Rundunar 'yan sandan jihar Gombe ta kama wani matashi mai shekara 18, bisa zargin kashe wata uwa mai 'ya'ya takwas.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar , ASP Mahid Abubakar, ya ce sun samu rahoto daga wani mutum mai suna Muhammad Abdullahi, mai shekara 45, da ya ce wani mutum ya kashe mahaifiyarsa da wuƙa
ASP Abubakar, ya ce rundunar 'yan sandan ta tura jami'anta da ke Pantami, inda lamarin ya faru, inda aka samu matar mai shekara 58 kwance cikin jini.
Daga nan aka garzaya da matar, mai suna Aishatu Abdullahi babban asibitin koyarwa na jami'ar Gombe, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta
Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa a lokacin da jami'an tsaron ke tuhumarsa.
''Ya bayyana yadda ya lallaɓa ya shiga ɗakin matar domin neman sifanarsa da ya ce ta ƙwace masa. bayan da ta shiga ɗakin ta same shi, sai ta tambaye shi dalilin shigarsa ɗakinta, amma ya ƙi ficewa daga ɗakin, a maimakon haka sai ya far mata, ya shaƙe ta tare da kashe ta da wuƙa, daga nan ya yi ficewarsa, ya bar wuƙar da rigarsa da jini ya taɓa, amma kuma ya fita da sifanar", kamar yadda mai magana da yawun 'yan sandan ya bayyana.
ASP Abubakar, ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya ce ya aikata laifin ne da taimakaon wani matashi mai shekara 17.
Wanda shi ma rundunar ta kama shi, amma kuma ya musanta hannu a aikata laifin.