Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Mukhtar Adamu Bawa and Usman Minjibir

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafi, anan muka kawo karshen labarai da rahotanni daga Najeriya da kasashen ketare, na yau Alhamis.

    Sai kuma gobe Juma'a idan Allah ya kai mu.

    Adadin sauran abokan aiki, Badriyya Tijjani Kalarawi da Abdullahi Bello Diginza ke sallama da ku daga nan sashen Hausa na BBC.

    Mu kwana lafiya.

  2. Najeriya da wasu kasashen Yammacin Afirka za su fuskanci hauhawar farashin abinci a 2024

    Ana fargabar Najeriya da wasu kasashen yammacin Afirka za su fuskanci karin hauhawar farashin kayan abinci kamar masara da gero da shinkafa da dawa da alkama da sauransu a shekarar 2024 da muka shiga.

    Hukumar Samar da Abinci da Ayyukan Gona ta Duniya ce ta fitar da wannan rahoto da hadin gwiwar Hukumar Samar da Abinci ta Duniya, FAO, inda a ciki ta bayyana cewa tashin farashin kayan abincin na da nasaba da abubuwa da dama da suka hada da rikice-rikicen da yankin Sahel ke fama da shi, da karyewar darajar kudaden kasashen da sauran su.

    A cewar rahoton farashin kayan abinci dangin tsaba, zai karu fiye da yadda aka saba gani cikin shekaru biyar da suka gabata, kan dalilai da dama da suka hada da raguwar ayyukan noma da tarnakin da ake samu a bangaren ciniki da sauran manyan kalubalen da duniya ke fuskanta tun ma ba matsalar tsaro da da karyear darajar kudaden kasashen da ke gabar tekun Guinea suke fuskanta.

    Rahoton ya ce ldan akai duba da Najeriya, cire tallafin man fetur ya taka rawa wajen hauhawar farashin abinci da sauran kayan masarufi.

    Wani jami'i a hukumar abincin ta duniya reshen Najeriya, Dakta Abubakar Sulaiman na Hukumar ya ce wajibi ne a fito da muhimman matakai da za su iya zama kandagarki wajen saukaka lamarin.

    Rahoton hukumar ya kuma nuna cewa an samu raguwar kashi 44 cikin 100, na yawan masara da gero da dawa da ake nomawa sakamakon matsalar sauyin yanayi, da tsaro, sai dai ya bayyana an samu ci gaba a bangaren noman rogo da doya da kayan lambu da sauransu.

  3. Halin da ake ciki a arewacin Gaza cikin hotuna

    Yayin da Isra'ila da Hamas da wani bangaren kungiyar Hezbollah ta Lebanon ke ci gaba da gwabza yaki, adadin wadanda ake kashewa na karuwa cikin sauri.

    Inda wadanda suka yi gudun hijira ke kara shiga halin tagayyara da rashin madafa, sakamakon yadda Isra'ila ke ci gaba da kai hare-haren kan matsugansu.

    Daga umartar su koma arewacin Gaza a matsayin mai aminci ko tudun mun tsira, sai sake umartar su bar nan su nausa kudanci inda nan din ma aka sake umartar su bar shi.

    Ga kadan daga hotunan halin da ake ciki a Khan Younis;

  4. Masu kidan gangi 12 sun mika wuya ga 'yansanda a Kano

    Rundunar 'yansandan jihar Kano ta ce wasu masu kidan gangi a jihar su 12 sun mika wuya bisa radin kansu ga rundunar.

    Cikin wata sanarwa da rundunar 'yan sandan jihar ta fitar ta ce makada gangin daga unguwannin Rijiyar Lemo da Kurna, rundunar ta ce a lokuta da dama su ne ke ingiza wutar dabanci a Kano.

    Sanarwar ta ce matakin wani ci gaba ne a kokarin da rundunar ke yi na kawar da dabanci da miyagun laifuka a Kano.

    Rundunar 'yan sandan ta ce mutanen sun nuna takaicinsu kan sana'ar tasu tare da alkawarta daina kidan gangin wanda ke taimakawa wajen ingiza harkokin daba a fadin jihar.

    Haka kuma sun alkawarta bai wa jami'an tsaro hadin kai a kokarin da suke na kakkabe dabanci a fadin jihar.

    Rundunar ta kuma yi kira ga al'umma da su ci gaba da bai wa rundunar hadin kai wajen ciyar da jihar gaba ta fannin tsaro.

  5. Najeriya ta tabbatar da mutuwar ɗalibin ƙasar da 'yan sanda suka harba a Kanada

    Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin bin kadin kisan da aka yi wa wani dalibi dan Najeriya mai shekara 19 da ke karatu a kasar Canada. Rahotanni sun bayyana ana zargin 'yan sandan Canada ne sukai ajalin matashin.

    Shugaban hukumar kula da 'yan Najeriya mazauna kasashen waje (Nidcom) Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana zargin kisan dalibin a Manitoba a Canada da rashin imani.

    A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar 4 ga watan Junairu 2024, dauke da sa hannun maimagan da yawun ofishin Abike ta ce za su tabbatar an yi wa mamacin adalci.

    Sanarwar ta kara da kira ga hukumomin kasar Canada da tuni suka ce sun fara gudanar da bincike kan lamari su ta bbatar an yi shi cikin adalci.

    Sun mika sakon ta'aziyya ga iyaye da 'yan uwa da aboakan dalibi Folabi, tare da fatan Allah ya sa bakin wuyarsa kenan.

    Yadda Folade ya gamu da ajalinsa

    Kamar yadda Nidcom ta fitar da sanarwa, bayanan da suka samu sun nuna dan sanda ne ya harbi matashin dan Najeriya mai shekaru 19 a ranar 31 ga watan Disamba 2023, gabannin shiga sabuwar shekarar 2024 a yankin Manitoba da ke Canada.

    Duk da cewa babu cikakkun bayanai kan mutuwarsa, amma hukumar 'yan sandan Monitoba sun wallafa takaitaccen bayani a shafinsu na intanet na cewa " sun ce an kira 'yan sandan ta wayar tarho, akan wani matashi da ya ke abu kamar maras hankali.”

    'Yan sandan sun ce su na isa wurin, duk kokarin da suka yi domin shawo kan matashin ya ci tura, dalilin da ya sa 'yan sandan sukai harbi kenan bisa tsautsayi ya yi ajalinsa.''

  6. Will Smith ya ba da kyauta ga ɗan ƙasar Guinea da ya je Jami'ar Al-azhar a keke

    Babban jarumain fina-finan Amurka Will Smith ya kira matashin nan dan kasar Guinea da ya je jami'ar Al-azar bayan ratsa kashen Afirka a kan keke.

    A shekarar da ta gabata ne Mamadou Safayou Barry ya shiga kanun labarai bayan shafe kilomita kimanin 4,000 a kan keke.

    Cikin kiran bidiyon da Smith ya yi wa matashin a birnin Alqahira, inda yake karatu, Smith ya fada masa cewa ya yaba da kokarin da ya yi sannan ya ba shi kyautar sabon keke da laptop.

    "Ina son duniya ta ji labarinka," in ji jarumin.

    Cikin wani takaitaccen bidiyo da aka dora a shafin YouTube na Smith, an nuna yadda dalibin yake magana da mutanen da ke zagaye da shi cikin zakuwa yana cewa ''Wannan shi ne Will Smith'' in ji Barry, 'Ina son fina-finanka.

    "Ban san yadda zan gode maka ba wallahi ," in ji matashin bayan da ya ji kyautar.

    A watan satumba ne tawagar yaran jarumin ta tuntubi BBC bayan wallafa labarin tafiyar matashin suna masu cewa labarin ya sosa zuciyar jarumin, don haka suna son yin magana da shi.

    A watan Mayun shekarar da ta gabata ne Mamadou Safayou Barry mai shekara 25 ya fara tafiyar daga asar Guinea da ke Yammacin Afirka zuwa fitacciyar jami'ar Al-Azhar tare da fatan cewa jami'ar za ta yi maraba da shi.

    Mista Barry wanda ke da aure da daya ba zai iya biyan kudin jirgi ba, don haka ne ya dauki kekensa inda ya yi tafiyar wata hudu inda ya ratsa kasashen Maliu da Burkina Faso ta Togo da Benin da Nijar da kuma Chadi.

    Ya yi doguwar tafiyar ne ta hanyar ratsa yankunan da ke fama da yake-yaken masu ikirarin jihadi, da kasashen da suka fusknacoi juyin mulkin soji.

    Ya sha kamu tare da tsarewa har sau uku ba tare da wata kwakkwarar hujja ba, sau biyu a Burkina Faso da kuma sau daya a Togo.

    Tafiyar Mista Barry ta samu armashi ne a lokacin da ya isa Chadi, inda wani dan jarida ya yi hira da shi sannan ya dora labarinsa a intanet, lamrin da ya sa wata kungiya ta biya masa kudin jirgi domin isa Masar.

    Bayan isarsa ne kuma jami'ar Al-Azhar ta ba shi gurbin karatu, da fari a fannin ilimin addinin musulunci, sannan daga baya aka ba shi gurbi a fannin fasaha a kyauta.

  7. Sojojin Najeriya sun ce sun kashe 'yan fashin daji 10

    Rundunar sojin Najeriya ta Hadarin Daji ta kai wa 'yan ta'adda farmaki tare da kubutar da mutum tara da aka yi garkuwa da su, sun kuma gano makamai da albarusai, da babur da na'urorin sadarwa.

    A ranar 3 ga watan Junairu 2024, runduna ta takwas ta sojin Najeriya ce ta yi wannan aikin karkashin jagorancin Manjo Janar Godwin Mutkut, a karamar hukumar Batsari da Safana da ke jihar Katsina a arewacin Najeriya inda aka kashe 'yan ta'adda 10 yayin da wasu da dama suka tsere da munanan raunuka.

    Sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce ta samu bindiga kirar AK-47, da alburusai da bindigogi kirar gida guda uku da harba-ruga bakwai da sauran da sauran bindigogi masu hatsari da na'urorin sadarwa da wayoyin hannu da kakin soji tare da babura hudu.

    Haka kuma sanarwar ta ce a wannan ranar ce dai kuma dakarun soji na rundunar HADARIN DAJI da ke aiki a jihar Zamfara suka kai samame kauyukan Dansadau da Dandalla a karamar hukumar Maru, inda suka kubutar da mutum tara da ake garkuwa da su da suka hadar da mata biyar da jarirai hudu.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa 'yan bindigar sun gudu ne suka bar mutanen bayan musayar da jami'an tsaro.

    Tuni aka sada mutanen da iyalansu a garin Magami kamar yadda sanarwar ta bayyana.

  8. Ma'aikatar lafiyar Gaza ta ce mutanen da suka mutu a Gaza sun kai 22,438

    Ma'aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta wallafa alkaluman mutanen da suka mutu a yankin Falasdinawa tun bayan fara yakin Isrta'ila da Hamas.

    Cikin wani sako da ta wallafa a shafinta Telegram, ma'aikatar ta ce mutum 22,438 ne aka kashe zuwa yanzu tun bayan da Hamas ta kai hare-hare cikin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.

    Haka kuma ma'aikatar lafiyar ta ce mutum 125 ne aka kashe tare da raunata 318 cikin sa'a 24 da suka wuce.

    Ya zuwa yanzu adadin wadanda suka jikkata ya kai 57,614, kuma kashi 70 na wadanda suka jikkatan mata ne da kananan yara.

    BBC ba ta iya tantance wadannan alkaluma ba, amma kungiyoyin duniya sun ce ba su da hujjar da za su karyata wadannan alkaluma da ma'aikatar lafiyar Gaza ta fitar.

  9. Ga hotunan jana'izar Saleh Al-rouri, jagoran Hamas da aka kashe a harin jirgi maras matuƙi

    An gudanar da jana'izar mataimakin shugaban kungiyar Hamas Saleh al-Arouri a birnin Beirut na kasar Lebanon. Masu makoki sun taru domin alhinin mutuwarsa, su na kuma dauke da tutar Hamas.

    Ga kadan daga cikin hotunan jana'izar sa:

  10. Ana jana'izar mataimakin shugaban Hamas da aka kashe

    Ana gudanar da janaizar mataimakin shugaban kungiyar Hamas, Saleh Al-Arouri a Beirut, babban birnin kasar Lebanon.

    Daruruwan al'umma ne suke rububin daukar makarar Saleh al-Arouri, ya zuwa masallacin Imam Ali da ke gundumar Tariq Al-jadida da ke birnin Beirut na Lebanon.

    Kisan gillar da aka yi masa shekaran jiya Talata ya tayar da fargabar cewa yakin da ake yi tsakanin Israila da Hamas zai iya rikidewa zuwa yakin da zai game gabas ta tsakiya gaba daya.

    A jiya Laraba, Hassan Nasrullah, jagoran kungiyar Hizbullah da ke Lebanon ya gargadi Israila cewa za su mayar zazzafan martani kan kisan.

    Isra'ila dai ba ta tabbatar ko musanta zargin cewa ita ce ta kai harin ba.

    Sai dai kuma wakili na musamman na Amurka zuwa gabas ta tsakiya ya tafi Isra'ila a ranar Alhamis domin yayyafa wa wutar rikicin da ke son tashi tsakanin Hizbullah da Isra'ila ruwa.

  11. Firaminista Rishi Sunak ya ce Birtaniya za ta gudanar da babban zaɓe

    Faraministan Birtaniya Rishi Sunak ya ce yana tunanin za a yi babban zaɓe a ƙasar cikin wata shida na ƙarshen wannan shekara ta 2024.

    Kalamansa na zuwa ne bayan an fara rade-radin cewa yana shirin kiran a yi zaben a cikin 'yan watanni masu zuwa.

    Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna jam'iyyarsa ta Conservative na bayan ta Labour mai adawa, nesa ba kusa ba.

    Shugaban jam'iyyar ta Labour, Keir Starmer na ci gaba da tallata manufar jam'iyyarsa wadda ya kira ta "Kyakkyawan fata" a maimakon abin da ya kira siyasar a fasa kowa ya rasa.

  12. NNPCL ta tabbatar mana ba za a ƙara kuɗin man fetur ba a Najeriya- IPMAN

    Kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Najeriya, IPMAN ta ce babu kanshin gaskiya dangane da rahotanni da ke yawo cewa za a kara kudin man fetur.

    Shugaban kungiyar na arewacin najeriya, Alhaji Bashir Dan Malam, a wata hira da BBC ya ce sun samu tabbaci daga kamfanin mai na kasar mai zaman kansa wato NNPCL.

    Dama dai kamfanin NNPCL ya musanta rahotannin cewa ana shirin kara farashin litar man fetur a kasar.

    A cewar NNPCL mutane su kwantar da hankalinsu, Najeriya ba za ta kara kudin mai ba a wannan lokacin.

    Tuni dai aka fara ganin dogayen layin ababan hawa a gidajen mai musamman a biranen Abuja da Legas da karin wasu a sassan Najeriya.

    Ana sayar da litar mai a Najeriya tsakanin naira 650 zuwa 660.

    Sai dai a watan Disambar 2023 ne bankin duniya ya shawarci Najeriya da ta kara kudin man zuwa naira 750, idan dai har kasar na son daina biyan tallafin man kocakan.

  13. 'Yan bindiga sun kashe mutum 10 a Zamfara

    Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa wani gungun ‘yan bindiga ya afkawa kauyen Kwanar Dutse da ke masarautar Dansadau da ke karamar hukumar Mulki ta Maru, a daren Laraba.

    Mazauna garin dai sun ce 'yan bindigar karkashin jagorancin gawurtaccen dan bindigar nan a yankin, Damuna sun afka musu ne saboda sun gaza biyan harajin naira miliyan ashirin da dan bindigar ya dora musu.

    Jihar Zamfara na fama da hare-haren 'yan bindiga da sace tare da garkuwa da al'umma domin kudin fansa, inda da wuya rana ta fito ta fadi ba a ji irin wadannan munanan labarin ba.

    Wata uwa da aka kashe wa da ta ce "muna zaune muna gudanar da al'amuranmu kawai sai muka ji harbi. Sai muka kwasa da gudu, a inda 'yan bindigar suka yi ta harbin kan mai uwa dawabi. Ina fatan za a sako min 'ya'yana".

    Shi ma wani wanda mazaunin garin ne ya shaida wa BBC cewa " yanzu haka akwai mata fiye da 50 da ke hannunsu a cikin daji".

    To sai dai gwamnatin jihar a ta bakin mai magana da yawun gwamnati, Sulaiman Bala Idris, ta ce ana samun sauyi sabanin yadda jihar ta Zamfara take a baya, "ina mamakin yadda jama'a ba sa fadar irin nasarorin da gwamnatin nan ke samu. Ko a shekaran jiya sai da aka kashe gagga-gaggan 'yan bindiga".

    A watan Nuwamban badi dai wasu maharan sun yi garkuwa da kimanin mutum dari da suka hada da mata da yara daga garuruwan a matsayin mayar da martini sanadiyyar wani hari ta sama da sojoji suka kai a maboyarsu.

  14. Fursunonin da aka saki don zuwa bikin Kirsimeti a gida sun ƙi komawa

    Ƴan sanda a Brazil na neman fursunoni fiye da 250 da suka ƙi komawa gidan yari bayan da aka basu dama su je bikin kirsimeti da iyalinsu.

    An saki fursunonin a jajiberin kirsimeti kuma ana sa ran su koma ranar 30 ga watan Disamban da ya gabata.

    Yayin da akasarin fursunonin 1,785 da aka bai wa wannan dama suka koma gidan yarin, sama da 250 sun gudu.

    A yanzu ana yi wa fursunonin da suka gaza komawa kallon waɗanda suka tsere.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce cikin fursunonin da suka gudu akwai wasu riƙaƙƙun masu laifi.

    A ƙarƙashin dokar Brazil, ana barin wasu fursunoni su je gida a ranakun da ake hutu.

    Dole ne fursuna ya kasance yana nuna dabi'u masu kyau tare da cika wasu ƙa'idoji haɗi da samun amincewar alƙali kafin ya cancanta a bashi damar zuwa hutu.

    Daga cikin ƙa'idojin akwai inda ake barin fursunoni su yi aiki a wajen harabar gidan yarin da rana inda da yammaci suke komawa kurkuku.

    Domin neman wannan dama, dole ne wanda ya yi lafi a karon farko ya kasance ya yi zaman gidan yari kashi ɗaya bisa shida na hukuncin da aka yanke masa yayin da waɗanda suka saba aikata laifi sai sun yi zaman gidan yari na kashi ɗaya bisa huɗu na hukuncinsu.

    Dokar ta yanzu wadda ta ba da irin wannan dama ta zuwa hutun kirsimeti da Easter da na ranar uwa da sauran ranakun hutu, tana cike da taƙaddama saboda ba a cika ganin fursunoni suna tserewa ba.

    A 2022, kashi 43 cikin 100 na fursunonin da aka bai wa damar zuwa hutu ba su koma gidan yari ba, a cewar hukumar kula da gidan yari.

    Majalisar dokokin Brazil na fuskantar matsin lamba kan amincewa da sabon ƙuduri da zai soke bai wa fursunoni damar zuwa hutu.

  15. Amurka ta ce karar da Afirka ta Kudu ta shigar a ICC kan Isra'ila ƙage ne

    Amurka ta yi watsi da karar da Afirka ta Kudu ta shigar a kotun Manyan Laifuka ta Duniya, ICC, kan yakin da Isra'ila ke yi a Gaza.

    Afirka ta Kudu ta fadi cewa Isra'ila na aikata 'kisan kiyashi' a Gaza, a wata kara da ta shigar a kotun ta ICC, a makon da ya gabata.

    "Ba mu ga wani abu da ke nuni da 'kisan kiyashi' ba," in ji mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Mathew Miller on Wednesday.

    Sai dai ya kara da cewa "amma akwai yakin da sojoji suke yi a can da ya jefa Palasdinawa cikin hadari."

    Shi ma mai magana da yawun majalisar tsaro ta fadar White House, John Kirby, a ranar Laraba, ya fadi cewa Amurka na yi wa karar kallon "wadda babu kanshin gaskiya kuma wadda bai ba kamata a kai ta ba."

    Isra'ilar ma ta yi watsi da karar ta Afirka ta Kudu kan zarge-zargen kisan kiyashi, inda ta ayyana ta a matsayin "maras tushe" sannan kuma "kage" ne.

    Afirka ta Kudu dai na goyawa Palasdinawa baya a yakin da Isra'ilar ke yi a Gaza, inda ita kuma Amurka take goyon bayan Isra'ila ta hanyar taimaka mata da karfin soji.

  16. Hare-haren Isra'ila na ci gaba da kashe Falasdinawa

    Jami'ai a Gaza sun ce luguden bama-bamai da Isra'ila ta yi da daddare ya kashe gwamman Palasdinawa.

    Wani jami'in ma'aikatar lafiyar Gazar ya ce mutane 14 ne suka mutu da suka hada da kananan yara wadanda aka kashe yayin wani luguden wuta da sojojin Isra'ilar suka kai garin Al-Mawasi da ke yammacin birnin Khan Younis, a kudancin Gaza.

    Da farko dai Isra'ilar ta ayyana garin a amtsayin wuri mai aminci ga dubban Palasdinawa 'yan gudun hijra.

    Nahed Abu Taime, wani likita a asibitin Nasser, inda ake kai matattu da wadanda suka raunata shi ne ya bayar da alkaluman wadanda suka mutu.

    " Sashen kulawar gaggawa na asibitn ya samu shahidai masu yawa da wadanda suka jikkata sakamakon hare-haren Isra'ila a safiyar yau. an kawo shahidai guda 16 nan asibitin wadanda wasun su mazauna al-Mawasi ne sakamakon hare-haren Isra'ila a wuraren zaman al'umma".

    Ya kara da cewa " mutum 53 sun samu rauni kuma an kawo su nan tun cikin dare kuma tun lokacin muke karbar fararen hula da suka jikkata".

  17. Shugaban Kenya na shan suka kan barazanar ƙin mutunta umarnin kotu

    Shugaban Kenya William Ruto na fuskantar caccaka sakamakon barazanar da ya yi na ƙin mutunta umarnin alƙalai da ya kira "masu cin hanci".

    A ranar Talata ne Mr Ruto ya ce wasu alƙalai da bai bayyana sunansu ba sun haɗa kai da ƴan hamayya domin kawo cikas a manufofin gwamnatinsa.

    Sai dai a martaninta, Cif joji, Martha Koome ta ce ƙin mutunta umarnin kotu ya keta yardar da al'umma ke da ita kan jami'ai da ma'aikatan gwamnati.

    "Idan jami'ai ko ma'aikatan gwamnati suka yi barazanar take umarnin kotu, an yi wa doka karen tsaye, abin da zai ba da dama ga mulkin kama karya a ƙasa," in ji Ms Koome cikin wata sanarwa.

    Ta kuma umarci alƙalai su ci gaba da aiwatar da ayyukansu ba tare da tsoro ba.

    Jagoran ƴan hamayya, Raila Odinga ya ce barazanar da Mr Ruto ya yi wa ɓangaren shari'a 'rashin daraja' doka ne.

    Mr Odinga ya ce shugaban ya ƙetare iyaka game da zargin da ya yi kan alƙalai.

    Hukumar kula da harkokin shari'a a Kenya wadda ke ƙarƙashin shugabancin Ms Koome, ta bayyana damuwa game da kalaman shugaban ƙasar.

    Ita ma ƙungiyar Lauyoyi ta ƙasar ta yi kira a shiga yajin aikin gama-gari a mako mai zuwa domin mara wa ɓangaren shari'a baya.

    Sai dai Mr Ruto cikin wata sanarwa da kakakin gwamnati ya fitar, Hussein Mohammed, a ranar Laraba, ya yi alƙawarin yaƙar abin da ya kira "cin mutuncin ɓangaren shari'a".

    Shugaban wanda ya hau kan mulki a Satumban 2022, ya fuskanci suka saboda bijiro da sabbin haraje-haraje daidai lokacin da mutane ke fama da tsadar rayuwa.

    An dai ƙalubalanci matakin nasa a kotu, duk da dai ba a kai ga yanke hukunci a kai ba.

  18. Hukumomi na neman ɗan bindigar da ya harbe limami a Amurka

    Ana ci gaba da neman wani ɗan bindiga wanda ba a san ko wane ne ba, da ya harbe limamin wani masallaci a garin Newark da ke cikin New Jersey a Amurka a ranar Laraba.

    Hukumomi sun faɗa a wani taron manema labarai cewa sun yi imani kisan Imam Hassan Sharif ba shi da alaƙa da ta'addancin cikin gida ko kuma "nuna bambanci".

    An samu Hassan Sharif kwance da raunukan harbi a wajen masallacinsa mai suna, Masjid-Muhammad-Newark, kafin ketowar alfijir.

    Daga bisani kuma rai ya yi halinsa a asibiti sanadin raunukan da ya ji.

    "Shaidar da aka tattara zuwa yanzu ba ta nuna cewa wannan abu na da alaƙa da ƙiyayya ko kuma wani ta'addanci na cikin gida," Atoni Janar na New Jersey Matthew Platkin ya faɗa wa manema labarai.

    Ya ƙara da cewa akasari masu bincike "ba za su fito bainar jama'a da irin wannan bayani da wuri a kan aikinsu ba" sai dai ƙaruwar nuna ƙyamar da ake yi wa Musulmai ce ta tursasa musu bayyana sakamakon farko-farko na bincikensu.

    Gwamnan jihar Phil Murphy ya fitar da wata sanarwa da ke neman duk wanda ke da wani bayani ya fito.

    Maƙwabta sun faɗa wa tashar talbijin ta WABC-TV cewa suna zargin harin na da alaƙa da ayyukan masu laifi a birnin na New Jersey mafi girma.

  19. Dangote ya faɗo daga matsayin attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka

    Mujallar Forbes da ke bibiyar harkokin masu arziƙin duniya, ta ce a yanzu hamshaƙin biloniyan nan ɗan ƙasar Afirka ta Kudu, Johann Rupert ne mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afirka.

    Hakan na nufin Johann Rupert mai shekara 73, ya kere attajirin ɗan kasuwa na Najeriya, Aliko Ɗangote a yawan arziki wanda a baya yake riƙe da matsayin.

    A alƙaluman da Forbes ta fitar na baya-bayan nan, a kan arzikin attajirai a kowacce rana, darajar arzikin Johann Rupert ta kai dala biliyan 10, yayin da Aliko Dangote aka ƙiyasta nasa arzikin a kan dala biliyan 9.7.

    Aliko Dangote, mai shekara 66, ya koma mataki na biyu a jerin masu arzikin Afirka bayan da dukiyarsa ta yi ƙasa daga dala biliyan 13.5 zuwa dala biliyan 9.5 a farkon shekarar 2024.

    Mujallar ta nuna cewa an samu raguwar kuɗin hamshaƙan ƴan kasuwa kamar Rabiu Abdussamad da darajar arzikinsa ya kai dala biliyan 5.7 da Mike Adenuga wanda nasa arziƙin ya kai dala biliyan 3.1.

    Bayanai na cewa raguwar darajar arzikin nasu, ba zai rasa nasaba da yadda darajar naira ke ci gaba da faɗuwa ba, da kuma wasu matsaloli da suka shafi tattalin arziki.

    • Dattawan Arewa sun ce za su sasanta Dangote da AbdusSamad BUA
    • Abu biyar da ya sa Dangote ya ci gaba da zama attijirin Afrika tsawon shekara tara
  20. Sarki Salman zai karɓi baƙuncin masu umrah 1000 a bana

    Sarkin Salman ya amince da karɓar baƙuncin masu Umrah 1,000 daga fadin duniya a shekarar 2024.

    Hakan kuwa na cikin tsare-tsaren bakuncin da mai kula da masallatan biyu zai karba a lokacin Hajji da Umrah da kuma ziyara, da ma'aikatar harkokin Musulunci ta kasar ke aiwatarwa kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyya, SPA ya rawaito.

    Sheikh Abdllatif Al-Sheikh, ministan harkokin Musulunci da Da'awa da kuma Shiryatarwa ya ce baƙin guda dubu sun hada da malaman addinin da shehunnai da masu iko da fitattun mutane da farfesoshi daga jami'o'i domin halartar Umrah da addu'o'i a masallacin Madina.

    Sheikh Abdllatif Al-Sheikh, ministan harkokin Musulunci da Da'awa da kuma Shiryatarwa ya yi godiya ga Yarima mai jiran gado kuma firaiministan kasar, Mohammed bin Salman bisa aikin alkairi.

    Ya ce wannan ya nuna irin yadda sarakunan ke kula da Musulmi da Musulunci da kuma kara yaukaka 'yanuwantaka a tsakanin Musulman wurare daban-daban na duniya.

    • 'Tsadar rayuwa ta sa kuɗina ba za su kai ni Hajji ba a yanzu'
    • Da gaske ne an ji karatu da kiran sallah a ɗakin Ka'aba ba tare da ladani ba?