin Gaza saboda yamusti da tashin hanklin da ta ce ma'aikatanta sun fuskanta.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargadin cewa al'ummar Gaza na gab da faɗawa cikin yunwa, inda yara ke mutuwa saboda yunwar.

  12. Ma'aikatan jami'oi sun ƙuduri shiga yajin aiki a Najeriya

    Ƙungiyar manyan ma'aikatan Jami'oin Najeriya, SSANU da kuma ta ma'aikatan jami'a da basa koyarwa, NASU sun ce za su tsunduma yajin aiki a ranar Litinin mai zuwa.

    Ƙungiyoyin sun cimma matsayar a ƙarshen wani taron da suka kammala a ranar Lahadi a birnin Akure na jihar Ondo da ke kudancin ƙasar.

    SSANU da NASU sun ce za su shiga yajin aikin na gargaɗi na kwana bakwai ne domin neman gwamnati ta biya musu wasu haƙƙoƙinsu.

    Ciki har da rashin biyan albashinsu na wata 4 da gwamnatin ƙasar ba ta yi ba na lokacin da suka shiga yajin aiki na ƙasa baki ɗaya, a shekarar 2022.

    Ƙungiyoyin sun nuna rashin jin daɗinsu kan rashin biyan mambobinsu albashin duk kuwa da cewa gwamnatin tarayya ta biya takwarorinsu na malaman jami'oi nasu kuɗaɗen.

    Shugaba Bola Tinubu tuni ya bayar da umarnin a biya ma'aikatan jami'oin kuɗaɗensu da aka yi, sai dai ƙungiyoyin na cewa har yanzu basu gani a ƙasa ba.

    • Halin da malaman jami'o'in Najeriya suka shiga saboda rashin albashi
    • Ƙarin kuɗin makaranta ya jefa iyaye tasku a Najeriya
  13. Ana binciken matuƙa jirgin saman Batik da barci ya kwashe ana tsaka da tafiya

    Indonesia na binciken wani kamfanin jiragen sama na cikin gida, Batik Air, bayan an gano cewa matuƙa jirgin sun kwashe da barci na tsawon mintoci 28, yayin da jirgin ke tsaka da tafiya a sararin samaniya.

    Mutanen biyu - waɗanda duka an dakatar da su, sun yi barci ne a lokacin da jirgin ke tafiya tsakanin Sulawesi da babban birnin ƙasar, Jakarta a ranar 25 ga watan Janairun da ya gabata.

    Ɗaya da daga cikinsu rahotanni sun nuna cewa ya gaji ne bayan ya kula da sabbin jariransa tagwaye.

    Jirgin ƙirar Airbus A320 ya ɗan kaucewa hanya, amma ya sauka lafiya tare da fasinjoji 153 da kuma ma'aikatansa.

    Matuƙin mai shekara 32 ya gaya wa abokin aikinsa ya ci-gaba da tuƙi, don yana buƙatar ya huta, kusan mintoci 30 da tashin jirgin.

    Abokin aikin nasa mai shekaru 28 ya amince da hakan, a cewar wani rahoto na ma'aikatar sufuri ta ƙasar.

    Amma kuma sai shi ma ya ɓuge da barcin.

    A cewar rahoton matarsa ta haifi tagwaye wata guda da ya wuce kuma ya taimaka mata wajen kula da su.

    Masu kula da zirga-zirgar jiragen sama na filin jirgin Jakarta sun yi ƙoƙarin yin magana da matuƙa jirgin, amma babu wanda ya amsa.

    An ji shuru na tsawon mintoci 28, kafin daga bisani babban matuƙin ya farka ya ga abokin aikin nasa shi ma yana barci. Kuma a sannan ne ya gano cewa jirgin ya ɗan kaucewa hanya.

    Daga bisani matuƙan sun amsa wa masu kula da zirga-zirgan jiragen, suka kuma saukar da jirgin lafiya.

    Gwajin lafiyarsu da aka yi kafin jirgin ya tashi ya nuna cewa suna cikin ƙoshin lafiya kuma za su iya tuƙa jirgin.

    Gwajin hawan jini da na bugun zuciya duka lafiya, sannan gwajin shan giya ya nuna cewa ba su sha barasa ba.

    • Yadda fasinja ya fitsare wata mata a jirgin sama
    • Yadda faɗa tsakanin mata da miji ya tursasa wa jirgin sama saukar gaggawa
  14. Abubuwan da suka kamata mu ci da waɗanda ba su kamata ba a lokacin azumi

  15. Makarantu a jihohi 14 na Najeriya na cikin haɗarin satar ɗalibai

    Gwamnatin Najeriya ta gano wasu makarantu a jihohi aƙalla 14 da kuma birnin Abuja, da ke da raunin da za a iya kai musu hari, yayin da ake samun ƙaruwar satar ɗalibai a ƙasar.

    Hajiya Halima Iliya, shugabar shirin samar da kuɗaɗen bayar da kariya ga makarantu na ƙasa, ta ce hukumar ta tattara bayanai da za su taimaka wajen kai wa makarantun ɗauki.

    A shekarar 2014 ne aka kafa hukumar bayan sace ɗaruruwan ɗaliban makarantar Chibok da ke jihar Borno a arewa-maso-gabashin ƙasar.

    Jihohin da wasu makarantunsu ke cikin haɗarin sun haɗa da Adamawa, Bauchi, Borno, Benue, Yobe, Katsina, Kebbi, Sokoto, Filato, Zamfara da birinin Abuja. A cewar hukumar.

    A ranar Alhamis da ya wuce ne ƴanbindiga suka sace ɗalibai 270 na makarantun firamare da sakandire a ƙauyen Kuriga da ke jihar Kaduna.

    Haka kuma a ranar Asabar da ta wuce ne wasu ƴanbindigar suka sace ɗaliban makarantar tsangaya kimanin 15 a ƙaramar hukumar Gada a jihar Sokoto.

    Sace-sacen sun biyo bayan sace wasu ɗaruruwan ƴangudun hijira a Ngala da ke jihar Borno da ake zargin ƴanBoko Haram da aikatawa.

    Iyaye da ƴan'uwan ɗalibai da sauran waɗanda aka sacen na ci-gaba da roƙon gwamnati ta kuɓutar da su.

    • Sace-sacen ɗalibai a makarantu 10 da suka girgiza Najeriya
    • 'Sai hukumomin tsaro sun haɗa kai a ga bayan matsalar tsaron Najeriya'
  16. Abdulsalami ya nemi Nijar, Mali, Burkina Faso su koma ECOWAS

    Tsohon shugaban Najeriya, kuma ɗaya daga cikin masu shiga tsakani kan rikicin ƙungiyar ECOWAS da jumhuriyar Nijar, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya yi kira ga ƙasashen yanki uku da su koma cikin ƙungiyar.

    Wannan ne karon farko da mai shiga tsakanin ya furta cewa, ficewar Ƙasashen Burkina-Faso da Mali da kuma jumhuriya Nijar daga ECOWAS mayar da hannun agogo baya ne.

    A cewarsa matakin ƙasashen zai iya kawo naƙasu ga tattalin arzikin yankin.

    Janar Abdulsalami Abubakar ya yi kira ga ƙasashen uku da su dawo cikin garke a yi tafiya da su, domin sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi.

    • Abun da ya sa Ecowas ta ɗage wa Nijar da Mali da Burkina Faso takunkumai
    • Me ya rage wa Nijar, Mali da Burkina Faso bayan ficewa daga Ecowas?
  17. Burtaniya zata kashe £117m don ba da kariya ga musulmai

    Gwamnatin Birtaniya ta yi alƙawarin ware Fam 117 miliyan (dalar Amurka miliyan 150) a cikin shekaru 4 domin inganta tsaron al'ummar musulmin ƙasar.

    Gwamnatin ta ce za a yi amfani da wani ɓangare na kuɗin domin ƙara matakan tsaro a masallatai da makarantun koyar da addini da wuraren da musulmai ke taruwa.

    Haka kuma ta ba da tabbacin cewa ba za a lamunci yi wa musulmin ƙasar barazana ko kalaman ƙiyayya ba.

    Sanarwar na zuwa ne bayan alƙawarin da gwamnatin ta ɗauka na kashe dala miliyan 90 don bayar da kariya ga Yahudawa.

    Tun bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas ake samun ƙaruwar ƙiyayya tsakanin mabiya addinin musulunci da kuma yahudawa mazauna Birtaniyar.

    • Musulmai da Yahudawan Birtaniya na fargabar alaƙarsu saboda yaƙin Gaza
    • Birtaniya na duba yiwuwar amincewa da kasar Falasdinawa - Cameron
  18. Isra'ila na ci gaba da ruwan wuta a Gaza duk da shigowar Ramadan

    Falasɗinawa sun fara azumin Ramadan yayin da ake ci gaba da gwabza faɗa a yankin tsakanin dakarun Isra'ila da sojojin Hamas kuma babu wata alamar cewa za a cimma tsagaita wuta.

    Isra'ila ta lalata muhallan akasarin al'ummar Gaza, yayin da a alokaci guda hukumomin bayar da agaji ke gargaɗin cewa mutane za su mutu saboda yunwa.

    A daren da ya gabata an yi artabu bayan da ƴansandan Isra'ila suka hana ɗarurtuwan matasa Falasɗinawa shiga masallacin Al Aqsa.

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu dai ya sha alwashin ci gaba da ruwan wuta a birnin Rafah da ke kudancin Gaza duk da gargaɗin da shugaban Amurka Joe Biden ya yi kan batun.

    A cikin saƙonsa na Ramadan ga al'ummar Gaza, Biden ya ce Musulmai da dama a duniya za su yi azumi ne da Falasɗinawa a ransu.

    • Yadda ake kashe ma'aikatan lafiya masu aikin ceton rai a Gaza
    • Isra’ila ta kai mummunan hari a birnin Rafah
  19. Firaiministan Chadi zai tsaya takarar shugabancin ƙasar

    Firaiminstan Chadi wanda gwamnatin sojin ƙasar ta bai wa muƙamin, Succès Masra ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin ƙasar, mako ɗaya bayan shugaban mulkin sojin ƙasar, Mahamat Déby ya sanar da tashi aniyar.

    Mista Masra, tsohon madugun ƴan'adawa ya sanya hannu a yarjejeniyar sulhu da shugaba Deby bayan ya koma ƙasar daga gudun hijira, kafin daga bisani a bashi matsayin firaiminista a watan Janairu.

    Masra ya shaida wa magoya bayansa a wani taron gangamin da aka yi a ranar Lahadi cewa, zai tsaya takarar shugabancin ƙasar ne saboda ya haɗa kan jama'a tare da 'kawo musu sauƙi.'

    Sai dai ƴan'adawa sun soki matakin da cewa wani makirci ne aka ƙulla domin nuna wa jama'a cewa shugaba Deby na da abokan hamayya, alhali Deby na da yaƙinin lashe zaɓen.

    "Yaudara ce, ba takarar gaske ba ce, rakiya ce kawai zai yi wa shugaban mulkin sojin. Kakakin ƙungiyar ƴan'adawa na GCAP, Max Kemkoye ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP, hakan.

    Babban abokin hamayyar Deby, kuma jaroran ƴan'adawa, Yaya Dillo an kashe shi a wata musayar wuta da jami'an tsaro a ranar 28 Fabairu.

    Gwamnatin ƙasar ta ɗora laifin harin a kansa, lamarin da ya musanta.

    Dillo ne aka fi ganin zai yi gogayya sosai da mista Deby a babban zaɓen ƙasar.

    Shugaba Déby ya karɓi ragamar shugabancin ƙasar ne bayan kisan mahaifinsa da ƴantawaye suka yi.

    Mahaifin nasa, Idriss Deby, ya shafe fiye da shekara 30 yana mulkin ƙasar.

    • Su waye 'yan tawayen Chadi, kuma me suke so?
    • Rawar da Idris Deby ya taka a yaki da Boko Haram a yankin Tafkin Chadi
  20. Ana sukar sanya sunan Tinubu a filin jiragen saman Neja

    Jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya ta sauya sunan filin jiragen sama a jihar zuwa filin jiragen sama na Bola Tinubu, lamarin da ya janyo suka daga wasu ƴanƙasar.

    Mai magana da yawun gwamnatin jihar, Hajiya Binta Mamman ta ce an sauya wa filin jiragen saman na ƙasa da ƙasa suna ne, domin gudunmawa ta fuskar ci-gaba da shugaban ƙasar ya baiwa jihar.

    Sai da wasu al'ummar ƙasar sun yi suka ga matakin, suna ɗora ayar tambaya kan tasirin yin hakan ta fuskar tattalin arziki.

    A ranar Litinin ne ake sa ran shugaba Tinubu zai kai wata ziyarar aiki jihar, inda zai ƙaddamar da filin jiragen saman da aka yi wa gyara da kuma wani wurin da aka ware domin ayyukan noma.

    Kafin sauya wa filin jiragen saman suna, ana kiransa ne da filin jiragen saman Abubakar Imam, wani marubuci kuma ɗanjarida wanda ya fara ƙirƙiro jaridar harshen Hausa ta farko a arewacin ƙasar.

    A shekarar da ta wuce ne hukumomin da ke kula da zirga-zirgar jiragen sama suka ce za su sauyawa wasu filayen jiragen sama 15 na gwamnatin tarayya suna, zuwa sunayen wasu fitattun mutane, ciki har da tsaffin shugabannin ƙasar.

    • 'Kasafin kuɗin da Tinubu ya gabatar cike yake da bashi da yaudara'
    • Ƴan siyasa mata da ake zargi da cin hanci da rashawa a Najeriya