Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, Habiba Adamu, Awwal Ahmad Janyau and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Jama'a mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Da fatan kun ji daɗin labaran da muka kawo muku a yau.

    Sai kuma gobe cikin yardar Allah.

    Ahmad Bawage ke cewa Allah Ya ba mu alkhairinsa.

  2. Tankokin yaƙin Isra'ila sun toshe hanyar fita daga Kudancin Gaza - Falasɗinawa

    Falasɗinawa a Kudancin Gaza sun ce tankokin yaƙin Isra'ila sun tare masu hanyoyin guduwa daga yaƙin da ake gwabzawa a birnin Khan Younis.

    Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce dakarun Isra'ila sun riƙa yin harbi kai-tsaye cikin ginin asibitin Nasser.

    Har yanzu dai rundunar sojin Isra'ila ba ta ce komai ba a kan batun.

    Shugaban hukumar kula da ƴan gudun hijira ta MDD ya ce akwai mutane da dama da suke neman mafaka a cikin Asibitin.

  3. Sojojin Najeriya sun kuɓutar da mutum huɗu da aka yi garkuwa da su a Kebbi

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kuɓutar da wasu mutum huɗu da aka yi garkuwa da su a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    Wani samame da sojojin rundunar shiyya ta 8 suka kai sansanonin ƴan bindiga a ƙauyen Sabon Gari da ke karamar hukumar Shanga a yau Talata, tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro na Cibil Defence da kuma ƴan sa-kai ne ya kai ga ceto mutanen.

    Wata sanarwa da mataimakin darektan yaɗa labaru na rundunar soji a Gusau, Kaftin Yahaya Ibrahim ya fitar, ya ce sun kuma samu nasarar kashe wani ɗan bindiga guda ɗaya.

    Ya kuma ce sun yi nasarar ƙwato bindigogi da harsasai.

    Sanarwar ta ce tuni mutanen da aka kuɓutar da suka kunshi maza huɗu, suka haɗu da iyalansu.

  4. An tasa ƙeyar Danbilki Kwamanda zuwa gidan yari a Kano

    An kama wani babban ɗan'adawa a Kano Danbilki Kwamanda tare da tasa keyarsa zuwa gidan yari.

    Tun da farko dai an gurfanar da Kwamanda bisa zargin yin wasu maganganu da ake zargin za su iya tunzura al’umma waɗanda suka shafi batun masarautun Kano.

    Hukumar DSS ce ta fara gayyatarsa tare da miƙa ga shi ƴan sanda, kamar yadda Lauyan da ke kare shi Barriser Ibrahim Abdullahi ya tabbatar wa BBC.

    "Ana zarginsa da yin wasu kalamai na tunzura jama'a kan batun masarautu a jihar Kano," in ji shi.

    Sai dai ya musanta zargin da ake ma sa a kotun.

    Ya yi kalaman ne a wani gidan rediyo a Kano, bayan kalaman jagoran Kwankwasiyya Rabi'u Musa Kwankwaso kan batun makomar masarautu a jihar ta Kano.

    A cikin kalamansa da suka janyo kama shi, Danbilki ya ce ba za su yarda da cire sarakunan ba.

    Kotu ta bayar da umarnin tafiya da shi gidan gyaran hali na Goron Dutse a Kano.

    Sai a ranar 29 ga watan Janairu kotu za ta saurari buƙatar belinsa, kamar yadda lauyansa ya bayyana.

  5. MDD ta ce yawan kisan gillar da ake yi a Haiti ya ƙaru a 2023

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce yawan kisan gillar da ake yi a ƙasar Haiti ya ruɓanya a 2023.

    Wani rahoton Sakatare Janar na MDD, António Guterres, ya ce mutane aƙalla 4,800 aka kashe a bara.

    Mista Guterres ya damu matuƙa da rikicin ƙungiyoyin ƴan daba da ake fama da shi.

    Da wannan ƙididdiga dai, Haiti ta shiga jerin ƙasashe masu fama da mummunan rikici a duniya.

  6. DSS ta kama Bello Bodejo kan kafa rundunar sa-kai ta Fulani

    Jami'an hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kama shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo, kan kafa rundunar sa-kai ta Fulani a jihar Nasarawa.

    Wasu shuagabannin kungiyarsa ta Kautal Hore kuma makusanta sun tabbatar wa BBC da batun kama Bodejo a yau Talata.

    Sun ce jami'an DSS tare da wasu sojojin Najeriya suka kama shi a garin Lafiya babban birnin jihar Nasarawa.

    Sai dai sun ce suna bin bahasi domin ba su san inda aka tafi da shi ba.

    A ranar Laraba 17 ga watan Janairu Bello Badejo ya ƙaddamar da rundunar a garin Lafiya inda ya ce za ta taimaka wajen yaƙar ɓarayi da ɓata-gari daga cikin Fulani

    Bayanai na cewa jami'an tsaron Najeriya sun kama Bodejo ne kan fargabar cewa kirkiro da ƙungiyar sa-kai zai iya janyo tashin hankali a faɗin ƙasar, kuma kasancewar ba ta da rijista da hukumar farin kaya ta DSS.

  7. West Ham ta ɗauki aron Phillips daga Man City

    West Ham ta kulla yarjejeniyar da Manchester City don daukar aron Kalvin Phillips zuwa karshen kakar bana.

    Phillips, mai shekara 28, ya saka hannu kan kunshin kwantiragin kaka shida lokacin da ya koma Ettihad daga Leeds kan £45m a Yulin 2022.

    To sai dai ba ya samun buga wasanni sosai karkashin Pep Guardiola, wanda ya buga karawa biyu kacal a bana.

    Phillips, wanda Juventus ke son dauka, na daf da zuwa West Ham a makon nan domin a auna koshin lafiyarsa.

    West Ham ce za ta dinga biyan albashin ɗan kwallon, haka kuma za ta iya mallakar Philips a karshen kakar nan, idan ya taka rawar gani.

    Kungiyoyi da dama sun yi sha'awar daukar Philips, amma City ta bukaci kudi mai yawa kafin ta amince ta bayar da aronsa.

    Phillips, wanda mamba ne a tawagar Ingila da Gareth Southgate ke jan ragama, zai koma Ingila ranar Talata tare da ƴan wasan City daga ɗan atisayen da kungiyar ta yi a Abu Dhabi.

    Daukar Philips da West Ham za ta yi zai taimaka wa kungiyar, bayan da koci, David Moyes ke kokarin kara karfin kungiyar mai fama da ƴan wasa da ke jinya.

  8. Blinken na ganawa da Tinubu a fadar shugaban ƙasa

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken na ganawa da tawagar gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu.

    Tattaunawar za ta shafi hulɗar dangantaka a fannin tsaro, karfafa ɓangaren lafiya da kuma ci gaban tattalin arzikin yankin.

    Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar ne ya fara tarbar Blinken lokacin da ya isa fadar shugaban ƙasa.

    Najeriya ce ƙasa ta uku da Blinken ke ziyarta a rangadi da yake yi zuwa ƙasashen yammacin Afrika da zimmar ganin ɗorewar tasirin Amurka a Afrika.

  9. An samu raguwar haɗura da kashi 22 cikin 100 a Najeriya – FRSC

    Hukumar kare afkuwar haɗura ta Najeriya, FRSC ta ce an samu raguwar haɗura a ƙasar da kashi 22 cikin 100 a 2023 saɓanin adadin da aka samu a 2022.

    Ta ce jumullar mutum 5,081 ne suka mutu sanadiyyar haɗuran da suka faru a sassan ƙasar a 2023.

    FRSC ta kuma ce kimanin haɗura 10,617 ne suka faru sai mutum 31,874 da suka ji rauni.

    Shugaban FRSC, Dauda Biu ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai game da ayyukansu a 2023.

    Kididdigar a cewar Biu, ya nuna an samu raguwa sosai a hatsari da mace-mace da kuma raunuka idan aka kwatanta da shekarar 2022.

    Haɗuran sun faru saboda take dokokin tuki da gudu fiye da kima da yawan tafiye-tafiyen dare da shan gaban motoci ba bisa ka'ida ba kamar yadda shugaban hukumar ya bayyana.

  10. Sau ɗaya kacal a shekara za a ziyarci Raudah a Masallacin Annabi - Saudiyya

    Ma'aikatar Aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta bayyana cewa daga yanzu sau ɗaya a shekara musulmi za su samu damar ziyartar Raudah a masallacin Annabi, wuri na biyu mafi tsarki a Musulunci.

    Kafar yaɗa labarai ta Haramain Sharifain mai kula da ayyukan ibada a Masallatan Harami na Makkah da Madina ta tabbatar wa da BBC da matakin.

    "Daga yanzu za a riƙa ba da izinin ziyartar Raudah wuri mai daraja sau ɗaya a shekara," in ji sanarwar.

    A cewar ma'aikatar aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya mutanen da ke da sha'awar ziyartar Raudah za su iya yin takardar izini bayan shekara ɗaya da kai ziyara.

    Raudah Al Sharifa, wani ɓangare ne na gidan Manzon Allah SAW da ke cikin Masallacinsa a Madina wanda kuma ke ɗauke da ƙabarinsa.

    Ma'aikatar ta Hajji da Umrah ta ce dole ne Musulmi masu ibada da ke son yin addu'a da ziyartar Rawdah su samu izini a hukumance kafin ziyarar.

    Bayan kammala aikin Umrah ko aikin hajji a babban Masallacin Harami, wuri mafi tsarki na Musulunci a Makkah, yawancin mahajjata na ziyartar Masallacin Annabi don yin addu'a da kuma nuna girmamawa gare shi.

    Ƙasar Saudiyya na sa ran Musulmi kusan miliyan 10 daga ƙasashen ketare za su gudanar da aikin Umrah a bana.

    A watan Afrilu, hukumomin Saudiyya sun kafa wani shinge da ke ƙewaye da Harami a Masallacin Annabi, inda aka maye gurbin wani shingen katako da ake da shi a baya.

    An samar da sabon shingen ne da nufin kare tsarin gine-ginen Masallacin.

  11. Mutumin da ake zargi da kisan kiyashi a Illinois ya mutu a Texas – Yan sanda

    Wani dan bindiga da ake zargi da kashe mutum takwas a birnin Joliet da ke Illinois a Amurka ya mutu bayan sa-in-sa da jami'an tsaro.

    Yan sanda a Joliet sun ce ana tunanin Romeo Nance mai shekara 23 ya harbe kansa bayan sa-in-sar kusa da Natalia a Texas.

    Ana zarginsa da kisan mutum takwas a wurare daban-daban a Joliet.

    Yan sanda sun gano gawarwakin bakwai cikin mutane takwas a wasu gidaje biyu ranar Litinin. Mutum na takwas kuma an gano shi ranar Lahadi.

    Gano gawarwakin ya janyo kaddamar da binciken gano wanda ake zargi da hukumomi suka yi gargadin barazana ne.

    Cikin sanarwa, yan sanda sun ce sun gano Mr Nance kusa da Natalia.

  12. An tsige shugaban majalisar dokokin jihar Ogun

    Rahotanni na cewa an tsige shugaban majalisar dokokin jihar Ogun, Kunle Oluomo.

    An tsige shi ne yayin zaman majalisar na yau Talata.

    Cikin mambobi 36, 18 sun goyi bayan a tsige Oluomo saboda dalilai na almundahana da ji-ji da kai da sauran laifuka.

    Bayan cire shi kuma, majalisar ta zabi Oludaisi Elemide a matsayin sabon shugabanta.

  13. Yadda sabon rikici a Filato ya janyo saka dokar hana fita a Mangu

  14. Jami'ar Bayero da ta Burtaniya sun ƙirƙiro sabuwar hanyar sarrafa garin dawa

    Cibiyar binciken noma a yankuna masu ƙamfan ruwan sama ta jami'ar Bayero a jihar Kano (BUK), a Najeriya da kuma Jami'ar Reading da ke Burtaniya, sun ƙirƙiro garin dawan da zai ɗauki dogon lokaci bai lalace ba.

    Haɗin guiwar ya kai ga ƙirƙiro hanyar ƙunshe garin dawan da waken soya da suka ce zai ɗauki lokaci mai tsawo ba tare da ya lalace ba.

    Cibiyar ta ce bayan shafe tsawon lokaci suna gudanar da bincike da hadin gwiwar cibiyar ICRISAT da kuma wani kamfani, a yanzu an samar da garin dawar wanda za a iya tuka tuwo da shi ba tare da ɗanɗanonsa ya sauya ba.

    Garin dawa na daga cikin garin hatsin da mutane da yawa ke amfani da su wajen yin tuwo, musamman a arewacin Najeriya.

    Masoya tuwo za su yi fatan ƙirƙiran garin ba zai tsaya kawai a kan dawa ba, musamman yadda farashin abinci ke ƙara hauhawa, lamarin da ke buƙatar alkinta wanda ake da shi.

  15. Nijar ta buƙaci tsaffin ma'aikan gwamnatin Bazoum su gabatar da shaidar kwangiloli

    A jamhuriyar Nijar, Hukumar COLDEF mai yaki da cin hanci da rashawa ta buƙaci jami'an tsohuwar gwamnati su gabatar da shaidun kwangiloli.

    Jami'an sun hada da na illahirin ma'aikatu da ministocin tsohuwar gwamnatin da su gabatar da takardun kwagilolin aikin da suka bayar a ma'aikatunsu.

    Matakin zai shafi tun daga fadar shugaban ƙasa zuwa ma'aikatu da kamfanonin gwamnati.

    Hukumar ta COLDEF ta ce ta ɗauki matakin ne a cigaba da neman bankaɗo irin ta'annatin da ake zargin an aikata a mulkin shekaru 12 Na ƴan Renaissance da aikatawa a ƙasar.

  16. Najeriya ta sanya sharuɗɗan bai wa ɗalibai tallafin karatu

    Gwamnatin Najeriya ta gindaya sharuɗɗan da ake buƙatar kowanne ɗalibi ya cika, kafin cin gajiyar shirinta na bayar da tallafin karatu.

    A cewar babban sakataren shirin Dr Akintunde Sawyer, duk ɗalibin da ke son samun tallafin zai nema ne ta hanyar cike fom a manhajar shirin ko ta shafinsa na internet.

    Bayanan da ake buƙata daga kowanne dalibi sun haɗa da lambar rijistar jarrabawarsa ta JAMB, da takardar haihuwa, da ta shaidar zama ɗan ƙasa, da lambarsa ta BVN.

    "’Haka kuma za mu buƙaci lambar shaidar samun guraben karatunsu, ta yadda za mu iya tabbatar da makarantar da suke son shiga, domin wani abu mai muhimanci game da wannan shiri shi ne idan aka tabbatar, za a dinga aika wa makarantun dukan kuɗin da ake buƙata ne kai tsaye’’ A cewar jami'in.

    Hukumomin ƙasar sun ce za a dinga amfani da harajin ilimi ƙarƙashin hukumar tara haraji ta kasar, a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin samar da kuɗaɗen gudanar da shirin.

    Gwamnatin ta ce an tsara shirin ta yadda babu wanda zai iya shigo da son rai a cikinsa, tana mai nuni da cewa kowane ɗan ƙasar na da damar neman tallafin.

    A Najeriya akwai ɗalibai da dama da ke barin karatun gaba da sakandare sakamakon ƙarin kuɗin makaranta, duk kuwa da kyakkyawan fatansu na samun ilimi mai zurfi don cika burinsu na rayuwa.

  17. An tsige shugaban majalisar dokokin jihar Ogun

    Rahotanni na cewa an tsige shugaban majalisar dokokin jihar Ogun, Kunle Oluomo.

    An tsige shi ne yayin zaman majalisar a ranar Talata.

    Ƴan majlisar 18 cikin 36 ne suka goyi bayan a tsige Oluomo saboda dalilai na almundahana da ji-ji da kai da sauran laifuka.

    Bayan cire shi kuma, majalisar ta zabi Oludaisi Elemide a matsayin sabon shugabanta.

    A watan Satumbar shekarar 2022, hukumar EFCC ta taɓa kama tsohon shugaban bisa zargin sama da faɗi da kuɗaɗen jama'a.

    Hukumar ta tsare shi na wasu kwanaki, kafin daga bisani aka sake shi, ko da yake ana ci gaba da bincike.

  18. 'Fiye da ƴan Najeriya 26,000 ke mutuwa saboda cututtukan da suka shafi sinadarin Tobacco

    Gwamnatin Najeriya ta ce mutane 26,800 ke mutuwa a duk shekara, a sanadiyyar cututtukan da suka shafi sinadarin Tobacco, yayin da ƴan ƙasar miliyan 4.5 daga shekara 15 zuwa sama ne ke tu'ammali da sinadarin.

    Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwar da hukumar kare masu amfani da kayayyaki ta ƙasar ta fitar a ranar Litinin.

    Muƙaddashin hukumar, Adamu Abdullahi, ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da wani shirin daƙile amfani da sinadarin na Tobacco wanda ke ƙunshe a taba sigari da wasu abubuwa.

    Shirin da aka sanya wa suna 'kada ka ƙona makomarka'.

    Adamu ya ce shirin na fatan magance ƙaruwar da ake samu na amfani da kayayyakin da ke ɗauke da sinadarin a tsakanin masu tasowa da kuma masu ƙarancin shekaru.

    Inda ya ƙara da cewa shirin na kuma neman magance matsalolin da hakan ke janyo wa ga al'umma baki ɗaya.

    Shugaban ya kuma jaddada muhimmancin samun ƙoshin lafiya, wanda ta haɗa da lafiyar gangar jiki da ta ƙwaƙwalwa da ta kuma walwala.

    Adamu ya kuma nuna muhimmancin haɗa ƙarfi waje guda domin samar da manyan gobe masu ƙoshin lafiya.

    Ya bayyana wasu daga cikin illolin tu'ammali da sinadarin tobacco ga matasa da suka haɗa da illa kan ƙwaƙalwa da hanyoyin numfashi da kuma yadda rayuwa ke ta'allaka da sinadarin nicotine.

  19. Rudani a Filato bayan yan majalisar jihar da kotu ta kora sun yi barazanar komawa aiki

    Yan sanda sun harba wa yan majalisar dokokin jihar Filato da kotu ta kora su 16 karkashin jam'iyyar PDP hayaki mai sa hawaye.

    Al'amarin ya faru lokacin da yan majalisar suka isa harabar majalisar tare da magoya bayansu a shirye-shiryen da suke na komawa zama.

    Yan sanda da sauran jami'an tsaro sun mamaye harabar majalisar Fadar gwamnati inda majalisar take tare da hana yan majalisar shiga sai dai yan majalisar sun ce ba za su bar wajen ba.

    Tsofaffin yan majalisar karkashin jam'iyyar PDP da kotun daukaka kara ta kora a watan Nuwamba sun yanke shawarar komawa zauren domin ci gaba da gudanar da harkokinsu.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito yan majalisar da aka kora karkashin jagorancin Ishaku Maren sun yi dafifi a harabar majalisar tare da magoya bayansu.

    Kotu ta kore su ne kan dalilan cewa PDP ba za ta iya gabatar da yan takara ba a zaben 2023 a Filato.

    Kotun daga baya ta ayyana mambobin jam'iyyar APC 16 da suka zo na biyu a zaben a matsayin wadanda suka lashe zabe.

    Duk da cewa tsofaffin yan majalisar sun soki lamarin, sun samu kwarin gwiwa bayan da kotun koli ta soke hukuncin kotu da ya kori gwamna Caleb Mutfwang.

    A hukuncinta na ranar 12 ga watan Janairu, kotun kolin ta ce karamar kotun ta yi kuskure wajen soke zaben gwamnan.

  20. Blinken zai gana da Tinubu yau a Abuja

    Gaba a yau ne Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken zai isa Najeriya a wani bangare na rangadin mako daya zuwa kasashen yammacin Afirka hudu.

    Amurka na fafutukar ganin dorewar tasirinta yayin da take samun gogayya daga Rasha da China.

    Kasashe a yammacin Afirka musamman a yankin Sahel sun fuskanci karuwar matsaloli ciki har da sauye-sauyen gwamnatoci a hudu cikin mambobin kungiyar ECOWA 15.

    Ziyarar ta zo ne daidai lokacin da Abuja, babban birnin Najeriya ke fuskantar matsalolin tsaro da sace-sacen jama'a.

    Najeriya ta fuskanci karuwar tashin hankali a arewaci da tsakiyar kasar inda yan bindiga ke kai hare-hare tare da satar mutane don kudin fansa.

    Kungiyoyi masu ikirarin Jihadi kamar Boko Haram da sauran kungiyoyi masu tafka miyagun laifuka sun kashe daruruwan farar hula tare da daidaita fiye da mutum miliyan biyu a shekarun baya-bayan nan, wani lamari da ke sa shakku game da kokarin da gwamnatin Najeriya take ikirari na kawo sauye-sauye da magance matsalolin tattalin arziki saboda janye tallafin man fetur.

    Shugaba Joe Biden na Amurka wanda ke fuskantar kalubale a kudurinsa na sake tsayawa takara, ya yi alkawarin kai ziyara Afirka bara sai dai hakan bai samu ba.

    Rangadin da Blinken ke yi na iya zama cikin yunkurin cika alkawarin sai dai yana zuwa ne a lokacin da ake samun sauye-sauyen lamuran siyasa tun ziyararsa ta karshe zuwa yankin a farkon shekarar 2023.