Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida and Usman Minjibir

  1. Sai gobe!

    Nan muka kawo karshen shafin namu na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata.

    Ku tare mu a gobe Laraba da yardar Allah.

  2. 'Hauhawar farashi ba za ta ragu ba sai Najeriya ta rage kayan da take bukata daga waje'

    Gwamnan Babban bankin Najeriya Olayemi Cardoso ya bayyana cewa kasar ba za ta rabu da matsalar karancin dala da hauhawar farashi ba sai ta kara yawan kayan da take fitarwa zuwa kasashen waje, maimakon shigar da mafi yawan kayan bukata da ake yi a halin yanzu.

    Gwamnan na CBN ya bayyana hakan ne ranar Talata lokacin da ya amsa gayyatar da majalisar wakilan kasar ta yi masa domin yin bayani kan hauhuwar farashin kayan masarufi da karancin takardar kudin dala da kasar ke fama da shi.

    Darajar naira dai na ci gaba da faduwa idan aka kwatanta da dalar Amurka, lamarin da ke kara iza wutar matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar.

    Sai dai a lokacin da ya bayyana gaban majalisar, Cardoso ya ce Babban bankin kasar da wasu hukumomi daban-daban na daukar matakan da za su taimaka wajen rage hauhawar farashi da daga darajar naira nan ba da dadewa ba.

    Gwamnan babban bankin Najeriya Olayemi Cardoso da ministan kudi da kuma ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Senata Atiku Bagudu da shugaban hukumar tattara kuddade shigar Najeriyar sun shafe kusan sa`a shida suna amsa tambayoyi daga `yan majalisar wakilai a kan faduwar darajar naira da tsadar rayuwar da ake fama da ita a kasar, inda jami`ai daga bangaren zartarwa suka nuna cewa gwamnatin tarayyar tana sane game da mawuyacin halin da `yan kasa ke ciki….kuma tana daukar matakai daban-daban don rage wa al`umma kuncin da suke ciki

    Sai dai sun bayyana cewa da wuya a yi bankwana da matsalar tasadar dala sai masana`antu sun bunkasa ta yadda za a dinga fitar da ake samarwa a gida ana ka iwa waje.

  3. Babu gaskiya kan cewa ƴan Najeriya na fuskantar barazana a Afirka ta Kudu

    Sashen kula da hulɗa da ƙasashen ƙetare na ƙasar Afrika ta Kudu ya bayyana takaci kan sanarwar da ofishin jakadancin Najerya a Pretoria ya fitar, yana shawartar ƴan Najeriya da ke zaune a ƙasar su yi taka tsantsan a lokacin karawar da za a yi tsakanin Najeriya da Afirka ta kudu a gasar Afcon da ke gudana a Ivory Coast.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun sashen hukumar kula da huldar kasashen waje a Afrika ta Kudu, Mr Clayson Monyela, ta fitar a yau Talata, ta ce shawarar abun takaici ce, saboda hakan zai iya haifar da tunzuri, a tsakanin yan kasar ta Afika ta kudu da Najeriyar da 'yan Najeriyar da ke da sha'awar zuwa kasarsu.

    'Muna da yakinin cewar Afirka ta Kudu da ke kaunar wasanni, babu wata barazana ga 'yan Najeriya, kuma ba mu amince da irin kalaman da ofishin jakandancin Najeriyar ya yi ba' inji Mr Clayson Monyela.

    Sanarwar ta kuma bayyana cewar a lokuta daban-daban kungiyar kwallon kafan Afrika ta Kudu Bafana-Bafana ta sha karawa da ta najeirya ta Super Egale, ba a kuma taba samun tarihi na wani rikici ko fada da ke alaka da karawar kasashen biyu ba.

  4. ECOWAS ta damu da halin da ake ciki a Senegal

    Kungiyar haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta bayyana damuwar ta dangane da halin da ake ciki a Senegal yayin da aka jinkirta gudanar da zabukan kasar har zuwa tsakiyar Disamba.

    ECOWAS dai na son hukumomin Senegal su koma kan tsarin da aka yi tun farko na gudanar da zaɓen, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

    ECOWAS din dai ta shawarci hukumomin Senegal da ka da su dauki dukkan wani mataki da zai iya cin karo da kundin tsarin mulkin kasar.

    Hakan dai na nufin cewar Kungiyar kasshen Afirkan ba ta goyan bayan dage zaben shugaban kasar, da jam'iyyun adawa suka bayyana shi da yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar juyin mulki.

    Haka kuma kungiyar ta kuma shawarci 'yan kasar da su kwantar da hanakalinsu da zama cikin lumana, tare da kira ga jami'an tsaron kasar da su kare hakkin dukkan 'yan kasar.

    Wasu daga cikin jam'iyyun adawa na kasar na shirya tunkarar kotun koli don kalubalantar dage zaben.

    Kimanin mutum 150 aka tsare a wata zanga zanga da aka kwana biyu ana yi a ƙasar.

  5. Osimhen zai buga wasan Najeriya da Afrika ta Kudu

    Kungiyar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles ta ce an tabbatar da cewa ɗan wasanta na gaba Victor Osimhen na da lafiyar da zai iya buga wasan da kasar za ta yi na kusa da na karshe da Afrika ta Kudu.

    An dai fitar da hotunan atisayen ƙungiyar ta Super Eagle a ƙasar Cote d'Ivore, inda aka nuno ɗan wasan na atisayen tare da sauran takwarorinsa.

    An dai shiga fargaba bayan da aka yi tunanin cewa ɗan wasan zai iya gaza buga wasan na gobe Laraba bayan da a jiya Litinin ya gaza bin sauran ƴan'uwansa ƴan wasan Najeriya zuwa birnin Bouake inda za su buga wasan.

    Najeriya dai ta buga dukkanin wasanninta na rukuni da matakin ƴan 16 da na kwata-fainal ne a filin wasanni da ke Abidjan, babban birnin ƙasar.

  6. Gwamnatin Najeriya ta tsawaita haramcin saukar jiragen Nijar a kasar

    Gwamnatin Najerya ta sake jaddada matsayarta ta na hana jiragen sama daga Jamhuriyar Nijar sauka a Najeriya, da hana dukkan wani jirge da ke zuwa Nijar bi ta sararin samaniyarta.

    Wata sanarwar da aka aika wa masu ruwa da tsaki a harkokin jirgin sama a ranar 29 ga watan Janairun 2024 ta ce an dauki matakin ne bisa ka'ida.

    AIC ta ce dakatarwar ba ta shafi jiragen da ke wani aikin gaggawa, ko wani aiki na musamman ba.

    Ta ƙara da cewar za a bukaci jiragen da ke aiki na musamman su nemi izini daga ofishin babban Sakataren ma'aikatar sufuri da bunkasa bangaren sufurin jirgin sama.

  7. Mace mafi tsufa a Iran ta rasu tana da shekara 125

    Masoumeh Sanei Targehi, wadda ake kaytata zaton itace matar da ta fi kowa tsufa a Iran ta mutu tana da shekaru 125.

    Ms. Sanei Taroghi ta ga a mulkin zamani uku, da suka hada da na Qajar, da na Pahlavi, da kuma gwamnatin jamhuriyar Islama ta Iran.

    Ranar da aka haifi Masoumeh Sanei Tarogh wato Daya ga watan Octoban, 1277, na cikin hotunan takardun haihuwarta,da kafar talabijin ta Iran ta hasak.

    A shekarunta na 125 ta girmewa Jean Calman na Faransa, wanda aka bayyana a mastayin mutumin da ya fi kowa jimawa a duniya da ya mutu a 1376 yana da shekaru 122.

    Shekaru hudu da suka gabata, kafafen yada labarai na cikin gida a Iran sun rawaito mutuwar wani dan kabilar Kurdish a kasar, mai shekaru 138, kamar yadda katinsa na dan kasar ya nuna.

    A cewar kudun bajinta na duniya ya nuna cewar mutumin da ya fi kowa shekaru a duniya wani dan kasar Spaniya ne da za yi bikin cika shekaru 117 a duniya.

  8. Rashin tsaro: Gwamnatin Abuja ta bai wa masu zama ƙasan gada wa'adin su tashi

    Hukumar kula da birnin Abuja ta bai wa ɗaruruwan mutane da ke zama a ƙarƙashin gadojin da ke birnin mako guda su tashi ko kuma su fuskanci fushin hukumar.

    Mai taimaka wa ministan birnin na Abuja kan muhalli da kawar da shara, Fred Kpakol ya ce sun ɗauki matakin ne sakamakon koken da mazauna birnin ke yi kan ƙwace da fashi da ake yi wa al'umma.

    Fred Kpakol ya ce gadojin da ake fuskantar wannan mastaala da aka umarci waɗanda ke zaune a kasansu sun haɗa da gadojin unguwannin Garki, Wuse II, Maitama, da Wuse.

    Haka kuma ya yi gargadin cewar waɗanda ke zaune a ƙarkashin irin waɗannan gadoji a ciki da wajen Abujar da su gaggauta barin wuraren saboda nan ba da jimawa ba za a ƙaddamar da wata runduna ta 'Operation Storm under the bridge', don ganin sun kakkaɓe birnin daga bazanarar tsaro da ake fuskanta.

  9. Donald Trump ba ya da rigar kariya daga shari'a - Kotu

    Wata Kotun daukaka kara ta yanke hukucin cewar toshon shugaban Amurka, Donald Trump ba shi da kariya daga tuhume-tuhumen da ake masa na kitsa ƙoƙarin sauya kayen da ya sha a zaɓen shugaban ƙasa na 2020.

    Baki ɗayan alkalan kotun uku sun ƙi amincewa da da'awarsa ta cewar za a hukunta shi saboda tsohon shugaban ƙasa ne shi, a lokacin da aka zarge shi da yunƙurin ƙwace sakamakon zaɓen.

    Sun ce tsohon shugaban Amurkan Donald Trump ya zama kamar kowanne dan kasa, wanda za a iya tuhumar sa da kowane irin laifi.

    Hukuncin dai ya nuna cewa yanzu ya zama tamkar wajibi ne Trump ya fuskanci tuhumar aikata laifuka da ake yi masa a kotu.

    Kwamitin yakin neman zaben Trump ya ce zai ɗaukaka ƙara zuwa kotun koli.

  10. Ƴansanda a Anambra na neman wani sufeta ruwa a jallo kan zargin kisa

    Rudunar ƴansandan Najeriya a jihar Anambra ta ce tana neman sufeta Audu Omadefu ruwa a jallo, kan zargin kisa a jihar.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴansanda a jihar, Ikenga Tochukwu, ya fitar a yau Talata ce ta sanar da hakan inda ta ce jami'in ya tsere tun bayan da ya aikata laifin da ake zargin shi da aikatawa.

    Ta ce har yanzu ba a kai ga sanin inda ya ɓoye ba.

    Haka kuma sanarwar ta nemi dukkan wanda ya gan shi ko ya san inda yake ya gaggauta sanar da ofishin ƴansanda mafi kusa.

  11. An gurfanar da faston masu 'azumin mutuwa' bisa zargin kashe mutum 191

    A Kenya an gurafar da wani fasto kan zargin kisan kai, bayan da aka gano gawawwaki sama da 400 da aka binne a wani rami mai zurfi a wani jeji da ke gabashin kasar.

    Wasu daga cikin waɗanda suka tsira da ƴan'uwan waɗanda suka mutu, sun ce Paul Mackenzie ya nemi mabiya cocinsa da yin azumi domin "haɗuwa da Yesu".

    Sai dai shi da wasu mutum 29, sun musanta aikata lafin da ake tuhumar su da aikatawa a lokacin zaman kotun da aka yi a birnin Malindi.

    Tuni aka tuhumi Mackenzie da aikata laifukan ta'addanci, da azabtar da yara ƙanana, wani zargi da ya musanta aikatawa.

    Ƴansanda da lauya mai gabatar da ƙara sun yi zargin cewar baya ga yunwa, wasu daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su, an shaƙe su, sannan aka toshe musu hanyoyin shaƙar isa, ko aka yi ta dukan su har suka mutu.

    Ana zargin mutum 30 ɗin da laifin kisan mutum 191.

    "Har yanzu ina jin tsoron sa", ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira ta shaida wa BBC, a lokacin da aka aka tambaye ta abin da za ta faɗa wa Mackaenzie idan har ta gamu da shi.

    "Ba na son ganin shi ko kaɗan," in ji matar mai shekara 29 a duniya, wadda ke da yara huɗu.

    Neema wanda ba sunanta na gaskiya ke nan ba, ta kasance mai bin cocin Good News International da ke Minlindi har zuwa lokacin da aka rufe shi a 2019.

  12. Intanet da layukan waya sun dawo aiki a sassan Sudan

    An dawo da ayyukan sadarwa da na intanet a wasu yankuna da sojoji ke iko da su a Sudan bayan shafe kwanaki biyu na katse hanyoyin sadarwa, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.

    An mayar da ayyuka a Port Sudan da El Fashir da El Obeid, babban birnin Jihar Red Sea da North Darfur da North Kordofan, da kuma jihar Kogin Nilu da ke arewa maso gabashin kasar.

    Manyan kamfanonin sadarwa guda uku a kasar sun bayyana cewa katsewar wutar lantarki da intanet ta shafi jihohi 13.

    Kamfanonin dai sun alakanta katsewar wutar lantarki da intanet da “al'amuran da suka fi karfin mu”.

    Gwamnatin soja da Digital Rights Lab - Sudan, mai sa ido kan kafofin yada labarai, sun zargi kungiyar RSF da laifin ƙatsewar, amma kungiyar ta musanta zargin.

    RSF ta dora alhakin a harin bam din da sojojin suka kai kan cibiyoyin kamfanonin sadarwa a babban birnin kasar, Khartoum.

    RSF ce ke kula da cibiyoyin kamfanonin sadarwa a birnin Khartoum kuma ta zargi kamfanonin da gazawa wajen warware matsalar sadarwar da aka shafe tsawon watanni ana fama da ita a Darfur da Kordofan.

    Idan har hakan ya ci gaba da wanzuwa, tonon sililin zai kara ta'azzara matsalar jin kai a Sudan yayin da miliyoyin mutane ke dogaro da kudaden da ake biya ta intanet na abinci da sauran abubuwan da ake bukata.

    Sojoji da RSF sun yi musayar laifi a baya kan lalata manyan kayan more rayuwa bayan yaƙin da ya barke a watan Afrilun 2023.

  13. Senegal na dab da shiga ruɗani bayan ɗage zaɓe

  14. 'Kaso 30 na mace-macen Jarirai a Duniya na faruwa ne a Najeriya'

    Kwamitin Kwamishinonin Lafiya na Arewa maso Gabashin Najeriya ya nemi tallafi daga Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas, (NEDC) da ta tallafa wajen rage yawan mace-macen mata da jarirai a shiyoyin ƙasar.

    Ya ce kashi 30 cikin 100 na mace-macen mata masu juna biyu da jariran da aka haifa a duniya suna faruwa ne a Najeriya.

    Shugaban kwamitin, Farfesa Baba Mallam Gana ya bayyana hakan ne a wata ganawa da shugabannin hukumar NEDC kan hanyoyin inganta harkar lafiya a yankin.

    Ya ce matsalar mace-macen mata masu juna biyu da jarirai da sauran matsalolin da suka shafi mata masu juna biyu da ke dagula harkar lafiya a yankin arewa maso gabas na da matukar muhimmanci a magance su.

    “Bangaren kiwon lafiya a yankin Arewa maso Gabas na cikin wani mawuyacin hali a halin yanzu, musamman idan aka yi la’akari da yanayin mata da jarirai da yaran da ake haifa.

    “Hukumar NEDC ta yi ayyuka da yawa a fannin kiwon lafiya, amma a gaskiya, a yanzu mun fi buƙatar hukumar.

    “Mu na da masaniya kan ayyukan hukumar, kamar inganta asibitin ido zuwa matsayin kasashen duniya. Yanzu, za mu yi aiki tare da Hukumar NEDC don inganta harkokin kiwon lafiyar al’ummar Arewa maso Gabas,” in ji Gana.

  15. Firaministan Habasha ya musata cewa yunwa ta kashe mutane a ƙasar

    Firaministan ƙasar Habasha Abiy Ahmed ya musanta rahotannin da ke cewa fari ta haifar da yunwa da ta yi sanadiyar mutuwar mutane a kasar.

    A makon da ya gabata wata hukumar gwamnatin tarayya ta ce kusan mutane 400 ne suka mutu sakamakon yunwa a yankuna biyu - Tigray da Amhara.

    A halin da ake ciki kuma, Birtaniya ta sanar da kudi fam miliyan 100 na sabbin tallafin jin kai ga kasar dake yankin kahon Afirka.

    Da yake jawabi ga 'yan majalisar a Addis Ababa, Mista Abiy ya amince cewa Habasha na fuskantar fari.

    Amma a cewarsa babu wanda ya mutu sakamakon yunwa.

    Kalaman nasa sun zo ne bayan da jami'ai a yankin arewacin Tigray mai fama da yaƙin basasa sun yi gargadin barkewar yunwa mai kama da daya daga cikin mafi munin rikicin abinci a tarihin kasar da aka gani a tsakiyar shekarun 1980 wanda ya haifar da taron tara kudade na duniya na Live Aid.

    Gwamnati ta sha yin watsi da yuwuwar yunwa ce ta kashe mutane.

    Wani rahoto da Cibiyar Kula da Ombudsman ta Tarayya ta fitar ya nuna cewa tuni daruruwan mutane suka mutu sakamakon yunwa, yawancinsu a Tigray.

    A ranar Litinin, Birtaniya ta ce haɗewar yaki da fari da gazawar amfanin gona ya haifar da "hadarin bala'in bala'i" a Habasha.

  16. An tuhumi malamin addinin kirista na Kenya Paul Mackenzie da laifin kisa

    An tuhumi malamin addinin kiristan nan na Kenya, Paul Mackenzie da kisan kai bayan mutuwar mabiyansa da dama sakamakon tilasta musu yin azumin mutuwa.

    Paul Mackenzie da mukarrabansa 29 sun musanta yin laifi a gaban babbar kotu da ke Malindi.

    Fiye da gawawwaki 400 har da yara kanana aka hako a bara daga wani fili da ake zargin mallakin faston ne.

    Paul Mackenzie ya isa kotun cikin motar gidan yari. An ga kuma yadda yake magana da lauyoyinsa.

    Shi da mukarraban nasa sun musanta kashe mutum 191.

    Tun farko an tuhume shi da aikata ta'addanci da azabtar da kananan yara, zarge-zargen da ya musanta.

    Wadanda suka tsira sun shaida wa BBC cewa an buƙaci su yi azumi domin shiga aljanna, inda ya fara da yara.

    A baya Paul Mackenzie ya ce bai tilasta wa kowa yin azumi ba.

  17. Ana shirin ƙaddamar da talabijin mai goyon bayan 'yan adawa a Habasha

    A yau ne gidan talabijin na Anchor TV mai goyon bayan 'yan adawa da ke Amurka ya sanar da cewa an kafa wani sabon gidan talabijin na 'yan adawa mai suna Ethiopian Satellite Network (ESAN TV) don dakile " tashoshin da ake amfani da su wajen watsa farfaganda" da ake zargin gwamnatin firaminista Abiy Ahmed ke amfani da su..

    Rahoton ya ce tsoffin 'yan jarida na gidan talabijin na Ethiopian Satellite (ESAT TV) mai zaman kansa da ke zaune a kasashen waje sun kafa sabon gidan talabijin ne a matsayin hanyar yada labarai irin wanda ake ɓoyewa mutane.

    "ESAN TV ta bayyana cewa za ta fara watsa shirye-shirye na yau da kullun daga mako mai zuwa," in ji Anchor Tv, inda ta ƙara da cewa an gudanar da shirye-shiryen gwaji a ranar 1 ga Fabrairu.

    Ƙasar Habasha tana daya daga cikin kasashen da suka fi fuskantar rashin ‘yancin yaɗa labaran jarida mafi muni.

    Kwamitin Kare ‘Yan Jarida dai a bara ya bayyana damuwarsa game da daure ‘yan jarida.

  18. An kashe ƴan Habasha bakwai a Somaliya

    Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kashe ‘yan kasar Habasha bakwai a garin Beled Hawo na kasar Somaliya mai iyaka da kasar ta Habashar da Kenya.

    Wannan ya zo ne a daidai lokacin da ake zaman ɗar-ɗar a tsakanin Mogadishu da Addis Ababa dangane da yarjejeniyar tashar jiragen ruwa da jamhuriyar Somaliland mai cin gashin kanta, kamar yadda kafar Ethio Forum mai zaman kanta ta ruwaito a jiya.

    Akwa zaman ɗar-ɗar a tsakanin Somaliya da Habasha tun bayan da Somaliland ta amince da bai wa Addis Ababa damar shiga gaɓar teku mai tsawon kilomita 20 a mashigin tekun Aden domin amfani da soji da kasuwanci saboda a amince da ita a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

    'Yarjejeniyar dai ta haifar da fusata a fadin kasar Somaliya, wadda ta dauki Somaliland a matsayin wani yanki na kasarta.

    Har yanzu dai hukumomi a Somaliya ba su ce uffan ba game da kisan, kuma har yanzu ba a san dalilin maharan ba, a cewar rahoton.

    Sai dai kuma an ce waɗanda harin ya rutsa da su 'yan ƙabilar Oromo ne daga yankin Oromia, inda firaministan Habasha Abiy Ahmed ya fito.

    A ranar 16 ga watan Janairu, shafin Ethio Forum ya kuma ba da rahoton cewa, Habashawa da ke zaune a Somaliya, musamman ma 'yan kabilar Oromo, suna fuskantar tsangwama.

  19. An kuɓutar da matar basaraken da aka kashe a Kwara tare da kama mutum 13

    An kubutar da matar basaraken gargajiyar da aka kashe, marigayi Oba Olusegun Aremu-Cole wanda aka kashe a fadarsa ranar Alhamis.

    An dai yi garkuwa da mai dakin nasa a ranar Alhamis da daddare tare da wata mata guda. wanda ba a tantnace ko wace ce ba, a ƙaramar hukumar Ekiti ta jihar Kwara.

    An kuɓutar da su ne a daren ranar Litinin kuma sun isa garin Koro da misalin karfe 10:45 na dare.

    Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Ejire-Adeyemi Toun, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

    Ko da yake bai bayyana sunan mutum na biyu da aka kubutar ba, rahotanni sun ce ’yar sarauniyar ce.

    A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, aikin ceton ya biyo bayan wani aikin hadin gwiwa da jami’an hukumar tsaron farin kaya (DSS) da ‘yan sanda da sojoji da ‘yan banga da mafarauta suka yi.

    Ya ce jami’an tsaro sun kutsa cikin dajin da ke tsakanin jihohin Kwara da Ekiti bayan da Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin tura wani jirgin sama na ‘yan sanda domin binciken cikin dajin.

    "Wannan aiki ceton ya kai ga nasarar ceto matar marigayin da kuma wani mutum daya a ranar 5 ga watan Fabrairun 2024."

    Sanarwar ta kara da cewa tuni aka haɗa waɗanda aka kuɓutar din da iyalansu, cikin jin dadi.

    “A ci gaba da binciken, Sufeto Janar na ‘yan sanda IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya amince da tura jami’an ‘yan sanda ta jirgin sama domin bincike ta sararin samaniya domin taimaka wa Kwara da jihar EkitiI."

    Ejire-Adeyemi ya kara da cewa, "aikin ceton ya kuma kai ga kama wasu maza 13 da ake zargi da hannu a yanzu haka."

    "Wadanda aka kama dai suna fuskantar tambayoyi masu karfi da nufin taimakawa wajen cafke 'sauran mutanen da ke da alhakin kai harin baki daya."

  20. Muna son a yi sasanci kan ficewar kasashen Sahel daga Ecowas – Yan farar hula

    Gamayyar kungiyoyin farar hula a Najeriya sun yi kiran a tattauna domin jawo hankalin Mali da Nijar da Burkina Faso su zauna a kungiyar Ecowas kasancewar ficewarsu zai jawo cikas a yakin da ake da ta'addanci a yankin.

    Kasashen uku na yankin Sahel da ke karkashin mulkin sojoji sun sanar da kudurinsu na ficewa daga Ecowas ranar 28 ga watan Janairu inda suka ce "kungiyar ta zama barazana ga mambobinta".

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa gamayyar kungiyoyin ta bukaci a samar da matakai na hana rabewar kamar yadda ta sanar cikin wata sanarwa.

    "Ficewar nakasu ne ga burin samar da hadin kan tattalin arziki a Ecowas har da samar da tsarin kasuwanci maras shinge tsakanin kasashe mambobin kungiyar. Zai yi mummunan tasiri ga rayuwar mutanen Afirka ta Yamma," in ji kungiyoyin.

    Gwamnatin Najeriya ta soki kasashen uku saboda ficewa daga kungiyar inda ta ce sojojin sun dauki matakin ne domin burge jama'a.

    Yankin Afira ta Yamma na fama da matsalar tsaro da juyin mulki a wasu kasashe kuma rarrabuwar kan kungiyar Ecowas na iya tabarbara yanayin da galibin kasashen yankin ke ciki.