A zaman kotun Majalisar Ɗinkin Duniya kan kiran Isra'ila da tsagaita buɗe wuta Gaza, alƙaliya Joan Donoghue ta karanto wasu wasiku da kalamai da manyan jami'an Majalisar Dinkin Duniya suka yi game da rikicin jin kai a Zirin Gaza.
Wasu daga cikin waɗannan wasiƙun sun lura da rugujewar al'ummar Gazan kuma rikicin jin kai yana ƙara ta'azzara.
Donoghue ta ce kotun ta yi la'akari da cewa fararen hula a Gaza na cikin mawuyacin hali.
Ta lura cewa ana ci gaba da kai farmakin sojin Isra'ila kuma Firaministan ya ce yaƙin zai ɗauki watanni masu yawa.
Isra'ila ta ce ta dauki matakin rage cutar da fararen hula amma yayin da irin wadannan matakan "ya kamata a karfafa su", alƙaliyar ta ce ba su wadatar ba.
Donoghue ta ce dole ne Isra’ila ta tabbatar da gaggawar cewa dakarunta na soji ba su aikata wani abu daga cikin wadannan ayyuka ba – kashe Falasdinawa ko kuma haifar da mummunar illa a jiki ko ta kwakwalwar mutane.
Ta kara da cewa, "Dole ne Isra'ila ta Ɗauki matakan da za ta iya Ɗauka don hanawa da kuma hukunta masu tunzura jama'a na yin kisan kare dangi kan 'yan kungiyar Falasdinawa."
Dole ne Isra'ila ta dauki matakai masu inganci cikin gaggawa don ayyukan yau da kullun da kuma matakan jin kai, in ji ta.
Donoghue ya ce dole ne Isra'ila kuma ta mika rahoto ga kotu a cikin wata guda da wannan umarni.