Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi and A'isha Babangida

  1. Rufewa

    To jama'a mabiyan wannan shafi namu na BBC da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye wadanda suka shafi Najeriya da makwabta da kuma sauran sassan duniya, a nan muke sallama da ku a yau Talata.

    Sai kuma gobe Laraba idan Allah Ya kai mu za mu sake dawowa. A madadin kowa da kowa ni Muhammad Annur Muhammad nake mana fatan alheri.

  2. Isra'ila ta ce ba za janye sojojinta daga Gaza ba ko sako fursunonin Falandinawa

    Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya ce Isra'ila ba ta da niyyar janye sojojinta daga Gaza ko kuma ta sako dubban fursunonin Falasdinawa, lamarin da ke kawo cikas ga batun sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta.

    Kalaman nasa na baya-bayan nan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Hamas Ismail Haniyeh ya ce kungiyarsa na nazarin shawarar da aka gabatar bayan tattaunawa a birnin Paris - inda ya kara da cewa zai ziyarci birnin Alkahira domin tattaunawa kan lamarin.

    Daya babbar kungiyar da ke dauke da makamai a Gaza, Islamic Jihad, ta ce ba za ta shiga wata tattaunawa kan ‘yan Isra’ilan da aka yi garkuwa da su ba, sai sojojin Isra'ila sun janye gaba daya an kuma tabbatar da tsagaita wuta a Gaza.

    A karon farko kuma sojojin Isra'ila sun tabbatar da cewa sun malale ramukan karkashin kasa da kungiyar Hamas ta gina a Gaza da ruwan teku.

    A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce ta dauki matakin ne don yunkurin gurgunta karfin da Hamas ke da shi a karkashin kasa

    Ta ce, an gudanar da ingantaccen bincike kafin kwararo ruwan tekun don tabbatar da cewa ruwan sha da ke karkashin kasa bai gurbata ba.

  3. Isra'ila ta lalata fiye da rabin gine-gine a yankin Gaza - bincike

    Wani bincike da BBC ta gani ya nuna yadda fiye da rabin gine-ginen yankin Gaza suka lalace sakamakon yakin da Isra'ila ke yi tun bayan da kungiyar Hamas ta kai wa Isra'ilar hari a ranar 7ga watan Oktoba.

    Cikakken bayani na hotunan binciken sun nuna yadda luguden bamabamai a kudanci da tsakiyar Gaza ke kara kamari tun farkon watan Disambar 2023, inda al'amarin ya fi shafar birnin Khan Younis.

    Isra'ila dai ta sha nanata wa Falasdinawa da su yi kaura daga arewaci zuwa kudanci domin tsaronsu.

    Gidaje sun yi rug-rugu sannan shagunan da a baya suka cike da hada-hada yanzu sun zama turbaya, jami'o'i su zama kufai inda kuma gonaki suka zama filaye fetal.

    Shemomi ne kawai na 'yan gudun hijra ke karuwa a kan iyakar yankin kudancin kasar domin fakewar dubban mutanen da aka raba da muhallinsu.

    Falasinawa miliyan 1.7 kusan rabin al'ummar yankin ne aka raba da matsuganansu, inda kuma suke a tattakure domin fakewa a kudancin yankin kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta shaida.

    Karin bincike da BBC ta yi ya nuna irin girman barnar da aka yi wa gonaki.

    Rundunar sojin isra'ila, IDF ta ce tana harin kungiyar Hamas da kuma "gine-ginen 'yan ta'adda", a lokacin da aka kalubalance su kan girman abin da suke aiakatawa a Gaza.

    Wasu hotunan tauraron dan adam da BBC ta samu sun nuna irin girman barnar da yakin ya haddasa.

    Binciken ya kara nuna cewa an rugurguza gidaje da gine-gine tsakanin 144,000 zuwa 175,000 a zirin Gaza wato kimanin kaso 50 zuwa 61 na yawan gine-ginen yankin.

    Binciken dai wanda Corey Scher of City University of New York da Jamon on Van Den Hoek da ke jami'ar Oregon University da ke Amurka suka yi sun bayar da taswira ta bazata kan girman barnar da Isra'ila ta yi a Gaza.

  4. 'Yan a-waren Kamaru sun kai mummunan hari

    'Yan a-waren Kamaru na yankin da ke magana da Turancin Ingilishi sun kai wani mummunan hari a lardin kudu maso yammacin kasar ta tsakiyar Afirka.

    Zuwa lokacin bayar da wannan rahoto an tabbatar da mutuwar mutum daya, tare da raunata wasu da dama a harin da mayakan suka kai ranar Lahadi a birnin Buea.

    'Yan a-waren da ke fafutukar ballewa daga sauran sassan kasar da ke magana da Faransanci na tilasta wa jama'a kaurace wa harkokin kasuwanci su zauna a gida ba fita da nufin gurgunta harkokin tattalin arziki.

    Hukumomin kasar ta Kamaru ba su ce komai ba game da harin na ranar Lahadi, wanda shafin intanet mai zaman kansa mai suna Journal du Cameroun, ya ruwaito cewa an kona motoci biyar tare da barnata dukiya a lokacin.

  5. APC ta gargadi masu neman kujerar shugabancinta

    Shugabancin jam'iyyar APC ( All Progressives Congress), wadda ke mulki a Najeriya, ya yi gargadi ga magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kogi na baya-bayan nan, Yahaya Bello, da su guji neman haddasa rudani a jam'iyyar da cewa jam'iyyar tana da shugaba na kasa.

    Babban Sakataren jam'iyyar na kasa, Felix Morka, shi ne ya yi gargadin a wani taron manema labarai a yau Talata a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja.

    Sa'o'i 48 da Yahaya Bello ya sauka daga mulkin jihar Kogi inda ya damka wa sabon gwamnan da aka zaba Usman Ododo, shafukan sada zumunta da muhawara sun cika da jita-jitar cewa Bellon na sha'awar kujerar shugabancin jam'iyyar.

    A ranar Litinin an ga yadda hotunan tsohon gwamnan na Kogi suka yanyame titunan Abuja har da sakatariyar jam'iyyar da ke babban birnin Najeriyar.

    To amma bayan taron babban kwamitin zartarwa na jam'iyyar, sakataren yada labaranta ya fito da sanarwa inda yake jaddada cewa a yanzu akwai wanda yake kan kujerar shugabancin jam'iyyar - wato tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

    Ya kara da cewa har yanzu Ganduje ne shugabansu saboda haka babu maganar takarar kujerar a yanzu kamar yadda magoya bayan Bello suke yadawa.

    Ya ce kodayake wannan lokaci ne na dumukuradiyya to amma yana gargadin masu yada wadannan hotuna da su bari.

    Saboda a cewarsa jam'iyyar na son mayar da hankali ne a kan yadda za ta daidaita al'amuran kasa a yanzu amma ba shugabancinta ba wanda ba su da matsala a kanshi.

    Sai dai kuma tsohon gwamnan jihar ta Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya nesanta kansa da wannan kamfe da ke danganta shi da neman kujerar shugabancin APC.

    Wata sanarwa da ofishin yada labarai na tsohon gwamnan ya fitar yau Talata ta zargi shugabannin hamayya da wadanda ya kira makiya a cikin jam'iyyar tasu da kitsa wannan abu domin bata sunan tsohon gwamnan.

  6. Sojojin Mali sun kashe "yan ta'adda" a tsakiyar kasar

    Sojojin kasar Mali sun ce sun kashe mayakan sa-kai da dama wadanda suka kai wa wasu kauyuka guda biyu hare-hare a yankin tsakiyar kasar.

    A ranar Lahadi ne dai da misalin karfe 6:30 na safe 'yan ta'adda da dama suka far wa kauyukan Fabacoura da Bouyagul a lokaci guda al'amarin da ya ahddasa mutuwar fararen hula masu dama.

    A wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojojin ta ce rundunar sojin sama bayan samun bayanai sun gano inda mayakan suke a wani daji inda kuma suka kai "samamen da aka yi dace na tarwatsa 'yan ta'addar".

    Rahotannin baya-bayan nan dai sun nuna yadda dazuka a tsakiyar kasar ta Mali suka zamo maboyar mayaka.

  7. Shugaba Tinubu ya ba da umarnin ceto daliban da aka yi garkuwa da su a Ekiti

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi allawadai da kisan masu sarauta guda biyu a jihar Ekiti wato Onimojo of Imojo-Ekiti, Oba Olatunde Samuel Olusola da Elesun of Esun-Ekiti, Oba David Babatunde Ogunsola.

    A wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan yada labarai, Chief Ajuri Ngelale ya fitar, shugaban ya sha alwashin hukunta wadanda suka aikata kisan.

    Shugaban ya kuma bai wa jami'an tsaro umarnin ceto dalibai da malaman da aka yi garkuwa da su a yankin Eporo-Ekiti da ke jihar ta Ekiti

    A ranar Litinin ne dai masu garkuwa da mutane suka sace yara dalibai guda shida da malamansu guda uku a kan hanyarsu ta komawa gidajensu.

  8. An bai wa iyalan 'yan sandan da suka mutu naira miliyan 135 a Zamfara

    Kwamishinan 'yan sanda na jihar Zamfara, Cp Muhamamd Shehu Dalijan ya mika cekin kudi na fiye da naira miliyan 134 ga iyalai 25 'yan sandan da suka rasu a kan aikinsu.

    Kudin dai na daya daga cikin alkawuran kyautata walwala da jin dadin iyalan kamar yadda Sifeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun ya dauka.

    Da yake mika musu cakin kudin, Cp Muhamamd Shehu Dalijan ya shawarci iyalan da su tabbatar sun yi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace.

  9. Ma'aikatan CBN akalla 1,500 da aka mayar Lagos daga Abuja sun tafi

    Akalla ma'aikata 1,500 na Babban Bankin Najeriya da aka mayar da ofisoshinsu Lagos daga Abuja za su fara aiki a sabbin ofisoshinsu da ke Lagos din ranar Juma'a.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa wata kafa a Babban bankin ta tabbatar wa wakilinta cewa , duk da cewa matakin dauke wasu sassan bankin daga hedikwatarsa zuwa Lagos ya gamu da suka sosai to amma duk da haka bankin ya ci gaba da aiwatar da shirin, inda a ranar Juma'a mai zuwa wasu daga cikin ma'aikatan da abin da ya shafa za su fara aiki a ofishin na Lagos.

    Babban Bankin na Najeriya ya ce ya dauki matakin mayar da wasu daga cikin sassanshi Lagos daga Abuja saboda abubuwa da dama, wadanda suka hada da rage cunkoso a hedikwatar da ke Abuja.

    Duk da cewa kungiyar dattawan Arewa (Northern Elders Forum) da wasu kungiyoyin arewacin kasar sun soki matakin amma gwamnan babban bankin ya kuduri aniyar tabbatar da shirin, wanda ake cewa ana sa ran zai rage yawan ma'aikatan da ke hedikwatar a Abuja daga ma'aikata 4,233 zuwa 2,733.

  10. Hamas ta ce za ta yi nazari kan sabuwar shawarar tsagaita wuta a Gaza

    Hamas ta ce za ta yi nazari kan sabuwar shawarar yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin da take yi da Isra'ila a Gaza, yayin da sojojin Isra'ilar ke ci gaba da kai hare-hare.

    Shugaban Hamas Ismail Haniyeh ya ce kungiyarsa ta karbi shawarwarin da aka gabatar bayan tattaunawa a birnin Paris - inda ya kara da cewa zai ziyarci birnin Alkahira domin tattaunawa.

    A Isra'ila, ministan tsaron kasar Itamar Ben Gvir, ya yi barazanar durkusar da gwamnati idan har aka amince da abin da ya kira yarjejeniya ta rashin hankali da Hamas.

    Sama da Falasdinawa 20,000 ne Isra'ila ta kashe a Gaza, tun bayan hare-haren ba-zata na ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai Isra'ila.

    haka kuma zaman dar-dar ya karu a Gabar Yamma tun bayan hare-haren bazata na ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai Isra'ila, inda a yanzu Isra'ila ke kai hari kusan kullum tare da dauki ba dadi da Falasdinawa.

  11. Yunwa ta kashe kusan mutum 400 a Habasha

    Wani jami'in kasar Habasha ya ce kusan mutane dari hudu ne suka mutu a yankunan arewacin kasar na Tigray da Amhara sakamakon yunwa da fari ya janyo.

    Endale Haile, ya shaida wa BBC cewa mace-macen sun faru ne cikin wata shida da suka gabata.

    Kalaman dai sun ci karo da wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar a birnin Addis Ababa da cewa babu wani tabbaci kan mutuwar mutane sakamakon yunwa.

    A watan Disamba, jami'ai a yankin Tigray sun yi gargadin cewa matukar ba a dauki matakan gaggawa ba, za a fuskanci yunwar da ta fi karfin wadda kasar ta yi fama da ita a tsakiyar shekarun 1980.

  12. An kaddamar da kwamitin samar da sabon mafi kankantar albashi a Najeriya

    Mataimakin shugaban kasar Najeriya Kashim Shettima ya kaddamar da kwamitin mutum 37 da zai bayar da shawara kan sabon mafi kankantar albashi a kasar.

    An rantsar da kwamitin ne wanda yake karkashin jagorancin tsohon shugaban ma'aikata na kasar, Bukar Aji , a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

    A jawabin da ya gabatar a wurin mataimakin shugaban kasar ya ce, kaddamar da kwamitin abu ne da ya tabbatar da alkawarin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi na inganta jin dadin ma'aikata

    Kwamitin wandaya kunshi bangaren gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da 'yan kwasuwa da kuma kungiyoyin kwadago zai bayar da sahawara ne kan abin da ya kamata a tsayar a matsayin sabon albashi mafi kankanta a kasar, inda a yanzu naira 30,000 ne.

    Idan kwamitin ya mika shawararsa bangaren zartarwa zai mika ta a matsayin kudurin doka ga majalisar dokokin kasar domin samun amincewa.

  13. Sojojin Nijar sun kori ƴan ƙasashen yamma 15

    Sojojin da ke mulki a Nijar sun kori yan kasashen yamma 15 ciki har da shugabar wani shirin Tarayyar Turai na tallafa wa farar hula.

    Kafar yada labarai ta Faransa, RFI ta ruwaito cewa an hana shugabar shirin Eucap, yar Jamus mai suna Katja Dominik shiga kasar bayan da ta sauka a filin jirgin sama na Yamai cikin dare a karshen mako.

    Lamarin na zuwa ne makwanni kaɗan bayan da sojojin suka soke kawancen tsaron da ke tsakanin kasar da Tarayyar Turai tare da janye amincewarsu ga Eucap Sahel Nijar, wani shirin turai mai mutum 120 da aka kafa a 2012 domin taimaka wa sojojin kasar.

    Bayan da sojojin na Nijar suka hambarar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum a watan Yuli, EU ta sanar da kakaba takunkumai kan sojojin.

    A martaninsu, sojojin sun raba gari da kawayen kasar na kasashen Yamma.

    Tuni dai Nijar ta karkata ga Rasha domin samun tallafin tsaro da kayan noma da kuma makamashi.

  14. Sojojin ruwan Indiya sun ceto 'yan Pakistan 19 daga hannun 'yan fashin tekun Somaliya

    Sojojin ruwan Indiya sun kubutar da 'yan kasar Pakistan 19 bayan da 'yan fashin tekun Somaliya suka kama jirgin ruwansu na kamun kifi a gabar tekun ƙasar.

    'Yan fashin teku 11 na Somaliya sun shiga jirgin ruwan kamun kifi mai suna Al Naeemi da ke ɗauke da tutar Iran inda suka yi garkuwa da dukkan ma'aikatan jirgin, in ji rundunar sojin ruwa.

    Jami'an sojojin ruwan da suka amsa "sun tilasta sakin ma'aikatan jirgin da kuma jirgin" bayan da jirgin ruwan INS Sumitra na Indiya ya kama jirgin da aka yi awon gaba da shi, in ji rundunar sojojin ruwan Indiya a ranar Talata.

    Kuɓutar da 'yan Pakistan din dai shi ne aikin yaƙi da 'yan fashin teku na biyu da INS Sumitra ta kai cikin sa'o'i 36.

    A sa'o'i kadan da suka gabata sun kuɓutar da wasu mutane 17 da 'yan fashin tekun Somaliya suka yi garkuwa da su a wani jirgin ruwan kamun kifi mai ɗauke da tutar Iran a mashigin tekun Aden.

    Akwai fargaba game da ƙaruwar hare-haren da ake kai wa jiragen ruwa a gaɓar tekun Somaliya a daidai lokacin da mayakan Houthi ke kai hare-haren makamai masu linzami a baya-bayan nan a tekun Bahar Maliya.

  15. Cin hanci da rashawa sun ragu a Najeriya – Cislac

    Wata kididdiga da kungiyar Transparency International ta fitar kan rashawa ta nuna cewa an samu ci gaba wajen yaki da matsalar a Najeriya inda a yanzu kasar ke mataki na 145 cikin kasa 180 da aka yi nazari a kai.

    Kididdigar ta nuna cewa Najeriya ta kara maki daya kan maki 24 da take da shi a baya inda a yanzu take da maki 25 cikin 100 baya ga matsawa daga matsayinta na 150.

    Kididdigar na duba yadda yanayin matsalar rashawa take a gwamnatin kasashen da aka yi nazarin su.

    Tana bai wa kowace kasa maki daga 0 zuwa 100 - 0 na nufin matsalar rashawa ta yi katutu yayin da 100 ke nufin nasara a yaki da rashawa.

    Cibiyar Rajin Kyautata Ayyukan Majalisun Dokoki da Yaƙi da Rashawa a Najeriya CISLAC wadda ta gabatar da jadawalin a Abuja, ta ce makin da Najeriya ta samu kasa yake da maki 33 na kasashen da ke kudu da hamadar sahara.

    Jadawalin bai fito da bayanan rashawa ba a kasar amma ya bayyana yadda ake kallon cin hanci a Najeriya.

    Cislac ta ce kididdigar ba wai tana nazarin ayyukan hukumomin yaki da rashawa ba ne da ta ce suna kokari wajen yakar cin hanci a Najeriya.

  16. Kalli yadda ƴan Ivory Coast suka kwana suna murnar nasara kan Senegal a gasar Afcon

    Ƴan ƙasar Ivory Coast sun kwana suna murna bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar ta doke Senegal a wasan zagayen ƴan 16.

    Ivory Coast ta doke Senegal ne a bugun fenareti bayan an tashi wasan kunnen-doki 1-1.

    Ivory Coast za ta kara ne da tawagar Cape Verde a zagayen kwata-fainal na gasar ta Afcon wadda Ivory Coast ɗin ke karɓar baƙunta.

  17. An sace dalibai bakwai da malaman makaranta a Ekiti

    Yan bindiga sun sace dalibai shida da malamai uku daga wata makaranta a jihar Ekiti da ke Kudu maso yammacin Najeriya.

    Gwamnatin ta ce lamarin ya faru ne ranar Litinin da daddare wanda shi ne karon farko da aka sace daliban makaranta a Najeriya a wannan shekarar.

    Yan bindiga sun sha sace mutane da matafiya da dalibai don neman kudin fansa yayin da Najeriya - kasa mafi yawan al'umma a Afirka ke fama da matsalar tsaro da rikicin masu ikirarin jihadi a arewa maso gabashin kasar.

    Gwamnatin jihar ta Ekiti cikin wata sanarwa ta ce lamarin ya faru ne lokacin da daliban da malaman ke dawowa daga wata tafiya da suka yi.

    Direban motar shi ma yana hannun masu garkuwa. Hukumomin tsaro a jihar sun ce sun soma bincike domin gano masu hannu a garkuwar, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Zuwa yanzu dai babu wanda ya dauki nauyin sace mutanen ko ma neman kudin fansa.

  18. Atiku ya soki Tinubu kan 'tafiya hutu' lokacin da ake kashe mutane a Najeriya

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya caccaki shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu kan yadda yake tafiye-tafiye a daidai lokacin da kasar ke dabaibaye da kalubalen tsaro.

    Atiku wanda ya yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaɓen 2023 ya bayyana haka ne a shafinsa na X inda ya ce masu garkuwa da mutane na cin karensu babu babbaka a kasar.

    Ya bayar da misali da yadda yan bindiga suka kashe wata uwa mai shayarwa da dattijuwa a Abuja saboda gaza biyan kudin fansa da kashe sarakunan gargajiya biyu a jihar Ekiti.

    A cewarsa Najeriya na bukatar shugaban da ba ya bukatar hutu domin tunkarar kalubalen tsaro da tattalin arziki da ke durkushewa.

    • Hujjojin kotun ƙoli na yin watsi da ƙarar Atiku da Obi kan nasarar Tinubu
    • Babu hujjar da ke nuna cewa takardun digirin Tinubu na bogi ne
  19. Sojoji sun kuɓutar da mutum 35 tare da kashe ƴan bindiga biyu a Katsina

    Rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadarin Daji (OPHD) ta ce ta yi nasarar kashe ƴan bindiga biyu a jihar Katsina tare da kuɓutar da wasu mutum 35 da aka yi garkuwa da su a wani samame da sojojin suka yi a jihar a ranar 27 ga watan Janairu.

    Kakakin Rundunar, Kyaftin Yahaya Ibrahim ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

    Ya bayyana cewa wasu 'ƴan ta’adda' da dama sun tsere da raunukan harbin bindiga.

    Sanarwar ta kara da cewa "A yayin farmakin, sojojin sun yi arangama da masu ɗauke da makamai, inda suka kashe biyu daga cikinsu yayin da wasu suka tsere da mummunan raunin bindiga."

    “A ci gaba da gudanar da ayyukan share fage na lokaci guda a yankunan da ke da alhakin gudanar da ayyuka a jihar wanda ya ci gaba da samun gagarumar nasara, dakarun rundunar hadin gwiwa ta operation hadarin daji da ke aiki a jihar sun ceto mutane 35 da aka yi garkuwa da su tare da kashe wasu ‘yan ta’adda biyu a jihar Katsina a wani samame da suka kai."

    Ya ce waɗanda aka ceto sun haɗa da maza 19 da mata 12 da kuma yara huɗu, ya ce nan take kwamandan rundunar, Birgediya Janar Oluremi Fadairo ya miƙa su ga gwamnatin jihar Katsina.

  20. Gamayyar kungiyoyin farar hula ta buƙaci Tinubu ya sa dokar ta ɓaci kan tsaro

    Wasu kungiyoyin farar hula 48 sun yi kira kan shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ayyana dokar ta baci kan sha'anin tsaro a kasar.

    Gamayyar kungiyoyin ta yi wani taron manema labarai a Abuja, babban birnin kasar ranar Litinin.

    A makon da ya gabata ne aka kashe mutum 43 a wani rikici da aka shafe kwanaki biyu ana yi a jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya inda a Abuja kuma aka samu jerin sace-sacen mutane don kudin fansa.

    Auwal Musa wanda ya yi magana a madadin gamayyar, ya ce mutum 2,423 aka kashe a mummunan yanayi yayin da aka sace kusan mutum 1,872 tsakanin Mayun 2023 lokacin da Shugaba Tinubu ya karbi ragamar shugabanci da 26 ga watan Janairun bana.

    Ya ce sun damu matuka da yadda ake yawaita sace mutane yana mai bayyana cewa farko-farkon Janairun 2024, an samu mutum 230.

    A baya-bayan nan rundunar yan sanda a Abuja ta kaddamar da runduna ta musamman domin dakile masu sace-sacen jama'a.

    • Rikicin Filato: 'Na ga gawawwaki yashe a kan titi'
    • Yadda sabon rikici a Filato ya janyo saka dokar hana fita a Mangu
    • Yadda sojin Najeriya suka yi wa ƴanbindiga ruwan wuta a Kaduna