Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Blinken ya gana da Mahmoud Abbas a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Sai da safe

    Daga nan za mu tsaya a kawo rahotannin kai-tsaye na ranar Lahadi.

    Amma fa za mu sake haɗuwa da ku gobe da safe don kawo wasu sababbi.

    Umar Mikail ne ke addu'ar Allah ya ba mu lafiya.

  2. An yi wa Falasɗinawa addu'o'i a Masallacin Ƙasa na Abuja

    An gudanar da addu’o’i na musamman ga Falasɗinawa a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja, babban birnin Najeriya a yau Lahadi.

    Malamai da dama ne suka hadu don gudanar da addu’o’in ƙarkashin jagorancin jagorancin Farfesa Ahmad Ibrahim Maqri.

    Haka kuma malaman sun gudanar da jawabai na nuna goyom bayan Falasdinawan, tare da kiran a kawo karshen yakın da ake yi a Gaza.

    Kusan wata ɗaya ke nan Isra'ila na luguden wuta a Zirin Gaza bayan mayaƙan Hamas sun kai mata hari ranar 7 ga watan Oktoba.

  3. Tinubu zai tafi Saudiyya

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai tafi Saudiyya a makon nan domin halartar taron Saudiyya da ƙasashen Afirka.

    Da yake magana da manema labarai a fadar gwamantin Najeriya, kakakin shugaban ƙasa Ajuri Ngelale ya ce Tinubu zai je taron ne "da zimmar neman ƙarin zuba jari daga ƙasashen waje".

    Kazalika, shugaban zai halarci taron ƙasashen Larabawa da na Afrka, kuma za su gudana ne a ranakun 10 da 11 ga watan Nuwamba a birnin Riyadh na Saudiyya.

    A cewar Mista Ngelale, Tinubu zai tattauna game da hulɗar tattalin arziki tsakanin nahiyoyin biyu, da yaƙi da ta'addanci, da muhalli, da kuma noma.

  4. Isra'ila ta dakatar da ministanta da ya ce 'za a iya harba wa Falasɗinawa nukiliya'

    An dakatar da wani ƙaramin minista daga shiga duk wata ganawa ta gwamnati har sai hali ya yi bayan nuna cewa "akwai yiwuwar" Is'ra'ila za ta iya harba bam ɗin nukiliya kan Falasɗinawa a Zirin Gaza.

    Amihai Eliyahu, wanda shi ne ministan al'adu, ya yi kalaman ne yayin wata hira da gidan rediyon masu tsattsauran ra'ayi matuƙa a Isra'ila mai suna Kol Beramah.

    Ya ce "babu wasu fararen hula a Gaza" kuma bai wa Falasɗinawa agaji gazawa ce.

    Da aka tambaye shi ko amfani da nukiliya a kansu ba zai zama laifi ba, ministan bai kawar da hakan ba.

    Firaminista Benjamin Netanyahu ya yi martani cikin sauri, yana mai cewa kalaman "ba su dace da manufarsu ba".

  5. Chadi ta janye jakadanta daga Isra'ila saboda 'hare-hare a kan Gaza'

    Ƙasar Chadi ta ce ta kira jakadanta a Isra'ila zuwa gida don tattaunawa game da "hare-hare da tashin hankalin da ba a taɓa gani ba a Zirin Gaza".

    Cikin wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen ƙasar, gwamnati ta yi tir da "rasa rayukan fararen hula kuma ta yi kira a tsagaita wutar da za ta kai ga samun kwanciyar hankali ga Falasɗinawa".

    A shekarar 1972, Chadi wadda Musulmai suka fi rinjaye, ta yanke hulɗar da jakadanci tsakaninta da Isra'ila, har sai a 2019 suka daidaita.

    Yanzu Chadi ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta ɗauki irin wannan mataki tun bayan fara yaƙin a ranar 7 ga watan Oktoba.

    Zuwa yanzu, ƙasashen Turkiyya, da Chile, da Bahrain, da Honduras, da Colombia, da Jordan sun janye jakadunsu daga Isra'ila don nuna ɓacin ransu da hare-haren na Isra'ila a Gaza.

    Isra'ila ta ce mayaƙan Hamas sun kashe mutum 1,400 lokacin da suka kai hari ranar 7 ga Oktoba, inda ta ci alwashin ganin bayan ƙungiyar a hare-haren ramuwar gayya - waɗanda suka kashe Falasɗinawa sama da 9,500 zuwa yanzu.

  6. Tsagaita wuta zai ba Hamas damar sake shiri don kai hare-hare - Anthony Blinken

  7. Sojojin Isra'ila sun ce sun harbo jirgi maras matuƙi a Lebanon

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta sun samu nasarar harbo wani jirgi maras matuƙi da aka saita ya nufi ƙasar daga Lebanon.

    Sojojin sun ce sun harbo jirgin ƙasa tun kafin ya fice daga ƙasar ta Lebanon.

    Haka kuma sojojin sun ce an harba makaman tarwatsa tankokin yaƙi masu yawa daga Lebanon zuwa ƙasarsu, inda suka mayar da martani ta hanyar harba makaman atilare.

  8. Sojojin Najeriya sun gano masana'antar ƙera makamai a Plateau

    Dakarun sojin Najeriya sun ce sun gano tare da lalata wata masana'antar da ake ƙera makamai ba bisa ƙa'ida ba a unguwar Vom da ke ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a jihar Plateau da ke tsakiyar Najeriya.

    Cikin wani saƙo da rundunar sojin ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, ta ce ta gano bindigogi masu yawa a lokacin samamen.

    Daga cikin bindigogin da sojojin suka gano a masana'atar akwai ƙirar AK-47 shida, da ƙananan bindigogi masu sarrafa kansu guda huɗu da jakankunan AK 11 da ƙaramar bindiga ƙirar Pistol.

    Sauran abubuwan da sojojin suka ce sun gano, sun haɗar da kwanson saka alburusai na AK-47 huɗu, da sauran kayyakin ƙera bindigogi daban-daban.

    Haka kuma sanarwar ta ce sojojin sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a gudanar da masana'antar.

  9. Hamas ta ce mutum 9,770 aka kashe a Gaza

    Ma'aikatara lafiyar Hamas a Gaza ta saki alƙaluman adadin mutanen da aka kashe a Gaza.

    Ta ce Falasɗinawa - ciki har da ƙananan yara 4,800 - aka kashe tun bayan harin 7 ga watan Oktoba, lokacin da Isra'ila ta fara kai hare-haren bom a Gaza, a wani mataki na ramuwar gayya kan hare-haren da Hamas ta kai mata, tare da kashe mutum 1,400 tare da kama mutum 240.

  10. Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu

  11. ƙungiyoyin fararen hula na son a kama mutanen da ake zargi da almundana a Nijar

    A Jamhuriya Nijar wasu 'yan ƙungiyoyin fararen hula sun gudanar da zanga-zanga a Yamai babban birnin ƙasar.

    Inda suke kira ga sojojin mulkin ƙasar su kama mutanen da ake zargi da yin almundahana da dukiyar ƙasar.

  12. Blinken ya gana da Abbas a birnin Ramallah

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya gana da shugaban Falasɗinawa, Mahmoud Abbas.

    Blinken ya ''jaddata burin MAurka na kai kayayyakin buƙatun rayuwa zuwa da ci gaba da muhimman ayyuka'' a Gaza, kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar wajen Amurka, Matthew Miller ya bayyana.

    Ya kuma bayyana ƙarara cewa "ba za a tilasta wa Falasɗinawa barin muhallansu ba".

    Mista Blinken da Mahmoud Abbas sun tattauna yunƙuri "maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali" a Gabar Yamma da Kogin Jordan, ciki har da buƙatar ''dakatar da ayyukan cutarwar da ake yi wa Falasdinawa, tare da kama mutanen da ke aikata hakan", in ji Mista Miller.

  13. 'Yan bindiga sun saki ɗalibin Kaduna da ya shafe fiye da shekara biyu a hannunsu

    Masu garkuwa da mutane sun saki ɗalibin - makarantar Bethel Baptist ta Kaduna - bayan shafe fiye da shekara biyu a hannunsu.

    A ranar Juma'a ne aka saki Treasure Ayuba, wanda shi ne ɗalibi na ƙarshe da ya rage a hannun masu garkuwa da mutanen, bayan shafe shekara biyu da wata huɗu a hannunsu.

    Yayin da yake tabbatar wa BBC sakin ɗalibin, shugaban ƙungiyar Kiristoci ta CAN reshen jihar Kaduna, Rabaren Joseph Yahab - wanda kuma jagoranci gwagwarmayar sakin ɗaliban da aka sacen, ya ce a yanzu ɗalibin na tare da iyayensa bayan an kai shi asibiti domin yi masa gaje-gwaje.

    A cikin watan Yulin 2021 ne dai wasu gungun 'yan bindiga suka dirar wa makarantar 'Bethel Baptist High School' da ke ƙauyen Maraban Damishi a ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna, inda suka sace ɗaliban makarantar 121.

    Gwamnan jihar sanata Uba sani ya bayyana jin ɗaɗinsa da sako ɗalibin.

    Yayin da yake gidayarsa ga ubangiji kan wannan lamari, Gwamnan ya kuma gode wa mutane hukumomi bisa ƙoƙari da addu'o'in da suka yi don tabbatar da kuɓutar da ɗalibin.

    Jihar Kaduna na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar 'yan bindiga da ke kai samame ƙauyuka da sace mutane don neman kuɗin fansa, da ƙona musu gidaje bayan sace dukiyoyinsu.

  14. Amsoshin Takardunku

  15. Blinken zai gana da shugaban Falasɗinawa

    A yayin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ke ziyara a yankin Gabas ta Tsakiya a yunkurinsa na kawo lalama a ricin Gaza, nan gaba kaɗan ne ake sa ran zai gana da shugaban Falasdinawa.

    Mista Blinken - wanda a ranar Juma'a a ziyar Tel Aviv, sannan ya ziyarci birnin Amman a ranar Asabar - ya nufin birnin Ramalla a abar Yamma da Kogin Jorda inda Isra'ila ta mamaye, inda ake sa ran zai gana da shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas.

    Mahmoud Abbas - wanda ya kasance shugaban hukumar Falasɗinawa ta (PA) tun a shekarar 2005 - ɗan jam'iyyar Fatah ne, kuma babban abokin hamayyar jam'iyyar siyasa ta Hamas da ke iko da Gaza.

    PA ce ke iko da wasu sassan yankunan Gabar Yamma da Kogin Jordan waɗanda ba sa ƙarƙashin ikon Isra'ila.

    Idan an jima ne ake sa ran Mista Blinke zai wuce zuwa Turkiyya.

  16. An sake yin zanga-zangar goyon bayan Gaza a Birtaniya da Amurka

    Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a garuruwa da biranen Birtaniya ranar Asabar, don neman kawo ƙarshen hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza.

    'Yan sansan Landan sun ƙiyasta cewa kimanin mutum 30,000 suka yi zanga-zangar a birnin Landan kaɗai.

    A tasoshin jiragen ƙasa na Edinburgh da Glasgw da na birnin Landan, masu zanga-zangar sun yi ta zama a ƙasa inda suka hana fasinjoji shiga jirage, in ji 'yan sanda.

    Can ma a Amurka dubban mutane ne suka gudanar da da wata gagarumar zanga-zanga a birnin Washington DC, ranar Asabar a kusa da fadar gwamnatin ƙasar, inda wasu ke sukan shugaban ƙasar kan goyon bayan Isra'ila.

    Masu zanga-zangar sun rike tutar Falasɗinawa da kwalayen da ke ɗauke da saƙonni daban-daban da ke nuna "Rayukan Falasɗinawa na da muhimmanci" da wasu kuma da ke nuna cewa ''A kawo ƙarshen mamayar Gaza a yanzu".

    Haka ma a birnin Paris na Faransa, an gudanar da babar zanga-zanagr nuna goyon baya ga Falasɗinawa, bayan da baya hukumomin ƙasar suka dakatar da yunƙurin zanga-zanagr a baya saboda rashin zaman lafiya.

  17. 'An kai hari sansanin 'yan gudun hijira a Gaza tare da kashe da dama'

    Ma'aikatar lafiyar Hamas a Gaza ta ce Isra'ila ta ƙaddamar da mummunan hari ta sama a tsakiyar Zirin Gaza.

    Mai agana da yawun ma'aikatar ya ce fiye da mutum 30 aka kashe a sansanin 'yan gudun hijira na al-Maghazi ranar Asabar da daddare.

    Mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila ya ce za su duba ko dakarunsu sun kai hari wannan yanki a daidai wannan lokaci, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

    AFP ya kuma zanta da wani ɗan jarida mai suna Mohammed Alaloul wanda ya ce an kashe 'ya'yansa biyu, da ɗan'uwansa guda a harin.

    BBC ba ta iya tantance abin da ya faru a lamarin ba.

  18. Sakataren harkokin wajen Amurka zai je Turkiyya

    Sakataren hsrkokin wajen Amurka Antony Blinken zai je Turkiyya bayan wani bulaguro da yake yi a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ya gana da shugabannin ƙasashen yankin - waɗanda suka ɓukace shi da sanya bakin don tsagaita wuta a Gaza.

    An samu zanga-zanga a Turkiyya gabanin ziyarar Mista Blinken.

    A baya-bayan na shugaban ƙasar Turkiya, Recep Tayyip Erdoğan, ya yi kakkausar suka ga Isar'ila da ƙasashen Yamma da ke goya mata baya, yayin adadin mutanen da ke mutuwa a Gaza ke ƙaruwa.

    Blinke ya jaddada goyon bayan sa kan "tsagaita wuta" ta yadda fararen hula za su iya samun taimako.

    A ranar Asabar ne kuma shugaban Amurka Joe Biden ya ce akwai alamun nasarar tsagaita wutar.

    Kawo yanzu dai firaminsitan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ba za tsagaita wuta ba, har sai an saki duka mutanen da Hamas ke garkuwa da su.

  19. Me ya sa ba za a buɗe mashigar Rafah ga kowa ba?

    Yayin da rikicin Isra'ila da Hamas ke ci gaba da rincaɓewa, hankali duniya ya koma kan mashigar Rafah da ke kan iyakar Masar da Gaza.

    Kasancewar duk sauran iyakokin Gaza da Isar'ila a rufe suke, Rafah ce kawai hanya ɗaya tilo da ake iya amfani da ida wajen shigar da kayan agaji, ko kuma fita ga mutanen da suka maƙale a Gaza.

    Sai dai ita kanta Mashigar Rafah na ƙarƙashin sa-idon Masar, kuma ita kanta ba koyaushe ne take a buɗe ba.

    Cikin wannan bidiyon mun kawo mubayai game da dalilan Masar na sanya-do, da taka-tsantsan kan mashigar

  20. Ukraine ta kai hari kan jirgin ruwan Rasha

    Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce Ukraine ta kai wa jirgin ruwanta hari a birnin Kerch mai tashar ruwa da ke yankin Crimiea da ta mamaye.

    Rashar ta ce a ranar Asabar Ukraine ta harba makamai masu linzami 15, amma dukansu sojinta sun kakkaɓo su, sai guda ɗayan nan da ya faɗa kan jirgin ruwan.

    Tun da fari, sojin Ukraine sun wallafa a shafin Telegram cewa sun yi nasara a harin da suka kai birnin na Kerch.

    Wani ɗan jarida mai goyon bayan Ukraine ya ce harin ya faɗa kan ƙaramin jirgin ruwan Rasha mai suna Askold, sai dai babu hoto ko bidiyon da ya tabbatar da bayanin nasa.