Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    To masu bibiyar wannan shafi na BBC Hausa da ke kawo muku labarai da rahotanni da suka shafi Najeriya da makwabtanta da sauran sassan duniya, kai tsaye a nan ne muke muku ban-kwana a yau Alhamis.

    A madadin kowa da kowa ni Muhammad Annur Muhammad nake fatan za su sake kasancewa da mu a gobe Juma'a idan Alllah Ya kai mu.

    Mu kwana lafiya

  2. 'Kashi 81 cikin ɗari na ma'aikatan Najeriya ba su da amfani'

    Kusan kashi 81 cikin ɗari na ma'aikatan Najeriya ba sa wani ɓangare da ke samar da cigaba ga tattalin arziƙin ƙasar, in ji shugaban kwamitin da shugaban ƙasar ya kafa na manufofi da tsare-tsaren kuɗi da sauye-sauye a haraji, Taiwo Oyedele.

    Oyedele ya ce duk da cewa yawan marassa aiki a Najeriya kaɗan ne inda yake kashi 4.2 cikin ɗari, yawancin 'yan ƙasar masu aiki ba su da wani amfani na ƙwarai ga tattalin arziƙin ƙasar.

    Mista Oyedele ya ce Najeriya na mataki ɗaya ne da Birtaniya wajen yawan kashin marassa aikin yi wato 4.2 cikin ɗari, kuma abin da ya sa kenan har yanzu Najeriya ta kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka fi talauci a duniya.

    Ya ce akwai mutum sama da miliyan 113 da ke cikin fatara a Najeriya a shekara ta 2022, kuma yana ganin shakka babu yawan a yanzu ya fi haka domin a lokacin ba a janye tallafin mai ba da kuma daidaita farashin canjin dala.

    Shugaban kwamitin na magana ne a wajen taron ƙoli na kasuwanci da zuba jari na Afirka a yau Alhamis, a Lagos.

    Oyedele ya ce kasancewar Najeriya ba za ta iya sauya alƙibilar tattalin arziin duniya ba, amma yin sauye-sauye a manufofinta ka iya taimaka wa halin tattalin arziƙin da ake ciki a ƙasar.

  3. An yanke wa jagoran 'yan hamayya na Tunisia ɗauren shekara uku

    Wata kotu a Tunisia ta yanke wa jagoran 'yan hamayya kuma mai sukar Shugaba Kais Saied hukuncin zaman gidan yari na shekara uku.

    Rasheed Ghannouchi, mai shekara 82 yana zaman gidan yari a yanzu haka na wata 15, kan zarginsa da tunzura mutane su ci mutuncin 'yan sanda.

    Lauyansa ya ce alƙalin ya yanke masa sabon hukuncin ne saboda bai wa jam'iyyarsa ta Ennahda kuɗi ba bisa ƙa'ida ba.

    A bara, hukumomin Tunisia suka haramta duk wani taro a ofishin jam'iyyar Ennahda, suka kuma rufe hedikwatarta a matsayinta na babbar jam'iyyar hamayya a ƙasar.

  4. Mahari ya yi garkuwa da mutane a kantin Amurka a Turkiyya

    'Yan sanda a Turkiyya sun ce wani mutum ya yi garkuwa da mutane da dama a wani ofishin kamfanin Amurka da ke kusa da babban birnin ƙasar Istanbul.

    Hotunan da suka karaɗe shafukan intanet sun nuna mutumin a tsaye a ƙofar shiga wajen sayar da kayan kwalliya na kamfanin Procter & Gamble.

    A jikin bangon da ke kusa da shi, an zana tutar Falasdinawa an kuma rubuta "za a buɗe wa Gaza ƙofofi" da jan rubutu.

    Mutumin yana sanye da wata riga mai abin fashewa a jikinta kuma yana rike da bindiga a hannunsa.

    'Yan-sanda sun zagaye yankin da yake, an kuma girke dakaru na musamman daga jami'an tsaro zuwa na lafiya a wurin.

  5. An buƙaci manoman Faransa su kawo ƙarshen zanga-zangar da suke yi

    Babbar ƙungiyar manoma a Faransa ta yi kira a kawo ƙarshen zanga-zangar rufe tituna a faɗin ƙasar bayan alƙawarin taimakon kuɗi da gwamnati ta yi musu.

    Firaiminista Gabriel Attal, ya bayyana wasu matakai da za a ɗauka a nan gaba domin kwantar da hankalin manoma da suke kuka da tashin farashin kayayyaki da kuma wasu dokokin Tarayyar Turai.

    Ya kuma janye yarjejeniyar kasuwanci da ƙasashen Latin Amurka tare da sanar da wasu hanyoyin kare abincin da suke fitar da shi ƙasashen ƙetare.

    Ba a dai sani ba ko sauran manoman da ke zanga-zangar a wasu wuraren za su haƙura su janye motocin da suka girke a kan tituna.

  6. Ƴan Arewa ba sa goyon bayan dattawan Katsina a kan Tinubu da zaɓen 2027 - Matawalle

    Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma ƙaramin ministan tsaro na Najeriya, Bello Mohammed Matawalle ya yi watsi da kalaman ƙungiyar dattawan jihar katsina a kan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 da cewa ba ra'ayin al'ummar arewacin Najeriya ba ne.

    Ministan na martani ne a kan barazanar da kungiyar dattawan (Katsina Elders' Forum) ta yi ne a kan shugaban ƙasar a kan matakin gwamnatinsa na mayar da hukumar kula da filayen jirgin sama na ƙasar da aikin faɗaɗa filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina da kuma wasu sassan babban bankin kasar daga Abuja zuwa Lagos.

    Wasu rahotanni da dama na cewa kungiyar dattawan ta buƙaci shugaban ƙasar da ya sauya shawara a kan wannan mataki da ya ɗauka ko kuma ya rasa goyon bayan al'ummar arewacin ƙasar a zaɓen 2027.

    Matawallen Maradun ya bayyana barazanar ƙungiyar ta Dattawan na Katsina da cewa ba komai ba ne illa wani yunƙuri na haddasa ƙiyayya da tsana da raba kai da kuma neman haddasa fitina tsakanin arewacin najeriya da 'yan uwansu na sauran sassan ƙasar.

    Ministan ya ce bai dace ba a ce dattawan sun yi waɗannan kalamai a madadin arewacin Najeriya duk da cewa sun sani sarai cewa ba ra'ayin yawancin al'ummar arewa ba ne

    Tsohon gwamnan na zamfara ya ce abin da arewacin Najeriya ke buƙata a yanzu shi ne tsaro ga rayuka da dukiyarsu, abin da ya ce Shugaba Tinubu ya duƙufa samarwa.

    Ƙaramin ministan tsaron ya kuma yi barazanar cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani abu da zai haifar da naƙasu ga dumukuraɗiyyar ƙasar da kuma haddasa ƙiyayya tsakanin arewa da sauran sassan ƙasar ba.

  7. Da ba a cire tallafin mai ba da wahalar Najeriya ta fi ta yanzu - Gwamnatin tarayya

    Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a na Najeriya, Alhaji Mohammed Idris Malagi ya ce, da gwamnati ba ta cire tallafin mai ba da wahalar da ake ciki a ƙasar ta fi haka a yanzu.

    Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake kare matakin gwamnatin ƙasar na cire tallafin mai a yayin wata hira da tashar talabijin ta Channels.

    A lokacin jawabinsa na farko bayan rantsuwa, a Abuja, a watan Mayu na 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu sauran tallafin mai.

    Tun daga lokacin da shugaban ya sanar da janye tallafin man kayayyaki da sauran harkokin rayuwa a Najeriya suke ta tashin gwauron zabo, rayuwa take ta kara tsada ga jama'a.

    Kafin cire tallafin man ana sayar da lita ɗaya a ƙasar a lokacin a kan naira 189 a watan Mayu, amma bayan sanarwar cirewar farashin ya koma daga naira 650 zuwa sama.

  8. MURIC ta soki kwamitin da gwamnatin Filato ta nada don warware rikicin Mangu

    Kungiyar kare 'yancin Musulmi a Najeriya, MURIC ta zargi gwamnanatin jihar Filato da nuna wariya da kyama ga al'ummar Musulmi saboda rashin sanya musulmi ko daya a cikin kwamitinta na tsaro da ta hada mai mutum 11 domin warware rikicin kabilanci a garin Mangu da kewaye.

    A ranar Laraba ne dai gwamnan jihar Filato, Caleb Manasseh Mutfwang ya nada kwamitin na tsaro na mutum goma sha daya domin nemo bakin zare dangane da yadda rikicin kabilanci ya dabaibaye al'ummar a 'yan watannin nan.

    Shugaban kungiyar ta MURIC, Farfesa Ishaq Akintola a wata sanarwa ga manema labarai "akwai alamar tambaya a ce kwamiti mai mutum 11 amma babu sunan Musulmi ko daya alhali kuma a cikin kabilun da ake rikicin da su a kwai Musulmi. Wannan ya nuna cewa da wuya a yi adalci."

    Sai dai gwamnatin jihar Filato ta ce mutane ba su fahimci ainihin aikin komitin ba ne, inda ta musanta zargin nuna wariyar da ake yi mata.

  9. Ukraine ta lalata jirgin ruwa mai dauke da makamai masu linzami na Russia

    Kasar Ukraine ta kai hari kan wani jirgin ruwan kasar Russia mai dauke da makamai masu linzami da ke kan Bahar-al-aswad.

    Jami'ai a Ukraine sun ce sojojinta ne na musamman na Group 13 suka kai harin da ya lalata jirgin ruwan.

    Tawagar bincike da ceto ta Russia ba ta iya yin katabus ba a wurin.

    Wani jami'i a ma'aikatar kasashen wajen Ukraine din Olexander Scherba ya bayyana harin da "abin sha'awa".

    Kasar Ukraine dai ta cimma wasu jerin nasarori a yakin da take da Baharal aswad inda take lalata ko jiragen yakin kasar Russia duk da cewa Ukraine ba ta da nata jiragen na kashin kanta.

    A watan Disamba, Ukraine dai ta ce ta lalata babban jirgin yaki na kasar Russia, Novocherkassakat Feodosia a yankin Crimea. Kuma kasar ta Rasha ta tabbatar da lalata jirgin nata.

  10. Amurka ta amince a kai jerin hare-hare kan muradun Iran da ke Syria da Iraqi

    Wasu jami'an gwamnatin Amurka sun shaida wa kafar watsa labarai ta CBS News cewa gwamnatin ta amince da tsare-tsaren kai jerin hare-haren kan muradan kasar Iran da ke kasashen Syria da Iraqi.

    Hare-haren za su kasance ne na 'yan kwanaki kamar yadda jami'an suka shaida duk da cewa ba a fayyace lokacin da za a kaddamar da hare-haren ba.

    Wannan dai na zuwa ne bayan wani harin jirgi maras matuki da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Amurka guda uku a kasar Jordan kusa da iyakar Syria a ranar Lahadi.

    Amurka ta zargin cewa mayakan sa-kai ne Islamic Resistence da ke goyon bayan Iran ne suka kai harin

    Ana dai zaton cewa kungiyar da ke Iraq tana da kungiyoyi masu tayar da kayar baya da dama a cikinta wadanda ke samun tallafi da makamai da horo daga dakarun juyin-juya hali na kasar Iran na Revelutionary Guards.

    Kungiyar ta dauki alhakin kai harin kan sojin na Amurka na ranar Lahadi.

    To sai dai kasar Iran ta musanta hannu a harin wanda ya kuma jikkata sojin Amurkan 41 a sansaninsu da ake kira Tower 22.

    Yayin wani taron manema labarai ranar Alhamis, Sakataren tsaron Amurka, Lloyd Austin ya ce Amurka "ba za ta amince da hare-hare kan sojinta" ba.

    "Za mu dauki dukkan matakan da suka dace wajen kariya ga Amurka da muradanmu da kuma al'ummarmu", in ji Lloyd. "Za mu mayar da martani a duk inda muka zabi yin hakan da kuma yadda muke son aiwatarwa."

    To sai dai jami'an Amurkar ba su shaida wa kafar ta CBS News komai ba game da hakikanin lokacin da za a aiwatar da hare-haren. Sai dai jami'an sun ce za su kaddamar da hare-haren ne a lokacin da yanayin sararin samaniyya ya yi muni to amma dai kuma za tabbatar an kai hare-haren ido na ganin ido domin rage yawan mutuwar fararen hula.

    A dai-dai lokacin da Amurkar ta sha alwashin mayar da martanin na harin jirgi maras matuki, shugaba Joe Biden da sauran jami'an tsaro sun ce Amurkar ba ta da burin fadada yaki da kasar Iran saboda gudun ta'azzarar rikici a yankin.

    "Ba abin da nake son gani ba kenan," kamar yadda mista Biden ya shaida wa 'yan jarida a Fadar White House a farkon wannan makon.

  11. Kotu ta bayar da belin Danbilki Kwamanda

    A jihar Kano, an saki fitattaccen dan siyasar nan Danbilki Kwamanda bayan da wata kotun majisteret ta bayar da belinsa.

    Lauyan Danbilki ya shaida wa BBC cewa an sake shi ne bayan ya cika sharuddan belin da kotun ta gindaya masa.

    Tun da farko dai an gurfanar da Kwamanda ne bisa zargin yin wasu kalamai da kotun ta ce ka iya tunzura al’umma waɗanda suka shafi batun masarautun Kano.

  12. Shugabannin ƙasashen kudancin Afirka za su yi taro kan cutar kwalara

    Shugabannin ƙasashen kudancin nahiyar Afirka za su gudanar da wani taro na musamman ranar Juma'a yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan ɓarkewar cutar kwalara a ƙasashen yankin da dama.

    Dubban mutane ne suka kamu da cutar yayin da ɗaruruwa suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar wadda ta ɓarke tun a cikin shekarar da ta gabata.

    Kwalara cuta ce da ke yaɗuwa ta hanyar gurɓataccen ruwa wadda ke iya kashe mutum cikin ƙanƙanin lokaci idan ba a ɗauki mataki cikin hanzari ba.

    Cutar ta fi ɓarkewa ne a wuraren da babu tsafta.

    A taron na ranar Juma'a, shugabannin ƙasashen Zimbabwe da Zambia za su mayar da hankali kan abubuwan da ke ta'azzara yaɗuwar cutar.

    Ana sa ran kuma za su tattauna kan hanyoyin da za a daƙile ci gaban yaɗuwar cutar.

    Hukumomi na Majalisar Dinkin Duniya sun ce a shekarar da ta gabata an samu mutum 200,000 da suka kamu da cutar, yayin da mutum 3,000 suka rasa rayukansu a ƙasashen Afirka 13.

  13. Ƴan kasuwar Kantin kwari sun yi addu'a kan matsin rayuwa a Najeriya

    Wasu ƴan kasuwa da ke hada-hada a kasuwar Kantin kwari da ke birnin Kano sun gudanar da addu'o'in neman samun sauƙi kan matsin tattalin arziƙi da ake ciki a Najeriya.

    Ƴan kasuwar sun fito daga kantunansu inda suka gudanar da sallah da addu'o'i tare da neman ɗauki daga ubangiji.

    Ɗaya daga cikin ƴan kasuwar mai suna Hamisu Sani ya shaida wa BBC cewa al'amura sun rincaɓe inda yanzu haka abinci ke gagarar al'umma.

    Ya ce "mun gudanar da addu'o'i domin samun ɗauki daga ubangiji kan wannan hali, domin ba mu san abin da shugabanni ke yi kan wannan hali ba."

    Ya ƙara da cewa "Buhun shinkafa da na sukari a yanzu haka sun gagari talaka."

    Tashin kayan masarufi ya munana a Najeriya cikin kwanakin nan.

    Lamarin ya ƙazance ne sanadiyyar wasu daga cikin shirye-shiryen da gwamnati ta ɓullo da su, kamar na cire tallafin man fetur.

  14. Tinubu ya koka kan yadda ake yi wa yan Najeriya kuɗin-goro kan miyagun laifuka

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya koka kan yadda ake yi wa ƴan Najeriya kuɗin goro da sunan masu aikata laifuka ta intanet.

    Ya ce irin wannan yana ɓata sunan akasarin al'ummar Najeriya da suke masu bin doka da oda. A cewar shugaban, an shafe tsawon shekaru ana yi wa ƴan Najeriya mummunar fahimta.

    Shugaba Tinubu wanda ke birnin Paris na Faransa ya faɗi haka ne cikin wani jawabi da mataimakinsa Kashim Shettima ya gabatar.

    Daga farkon shekarun 2000, ana kallon ƴan Najeriya a matsayin masu aikata ta'annati ta intanet - daga kutse da neman soyayya don samun kuɗi.

    Tinubu ya ƙara da cewa alaƙanta laifukan intanet da al'ummar Najeriya ba shi da hujja kuma ba ya nuna yadda rayuwar ƴan Najeriya take waɗanda aka san su a matsayin jajirtattu da gaskiya sannan suna bayar da gudumawa ga ci gaban kasashe ta fannoni da dama daga batun ƙirƙirarriyar basira zuwa ga fannin lafiya.

    A 2020 ne, hukumar binciken manyan laifuka a Amurka, FBI ta saka Najeriya a matsayin ta 16 a jerin ƙasashen da laifukan intanet ya fi shafa.

    Laifukan intanet na janyo wa Najeriya asarar dala miliyan 500 kowace shekara, kamar yadda hukumar kula da harkokin sadarwa a Najeriya ta bayyana.

  15. Mabiya addinin Hindu sun fara bauta a Masallacin Gnanabapi na Indiya

    Mabiya addinin Hindu sun fara ibada a wani masallacin Gnanabapi da ke Varanasi a Uttar Pradesh daga safiyar Alhamis bayan da kotu ta sahhale musu yin hakan.

    Kotun da ke Varanasi a ranar Laraba ta umarci masu tafiyar da al'amuran masallacin da su yi tanadi domin mabiya addinin na Hindu su fara bautar Puja a wajen.

    Wani jami'i a Varanasi, S Rajalingam ya shaida wa ƴan jarida a safiyar Alhamis cewa "Na bi umarnin da kotu ta bayar ".

    Irin haka ta taɓa faruwa shekaru 38 da suka wuce a ranar 1 ga watan Fabarairun 1986 lokacin da aka buɗe masallacin Babri da ke Ayodhya.

  16. Za mu sauya fasalin kasuwar tsohuwar Fanteka – Uba Sani

    Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya gana da shugabancin kungiyar yan kasuwar tsohuwar Fanteka da a baya-bayan nan ta fuskanci ibtila'in gobara da ta yi sanadiyyar salwantar dukiya mai yawa.

    A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, gwamnan ya bai wa yan kasuwar tabbacin sake sauya fasalin kasuwar ta hanyar hadakar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

    A cewar gwamnan, idan aka kammala gina sabuwar kasuwar, za ta zama cibiyar masu sa'anar hannu mafi girma a Najeriya.

  17. Yan canji a Abuja sun dakatar da hada-hada

    Kungiyar yan canji a Abuja, babban birnin Najeriya ta dakatar da hada-hadar musayar kudi har sai baba ta gani sakamakon karancin dala.

    Yan Najeriya dai sun dogara kacokan kan kudin Amurka - dala domin tafiyar da harkokin da suka shafi kudi.

    Abdullahi Dauran, shugaban yan canji a Abuja, ya shaida wa BBC cewa sun dauki matakin ne domin nuna wa yan Najeriya cewa sun damu da yadda ake samun karancin dala matsalar da ya dora kan ayyukan kamfanin da ke hada-hadar kuɗaɗe ta Intanet irin na Crypto.

    Lamarin na zuwa ne daidai lokacin da Babban bankin Najeriya ke kokari na daidaita kasuwar musayar kudaden waje.

    Babban bankin ya umarci bankuna su sayar da dala yau Alhamis tare da gargadin mutane kan boye dalar domin samun riba.

  18. Kasashen Kudancin Afirka sun yi watsi da kiran sa dokar ta baci kan kwalara

    Ministocin lafiya na kasashen da ke karkashin ƙungiyar raya ƙasashen Afrika sun yi watsi da shawarar gaggauta ayyana dokar ta ɓaci kan cutar amai da gudawa a yankin.

    Shugabar cibiyar yaƙi da cutuka masu yaduwa ta Afrika Sylvia Masebo, ta ce kamata ya yi kowacce ƙasa ta duba ta yanke hukunci kan ko za ta ayyana dokar ta bacin game da ɓarkewar kwalara ko kuma a a.

    Yayin magana a wani taron tattaunawa na cibiyar a Addis Ababa babban birnin Habasha, Ms Masebo wadda ta kasance ministar lafiya a Zambia ta bukaci kasashe mambobin kungiyar da su ƙirƙiro matakan da zasu dakile yaɗuwar annobar da ta ɓarke.

    Ta ƙara da cewa annobar ta shafi kasashe mambobin ƙungiyar ta SADC guda 15.

    Zambia na daga ƙasashen da ke fama da ɓarkewar annobar mafi muni a gomman shekaru inda aka samu rahoton mutuwar mutane kusan 600 yayin da sama da 16,000 suka kamu da cutar tun Oktoban shekarar da ta gabata.

    Kasar ta fuskanci ɓarkewar annobar kwalara aƙalla sau 30 tun 1977 inda ƙungiyar jin ƙai ta WaterAid ta ce ɓarkewar cutar a baya-bayan nan yafi muni tun 2017.

    Barkewar cutar cholera da ake fuskanta a yanzu ya shafi kasashen Zimbabwe da Malawi.

    Shugabannin SADC sun shirya yin taro ta intanet a ranar Juma'a domin duba shirye-shirye da kuma yadda za su fuskanci ɓarkewar cutar ta kwalara a yankin.

  19. Youtube ya goge tashar Emmanuel TV ta TB Joshua

    Kamfanin Youtube ya goge tashar da ke wallafa bidiyon marigayi Fasto TB Joshua saboda saba ka'idojin furta kalaman kiyayya.

    Matakin ya zo makonni bayan wani bincike da BBC ta gudanar inda kungiyar Open Democracy ta bankaɗo shaidun cin zarafin mata da azabtarwar da marigayin ya yi a lokacin da yake raye.

    Tashar Emmanuel TV ta taka rawa sosai wajen ɗaga faston da ya zama fitacce a duniya.

    A shekarar 2021 ne TB Joshua ya mutu sai dai cocinsa na Synagogue ya ci gaba da tafiyar da harkokinsa a karkashin mai ɗakinsa Evelyn Joshua.

    Har yanzu cocin bai ce komai ba kan cire tashar daga Youtube sai dai ya ƙaryata zarge-zargen da aka yi wa marigayin.

    Tashar ta Emmanuel TV tana da mabiya fiye da rabin miliyan a kafar ta Youtube sannan miliyoyin mutane ne ke kallon bidiyon da tashar ke wallafawa.

    Wannan ne karo na biyu cikin shekara uku da Youtube ya dakatar da tashar saboda take wasu dokokin tafiyar da tasha a Youtube.

    A wani bangare na binciken da BBC, OpenDemocracy ta yi nazari kan bidiyon da tashar Emmanuel TV take wallafawa inda ta gano akwai bidiyo akalla 50 na cin zarafi a Youtube.

    Tawagar kungiyar sun shigar da korafinsu kan bidiyon ga Youtube inda aka dakatar da tashar a ranar 29 ga watan Janairu.

  20. Yadda yan canji a Kano suka rufe shagunansu a safiyar Alhamis

    Kungiyar yan canji a jihar Kano ta ce daga yanzu za ta rika bude kasuwar hada-hadar canji daga karfe 12 na rana zuwa 6 na yammacin kowace rana.

    Yan canjin da ke kasuwar wapa sun dauki matakin rage lokutan da kasuwar ke ci a wani bangare na nuna fushi da yadda farashin dala ke ci gaba da hauhawa.

    Kungiyar ta ce za ta ci gaba da yin haka ne har sai farashin dala ya sauka.

    A baya kungiyar tana bude kasuwar ne da karfe 8 na safe zuwa 9 na dare.