Rufewa
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe Litinin idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya
Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe Litinin idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Shugaban hukumar zaɓen Bangladesh ya ce mutanen da suka fita kaɗa ƙuri'a a babban zaɓen ƙasar ba su wuce kashi 40 ba cikin 100.
Kazi Habibul Awal ya ɗora alhakin hakan kan 'yan adawa bayan sun yi kiran ƙaurace wa zaɓen.
Ya kuma ce yunƙurin daƙile maguɗi da rikici bai yi nasara ba a wasu wuraren.
Firaminista mai-ci Sheikh Hasina ta matsu ta ga ta gudanar zaɓen da za a ce ingantacce ne, amma matsalar jam'iyyar 'yan adawa ta BNP ba ta shiga zaɓen ba".
Ta nemi mutane su kaɗa kuri'unsu, sannan ta kira jam'iyyar 'yan adawan a matsayin ta 'yan ta'adda.
Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin yin cikakken bincike a ma'aikatar jin-kai wadda Betta Edu ke jagoranta kan zargin badakalar kuɗaɗe.
Ministan yaɗa labaru da wayar da kai, Mohammed Idris shi ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Ce-ce-ku-ce ya ɓarke a ma'aikatar ne bayan zargin cewa ministar jin-ƙai Betta Edu ta bayar da umarnin tura kuɗi kimanin naira miliyan 585 zuwa asusun banki na wata mata.
Sanarwar da minista watsa labarun ya fitar, ta ce ta samu labarin abin da ke faruwa a ma'aiktar ta jin-ƙai a karkashin Betta Edu, inda ya ce gwamnati ta kuduri aniyar yin bincike don fito da gaskiya.
"Dangane da abubuwan da ke faruwa a ma'aikatar, shugaban ƙasa ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru," in ji sanarwar.
Idris ya ce gwamnati ta kuduri aniyar bankaɗo gaskiyar lamarin, tare ba da tabbacin cewa za a ɗauki matakin da ya dace don ganin an hukunta waɗanda aka samu da laifi.
Ministan yaɗa labaran ƙasar ya ce za a sanar da sakamakon binciken ga ƴan Najeriya.
Umarnin gudanar da bincike da shugaba Tinubu ya bayar, na na zuwa ne bayan fitar wata takardar biyan kuɗi da ministar ta aike wa ofishin babbar akanta janar da ƙasar, inda a ciki take buƙatar a tura zunzurutun kuɗi har naira miliyan 585, 189,500, don biyan tallafi, a wani ɓangare na tallafa wa masu tsananin buƙatar tallafi a wasu jihohin kasar huɗu.
To sai dai wani abu da ya ja hankali game da biyan kuɗaden shi ne sunan asusun bankin da aka biya kuɗin na wata mata ce mai suna Onlyelu Bridget Mojso.
Tuni dai ofishin babar akanta janar ta ƙasar ya ce ba ya biyan kuɗin gudanar da wani aiki na gwamnati a asusun wani mutum.
Shaidun gani da ido a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza sun ce an kashe mutane da dama sakamakon harin Isra'ila ta sama cikin dare.
Hotunan bidiyo da aka yaɗa sun nuna gawawwaki yashe a cikin ɓaraguzai na wani gida da aka ce na zaman mutane ne.
Wasu 'yan jarida a yankin sun ce kusan mutum 70 aka kashe.
Zuwa yanzu Isra'ila ba ta ce komai ba.
Ma'aikatar lafiya a Gaza ƙarƙashin ikon Hamas ta ce, mutum ɗari da sha uku aka kashe cikin sa'a 24 da suka wuce a zirin.
Yayin da yaƙin ya shiga wata na huɗu, Saktaren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken na ci gaba da zagaya yankin don kwantar da hankula.
Gwamnatin mulkin soja a Nijar ta nemi ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma, Ecowas, ta ɗage zaman tattaunawar da aka shirya yi ranar Laraba don ƙarƙare ranar mayar da mulki ga farar hula.
Firaministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine ya ce suna buƙatar ƙarin lokaci na tattaunawa da 'yan ƙasa, kuma yana son a mayar da ganawar zuwa 25 ga watan Janairu.
A makon da ya gabata aka fara taron ƙasa a birnin Agadez, wanda wakilai ɗari uku na 'yan siyasa, da sarakuna, da tsofaffin 'yan tawayen Azbinawa ke halarta.
Ecowas ta ƙaƙaba wa Nijar takunkumai masu tsauri tun bayan hamɓarar da Shugaba Mohamed Bazoum da sojoji suka yi a watan Yulin da ya wuce.
Tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Tavoro Nyame, ya bayyana cewa ya ɗauki darasin rayuwa a lokacin da yake zaman gidan yari a gidan gyaran hali na Kuje.
Nyame ya bayyana haka ne a yayin taron godiya da aka gudanar a sakatariyar ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN da ke Jalingo.
Tsohon gwamnan ya sha alwashin zama shugaba mai hazaka idan aka sake ba shi damar jagorantar jihar.
Ya bayyana cewa zaman gidan yari da ya yi, ya saka ya ɗauki darussa da dama, wanda hakan ya sa zai zama shugaba nagari ga al’umman jihar Taraba idan ya sake samun dama.
Nyame ya ce, “Na koyi abubuwa da yawa a gidan yarin Kuje da kuma a asibiti. Idan aka sake ba ni damar jagorantar al’ummar Jihar Taraba, zan yi abin da ya dace saboda gogewar da na samu.”
Ya jaddada muhimmancin yin imani da kuma juriya, inda ya shawarci shugabanni da su tsaya tsayin daka wajen fuskantar kalubalen da al'umma ke ciki.
Nyame, wanda ya shafe shekaru huɗu na hukuncin ɗaurin shekaru 14 da aka yi masa, ya ce tura shi zuwa gidan yarin na da alaƙa da siyasa.
Tsohon gwamnan ya buƙaci ‘yan Najeriya da su kasance masu taka-tsantsan wajen kashe kuɗaɗensu da kuma kira ga gwamnati da ta ba da fifiko ga manufofin inganta rayuwar ‘yan ƙasa.
Gwamnan yankin Kherson na kudancin Ukraine ya ce birnin ya fuskanci hare-haren Rasha na tsawon lokaci ba kakkautawa.
Alexander Prokudin ya ce an kai wa kasuwa da gidajen mutane hare-hare, tare da kashe mutum biyu da kuma jikkata wasu biyun.
Dakarun Rasha sun koma sansanoni a gabashin Dnipro tun bayan korar su daga birnin na Kherson wata goma sha huɗu da suka wuce, inda suke yawan kai wa birnin hari daga tsallaken kogi kusan a kullum.
Hukumar tsaro ta Civil Defence a Kano ta ce kama wani matashi mai suna Alkasim Ya'u bisa zargin kashe mahaifinsa.
Lamarin ya rafu ne a ranar Juma'a da dare a unguwar Tudun Yola da ke karamar hukumar Gwale.
Mai magana da yawun hukumar Ibrahim Abdullahi ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce mahaifin yaron mai suna Ya'u Mohammed wanda ɗan asalin jihar Katsina, ya kawo ɗan nasa ne Alkasim asibitin Dawanau don duba lafiyarsa saboda matsalar kwakwalwa da yake da shi.
Ya ce bayan zuwansu asibitin aka ce musu ba za su iya ganin likita ba sai washegari ranar Asabar, 6 ga watan Janairu.
"Maimakon su koma Katsina, sai mamacin ya yanke shawarar kwana a gidan ɗan uwansa da ke unguwar Tudun Yola.
"Alkasim ya faki idon mahaifinsa lokacin da yake cin abinci sai ya buga masa tangaram (plate) ɗin da yake cin abinci da shi. Babu kowa a gida lokacin saboda mutane sun tafi sallar Juma'a," in ji Abdullahi.
Ya ce daga bisani bayan dawowar mutane sai aka samu labarin abin da ya faru, inda aka garzaya da mahaifin asibiti inda kuma rai ya yi halinsa a jiya Asabar.
Jami'in hulɗa na rundunar ta Cibil Defence ya ce tuni aka miƙa matashin hannun ƴan sanda domin ci gaba da bincike.
Al'ummar Bangladesh na ci gaba da kaɗa ƙuri'unsa a babban zaɓen ƙasar da ake kyautata zaton shugabar ƙasar mai ci Sheikh Hasina za ta lashe.
Tuni dai aka tsaurara matakan tsaro, inda aka jibge jami’an soji da ‘yan sanda a sassa daban-daban na ƙasar.
Kafar yaɗa labaran Al-Jazeera ta ce an kashe wasu ma'aikatanta biyu a wani hari da aka kai wa ƙaramar motar da suke ciki a Gaza.
Hamza ɗa ne ga Wael Dahdoud, shugaban oshishin Al Jazeera da ke Gaza.
A makonnin farko na yaƙin Gaza ne aka kashe wa Mista Wael mata da 'ya'ya da kuma jikansa a hare-haren da Isra'ila ta kai wa wani sansanin 'yan gudun hijira da ke kudancin Zirin Gaza.
Gomman 'yan jarida ne suka mutu a Gaza sakamakon hare-haren Isra'ila, tun bayan fara yaƙin ranar 7 ga watan Oktoba.
Ƙungiyar Jami'o'in masu zaman Kansu ta Afirka (AAPU) ta yaba wa ƙoƙarin da ministan Ilimin Najeriya Tahir Mamman, ke yi na binciken takardun digirin boge a ƙasar.
Mataimaki Sakataren ƙungiyar na Yammacin Afirka, Salissou Mamaoudou, ne ya bayyana hakan a cikin wata takarda da ya fitar, a birnin Noukchoutt, na ƙasar Murtania.
Shi ma shugaban ƙungiyar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya tabbatar wa da BBC matsayin ƙungiyar tasu
Sakataren ƙungiyar ya ƙara da cewa matakin binciken da ministan ya ɗauka zai taimaka wajen samar da tsari nagartacce tare da ba da martaba da dawo da kimar karatun a idanun iyaye da ɗalibai.
Haka kuma ya ce a shirye ƙungiyar AAPU take don bai wa ministan haɗin kai wajen cigaba da gudanar da binciken a kan wasu Jami'o'in , da ba sa martaba wasu Jami'o'in da suke da kima a nahiyar Afirka.
Garin Kaltungo da ke jihar Gombe ya zama tamkar ramin gansheƙa duk inda mutum ya shiga zai iya karo da maciji.
Babu babba ba yaro, macizai na saran duk wanda ƙaddara ta faɗawa.
Yanzu haka noma na neman gagarar al'ummar garin saboda yadda macizan ke saran su.
Wani babban abu kuma shi ne irin tsadar da maganin kashe dafin yake da shi, inda ake sayan kwalba daya daga naira 50,000 zuwa 80,000.
Sai dai gwamnatin jihar ta ce tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta rage wa al'ummar garin raɗaɗin tsadar maganin.
Manoman sun ce macizan kan maƙale a ƙarƙashin amfanin gona kamar gyaɗa, ta yadda za zarar manomi ya je kusa da amfanin domin yin noma ko tugewa sai su sare shi.
Jami'an ceto a Japan sun zaƙulo wata dattijuwa mai shekara 90 daga ƙarƙashin ɓaraguzai, kwana biyar bayan wata girgizar ƙasar da ta auka wa tsakiyar kasar.
An same ta ne a cikin ɓaraguzan wani bene mai hawa biyu a birnin Suzu.
A ranar Litinin ne girgizar ƙasar mai ƙarfin maki 7.5 ta auka wa yankin da ke kusa da gaɓar tekun ƙasar, lamarin da ya haddasa mummunar ɓarna a yankin Noto.
Fiye da mutu 12 ne aka tabbatar da cewa sun mutu, yayin da fiye da 200 suka ɓace sanadiyyar iftila'in.
Jaridar Yomiuri Shimbun a ƙasar ta ce kimanin masu aikin ceto 100 ne ke aiki a birnin Suzu bayan da aka fahimci cewa akwai mata biyu da ake tunanin gine-gine sun danne su da rai a birnin
Jaridar ta ambato 'yan sanda na cewa an samu matar cikin koshin lafiya, sai dai ta gigice sakamakon tsananin sanyin da ake fuskanta a yankin.
Haka kuma masu aikin ceto sun sake gano wata matar mai shekara 40 a wurin, wadda ke fama da cutar bugun zuciya, kamar yadda rahotonni suka bayyana.
An zaƙulo matan biyu kwanaki bayan faruwar girgizar ƙasar.
Kwanaki ƙalilan bayan hukumar EFCC ta gayyaci tsohuwar ministar jin-ƙai ta Najeriya Sadiya Umar Farouk kan zargin ɓarnatar da wasu kuɗaɗe, sai ga shi sabuwar ministan jin-ƙan, Betta Edu na ƙoƙarin wanke kanta daga zargin sabuwar badaƙala a ma'aikatar.
Hakan na zuwa ne bayan fitar wata takardar biyan kuɗi da ministar ta aike wa ofishin babbar akanta janar da ƙasar, inda a ciki take buƙatar a tura zunzurutun kuɗi har naira miliyan 585, 189,500, don biyan tallafi, a wani ɓangare na tallafa wa masu tsananin buƙatar tallafi a wasu jihohin kasar huɗ.
To sai dai wani abu da ya ja hankali game da biyan kuɗaden shi ne sunan asusun bankin da aka biya kuɗin na wata mata ce mai suna Onlyelu Bridget Mojso.
Tuni dai ofishin babar akanta janar ta ƙasar ya ce ba ya biyan kuɗin gudanar da wani aiki na gwamnati a asusun wani mutum.
Wannan batu dai ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar musamman a shafukan sada zumunta inda mutane da dama ke kiran shugaban kasar Bola Tinubu ya sauke ministar daga mukaminta
Wani mai amfani da shafin X mai suna Waspapping_ya ce ''idan har aka kai safiyar gobe Betta Edu na kan matsayinta, to za mu son cewa Bola Ahmed Tinubu bai shirya wa jagorantar ƙasar nan ba. Babu yadda za a yi ka dakatar da Halima Shehu sannan ka bar Betta Edu, wadda ake da manyan zarge-zarge a kanta ba, ka dakatar da ita yanzu, sannan ka bar EFCC su gayyaceta domin tuhumarta.
Shi ma wani mai amfani da shafin X mai suna TahaAdamy cewa ya yi ''Kamar Halima, ya kamata a dakatar da Betta Edu, a binciketa, sannan a gurfanar da ita idan an same ta da laifi. Ya kamata shugaban ƙasa ya rushe ma'aikatar jin-ƙai, saboda tana neman zama wata matattarar cin hanci ga mutanen da suka jagorance ta a baya da kuma yanzu, a ƙarfafa hukumar NEMA don aiwatar da ayyukan hukumar.
A nata ɓangare ministar jin-ƙai Betta Edu ya musanta zargin, tana mai bayyana shi a matsayin maras tushe balle makama.
Ministar ta kuma ce wannan batun tuggun masu kawo ruɗani ne da ke ƙoƙarin ganin sun dankwafar da ƙoƙarin da ma'aikatarta ke yi wajen kawar da cin hanci da rashawa.
A farkon wannan makon ne hukumar EFCC ta gayyaci dakatacciyar shugabar hukumar bayar da tallafin dogaro da kai ta Najeriya, NSIPA, Hajiya Halima Shehu kan zargin badaƙalar kuɗaɗe.
Rahotonni na cewa Hajiya Halima ta tra wasu kudi kimanin naira biliyan 40 daga asusun hukumar NSIPA zuwa wasu asusu mallakin wata mata da kuma wani kamfani na daban.
Rukunin kamfanin Dangote a Najeriya ya ce bai aikata wani laifi, ko ba daidai ba da ya sa jami'an hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa suka ziyarci babban ofishinsa ba.
Cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar kan ziyarar da jami'an hukumar suka kai babban ofishinsa da ke Legas ranar 4 ga watan Janairu, ya ce ya fahimci girman damuwa da maganganu da hakan ya janyo tsakanin abokan hulɗarsa, da sauran mutane, don haka ne ma kamfanin ya ce ya fitar da sanarwar don fayyace ainihin abin da ya faru.
Sanarwar ta ce a ranar 6 ga watan Disamban 2023, ya samu wasiƙa daga hukumar EFCC, inda aka buƙaci kamfanin ya bayar da bayanan canjin kuɗin ƙasar waje da CBN ya bai wa kamfanin tun daga shekarar 2014 zuwa yau.
Kamfanin ya ce ya kuma rubuta wa hukumar EFCC takardar da ke nuna cewa kamfanin ya karɓi takardar buƙatar bayar da bayanan da aka buƙata.
''Mun kuma buƙaci ƙarin lokaci domin kammala tattara bayanan, don gabatar da su kamar yadda aka buƙata kasancewa bayanan shekara 10 aka buƙata'', in ji sanarwar.
To amma kamfanin ya ce hukumar EFCC ba ta ba shi amsa kan buƙatar ƙarin lokacin da ya nema ba, sannan bai ƙara musu lokacin ba, a maimakon haka sai ya dage cewa sai kamfanin ya gabatar da takardun bayanan da aka buƙace shi a lokacin da aka buƙata.
Sanarwar ta ƙara da cewa duk da ƙurewar lokacin da ya fuskanta, ya tabbatar wa da hukumar EFCCn aniyarsa na gabatar da takardun amma ya alƙawarta gabatar da takardun rukuni-rukuni.
Kamfanin ya ce a ranar 4 ga watan Janairun 2024, wakilansa suka gabatar da rukunin farko na takardun ga hukumar EFCC, amma sai jami'an na EFCC suka ki karɓar takardun, suka dage cewa sai sun ziyarci babban ofishinsa domin karɓar takardun da hannunsu.
''A yayin da wakilan kamfaninmu ke ofishin EFCC don gabatar da takardun, sai ga jami'an hukumar a ofishinmu da nufin karɓar takardun da an riga an kai musu ofishinsu, sun zo a wani yanayi da ba mu ji daɗinsa ba, domin hakan tamkar wulaƙanta mu ne'' kamar yadda sanarwar ta yi bayani.
Sanarwar ta ci gaba da cewa ''Abin takaicin ma shi ne jami'an ba su karɓi takardun a babban ofishin namu ba lokacin ziyarar tasu, kasancewar tuni takardun na ofishinsu''.
Kamfanin ya ce a matsayinsa na wanda ke bin doka da oda, a kodayaushe a shirye yake ya baiwa hukumar ta EFCC haɗin kai bisa duka bayanan da take nema.
''Tuni mun bai wa hukumar rukunin farko na takardun da take buƙata, kuma muna aiki wajen tattara rukuni na biyu domin bai wa hukumar a kan lokaci domin gudanar da aikinta''.
Kamfanin na Dangote ya ce - a matsayinsa na ɗaya daga cikin masu taimaka wa tattalin arzikin Najeriya, kuma babban kamfanin da ya fi ɗaukar 'yan Najeriya aiki, wanda kuma ya kasance ɗaya daga cikin mayan masu biyan haraji a ƙasar - a kodayaushe shi mai bin doka da oda ne, kuma a shirye yake wajen yin duk wani abu da zai taimaka wajen mayar da ƙasar mai kyakkyawan yanayin zuba jari ga 'yan ƙasar da na ƙetare.
A Najeriya darajar kuɗin na ci gaba da faɗuwa, lamarin da ke ƙara haifar da hauhawar farshin kayaki tare da wahalhalun matsin tatalin arziki.
Wasu masana dai na ɗora alhakin hakan kan yadda ake bayar da chanjin kuɗin ƙasar waje ba bisa ƙa'ida ba, lamarin da ke haifar da mabambantan farashin kuɗin ƙasar wajen.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta 'wargaza' ginin cibiyar Hamas da ke arewacin Zirin Gaza
Mai magana da yawun Rundunar Daniel Hagari ya shaida wa manema labarai cewa a yanzu ƙungiyar Hamas na gudanar da ayyukanta ne a yankin lokaci-zuwa lokaci ba tare da ''umarnin kwamandojinta ba''.
Ya ce Isra'ila ta kashe aƙalla dakarun ƙungiyar 8,000 a arewacin Gaza.
To sai dai BBC ba za ta iya tabbatar da wannan adadi ba.
Mista Hagari ya kuma ce a yanzu rundunar sojin Isra'ila za ta mayar da hankali wajen karya logon Hamas a kudanci da tsakiyar Gaza.
Isra'ila ta kashe fiye da mutum 22,000 tun farkon fara yakin, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Gaza ta bayyana, wadda ta ce a ranar Asabar kawai an kashe Falasdinawa 120.
An lalata yanki Gaza da munanan hare-haren Isra'ila, tare da raba al'ummar yankin miliyan 2.3 da muhallansu.
Isra'ila ta fara kai hare-hare kan Zirin Gaza ne bayan da ƙungiyar Hamas ta ƙaddamar da hare-hare a kudancin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, inda ta kashe mutum 1,200 mafi yawancinsu fararen hula, tare da yin garkuwa da kusan mutum 240.
Daga baya an yi musayar wasu daga cikinsu da wasu fursunonin Falasɗinawa da Isra'ila ke tsare da su, to sai dai har yanzu akwai fiye da mutum 120 da ke hannun ƙungiyar ta Hamas.
Ana ci gaba da kaɗa ƙuri'a a babban zaɓen ƙasar Bangladesh wanda ake kyautata zaton shugabar ƙasar mai ci Sheikh Hasina za ta lashe.
An tsaurara matakan tsaro, inda aka jibge jami’an soji da ‘yan sanda a sassa daban-daban na kasar, sakamakon yawaitar ayyukan zagon ƙasa da aka gudanar a yayin da ake shirye-shiryen zaɓen.
Wakilin BBC ya ce an banka wa runfunan zaɓe wuta, ba a kuma san waɗanda suka aikata wannan ɓarnar ba, sannan an kai wa wasu ‘yan takara hari.
Jam'iyyar Awami mai mulki ta zargi 'yan adawa da ƙaddamar da "ayyukan ta'addanci." Amma Babbar jam'iyyar adawa ta BNP - wadda ke jagorantar kaurace wa zaɓen - ta musanta hannu a tashin hankalin.
Firaministar Bangladesh Sheikh Hasina jim kaɗan bayan ta kaɗa ƙuri'arta a rumfar zaɓenta da ke wata unguwa a birnin Dhaka.
Zaɓen ka iya share mata hanya wajen sake ɗarewa kan kujerarta a karo na biyar bayan da babbar jam'iyyar adawa ta ƙaurace wa zaɓen.
Rahotanni sun ce Aljeriya ta sake mayar da jakadanta na ƙasar Mali, makonni biyu bayan ta dawo da shi gida sakamakon takun-sakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.
Gwamnatin sojin Mali ta zarge shi da yin katsalandan a harkokin cikin gidanta, ta hanyar ganawa da 'yan awaren Abzinawa.
A cikin watan Agusta ne wani faɗa ya sake ɓarkewa tsakanin Abzinawa da sojoji a birnin Bamako, bayan shafe shekara takwas ana zaman lafiya.
Shi ma Jakadan Mali a Algeria ya koma bakin aiki bayan ta dawo da shi gida cikin 'yan kwanakin nan.