Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Isra'ila na shirin kai hare-hare a Gaza 'ta ruwa, sama da ƙasa'

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Isra'ila na shirin kai hare-hare a Gaza 'ta ruwa, sama da ƙasa'

    Rundunar sojan Isra'ila ta ce tana shirin faɗaɗa yaƙin da take yi a kan Zirin Gaza ta ruwa, da sama, da ƙasa.

    "IDF [sojin Isra'ila] na shirin ƙaddamar da babban samame" tare da taimakon sojojin ko-ta-kwana, a cewar wata sanarwa daga rundunar.

    Ba a faɗi lokacin kai hare-haren ba amma da ma can ana tsammanin Isra'ila za ta kai hari ta ƙasa cikin Gaza, inda ta umarci mazauna birnin su fice daga arewaci zuwa kudanci.

    Ta ce tana shirya wani samame "ta sama, da ruwa, da ƙasa, in ji sanarwar.

  2. 'Yan sanda sun kama mutanen da suka yi 'yunƙurin sace taragon jirgi a Maiduguri'

    Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Borno ta ce ta kama wasu mutane da suka yi yunƙurin sace tarago-tarago na jiragen ƙasa daga tashar jirgin da ke birnin Maiduguri.

    Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Mohammed Yusufu Lawan, ya ce an kira su daga tashar jirgin kuma aka shaida musu cewa an ga wata babbar mota na shirin kwashe tarago-taragon, inda jami'ansu suka isa cikin gaggawa.

    "Kayan sun haɗa da taragon jirgi uku, kuma a nan take muka kama wani mutum mai suna Aliyu Mainasara," kamar yadda kwamishinan ya faɗa wa gidan talabijin na NTA.

    "Wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa shugaban hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa na Najeriya ne ya ba shi umarnin kwashe taragon zuwa jihar Filato saboda gwamnatin jihar za ta ƙirƙiri layin dogo a cikin birnin Jos."

    Sai dai kwamishinan ya ce mutumin bai nuna wata shaida da za ta tabbatar da iƙirarin nasa ba.

    Wasu kafofin yaɗa labarai a Najeriya na cewa mutum shida 'yan sandan suka kama da zargin sace tarago-taragon.

  3. Su wane ne mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su daga Isra'ila?

    Yayin da adadin waɗanda suka mutu a Isra'ila da Gaza ke ci gaba da ƙaruwa, akwai aƙalla mutum 150 da mayaƙan Hamas suka yi garkuwa da su.

    Ƙungiyar gwagwarmayar ta Falasɗinawa ta ce tana riƙe da su "a wurare masu aminci da hanyoyin ƙarƙashin ƙasa" a Gaza kuma ta yi barazanar kashe su idan Isra'ila ba ta daina ruguza gidajen farar hula ba a birnin ba tare da gargaɗi ba. .

    Daga cikinsu akwai Maya Regev mai shekara 21, da ɗan uwanta Itay mai 18, waɗanda aka ɗauke su daga Herzliya.

    Suna cikin matasan da ke halartar bikin Supernova a kudancin Isra'ila. A safiyar ranar da aka kai harin, mahaifin Maya ya ji muryar 'yarsa a waya tana cewa "baba suna harbi na!".

    Danginta sun ce daga baya sun gan ta sanye da ankwa a bayan wata mota cikin wani bidiyo da Hamas ta fitar.

  4. 'Yadda Putin ke son ya ci gajiyar yaƙin Isra'ila da Gaza'

  5. Har da ƙananan yara cikin mutanen da Isra'ila ta kashe suna guduwa a Gaza

    Tun a daren da ya gabata ne aka fara yaɗa bidiyon harin da Isra'ila ta kai kan wani jerin motoci da ke ɗauke da Falasɗinawan da suke guduwa daga arewaci zuwa kudancin birnin Gaza.

    Sashen BBC Verify ya tabbatar da cewa an kai harin ne a kan Titin Salah-al-Din, ɗaya daga cikin hanyoyin da masu guduwar ke daga arewa zuwa kudancin birnin.

    Titin cunkushe yake tsawon rana a jiya yayin da mazauna birnin ke bin umarnin Isra'ilar na tserewa daga yankin saboda hare-haren da take shirin kaiwa.

    Aƙalla mutum 12 ne aka gani a bidiyon sun mutu, wanda ya yi munin da ba za mu iya nuna shi ba.

    Akasarinsu mata ne da ƙananan yara - wasu daga ciknsu ba su fi shekara biyu zuwa biyar ba. Yanayin da aka ɗauki bidiyon ya nuna lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin birnin.

    Akasarinsu na kwance ne a bayan wata motar a-kori-kura - wasu kuma sun watsu a kan titin. Akwai kuma wasu ababen hawan warwatse a titi bayan an lalata su.

  6. Netanyahu ya ziyarci dakarun Isra'ila a filin daga

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya wallafa wani bidiyo da ke nuna shi yana ziyartar dakarun ƙasar a filin daga.

    Ya rubuta saƙon cewa: "Tare da sojoji a filin yaƙi da Gaza, Mun shirya tsaf."

    Wata sanarwa daga ofishinsa ta daban ta ce firaministan ya faɗa wa dakarun da ke jibge a wajen Zirin Gaza cewa "shin kun shirya shiga mataki na gaba? Mataki na gaba na ƙaratowa."

  7. Duk wanda ya mamaye ƙasarmu maƙiyinmu ne - Tsohon shugaban Hamas

    Tsohon shugaban ƙungiyar Hamas ya ce yana alfahari da harin da mayaƙan Hamas suka kai Isra'ila a makon da ya gabata, yana mai cewa harin "yunƙuri ne na kawo ƙarshen mamayar Isra'ila".

    Yayin da yake magana gidan talbijin na Haberturk TV, shugaban hulda da ƙasashen ƙetare na ƙungiyar Hamas, Khalid Meshal ya ce rikici tsakanin Irsa'ila da Falasɗinu ya samo asali ne tun shekarar 1948, ba makon jiya ba.

    "Isra'ila na cewa tana da ƙarfin soji, suna cewa ba za a ci galaba a kansu ba. Amma mun yi mamakin yadda aka ci galaba a kansu a makon da ya gabata," in ji shi.

    Da aka tambaye shi game da yadda mayaƙan Hamas ke kai wa fararen hula da ƙananan yara da tsofaffi hari, sai ya ce "Muna faɗa wa mayaƙanmu ka da su yi haka. To amma a lokutan yaƙi irin wadannan ala'umar kan faru. Ba wai yadda Isra'ila ke faɗa a koyaushe cewa ba ta kashe fararen hula".

    Da aka tambaye shi ko Hamas na aikata irin abin da take zargin Isra'ila da aikatawa? Mista Meshal ya ce "akwai babban bambanci".

    "Wannan ƙasarmu ce. Idan maƙiya suka zo daga waje, ko sojoji ko fararen hula, duk dai maƙiya ne, duk wanda ya zo ƙasarmu domin mamaya maƙiyinmu ne, kuma mai laifi".

  8. An lalata gine-gine fiye da 1,000 a Gaza - MDD

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da gine-gine dubu guda ne suka ruguje a Zirin Gaza a tsawon mako guda da Isra'ila ta ɗauka tana ruwan boma-bomai a birnin.

    Hukumar jin ƙai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ɗakuna 5,540 ne suak ruguje, yayin da gidaje kusan 3,750, suka lalace sakamakon hare-haren.

  9. Bidiyon yadda fararen hula ke ficewa daga Gaza

    Bidiyon yadda fararen hula ke ficewa daga arewacin birnin Gaza, cikin motoci da kuma ƙafafuwansu

  10. Hotunan hawan daba a fadar Sarkin Zazzau Suleja

  11. Lafiya Zinariya: Matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa

    Shirin Lafiya Zinariya na wannan makon ya duba batun matsalolin da suka shafi lafiyar ƙwaƙwalwa da alamomin kowacce.

  12. Labarai da dumi-dumi, Ƙatar da Saudiyya kai tsaye sun yi watsi da umurnin tayar da 'yan Arewacin Gaza

    Ƙatar da Saudiyya kai-tsaye sun yi watsi da batun tayar da Falasdinawa daga Gaza, bayan da Isra'ila ta ce su bar arewacin Gaza zuwa kudancin birnin.

    Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar ta yi kira da a 'dakatar da ƙwace Zirin Gaza, tare da bayar da cikakkiyar kariya ga Falasɗinawa fararen hula kamar yadda dokokin duniya da na jinƙai suka yi tanadi''.

    Ita ma takwararta ta Saudiyya cikin wani saƙon da ta wallafa a shafinta na X, ta yi kira da a samar da tallafin magunguna ga mazauna Gaza.

    "Hana musu waɗannan muhimman abubuwan buƙata domin gudanar da rayuwa cikin mutuntawa ka iya haifar da saɓa wa dokokin ƙasashen duniya kan jinƙai".

  13. Majalisar dattawa za ta yi ƙudurin cin tarar iyayen da suka ƙi kai 'ya'yansu makaranta

    Majalisar Dattijai ta yi karatun farko ga wani ƙuduri da ke neman a ci tarar naira 50,000 ga iyayen da suka gaza bai wa 'ya'yansu ilmin firamare da sakandire.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa Majalisar ta kuma buƙaci a riƙa bai wa kowanne yaro abinci kyauta a Najeriya.

    Ƙudurin wanda Sanata Orji Kalu ya gabatar mai taken 'Dokar ba da ilmi kyauta kuma dole a matakin farko ga kowa ta 2004, Sashe na 2, na cewa kowacce gwamnati a Najeriya ta samar da ilmin bai ɗaya kyauta kuma dole ga duk yaron da ke cikin shekarun shiga firamare da ƙaramar sakandire.

    Ƙudurin dokar ya kuma ce "Duk iyaye su tabbatar da cewa yaronsu sun halarta kuma sun kammala ilmin firamare da na ƙaramar sakandire ta hanyar ƙoƙartawa wajen tura su makarantar firamare da kuma ta sakandire".

    Dokar ta kuma bayyana cewa masu ruwa da tsaki a fannin ilmi cikin ƙananan hukumomi su tabbatar cewa dukkan iyaye ko wani mutum da ke kula ko riƙon wani yaro, ya sauke nauyin da aka ɗora masa a ƙarƙashin sashe na 2, ƙaramin sashe na 2 na wannan Doka.”

    Ƙudurin ya kuma yi nuni da cewa matuƙar mahaifi ya saɓa wa tanadin da aka zayyana tun farko, to ya aikata laifi, kuma idan aka same shi da laifi a karon farko, a tsawatar masa.

    Sai dai yanzu Majalisar Dattijai a gyaran fuskar da take ƙoƙarin yi, tana yunƙurin sauya tarar naira 5,000 da ke cikin dokar zuwa naira 50,000.

  14. Gane Mini Hanya

    Wata matsala da jama’a ke fama da ita ba tare da sun san sun da ita ba, ita ce ta idanu.

    Mafi yawancin lokuta za ka ga mutum ya fara da lumshe idanu, kafin daga bisani a rasa idanu baki daya.

    Likitoci dai na yawan shawartar al’umma da su rinka zuwa gwajin idanu a kai a kai, domin guje wa larural rashin gani.

    A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai aka yi bikin ranar lafiyar idanu ta duniya.

    Usman Minjibir ya tattauna da kwararrun likitocin idanu da suka kawo mana ziyara a ofishinmu na Abuja a makon.

    Ga kuma yadda tattaunawar ta su ta kasance.

  15. Labarai da dumi-dumi, 'An kashe kwamandan Hamas da ya jagoranci harin Isra'ila'

    Ma'aikatar tsaron Isra'ila ta ce ta kashe Ali Qadhi, kwamandan Hamas da ya jagoranci harin kan iyaka da aka kai kan gine-ginen Yahudawa ranar Asabar ta da gabata.

    Sojojin Isra'ila sun ce an kashe Ali Qadhi, a lokacin wani hari da jirgi maras matuƙi, bayan samun bayanan sirri sakamakon ƙoƙarin da hukumar leƙen asiri ta Shin Bet da kuma Cibiyar Tattara Bayanan Sirri ta Sojin Isra'ila.

  16. Hotunan bikin cikar sarkin Zazzau Suleja shekara 30 a kan karagar mulki

  17. Gwamnatin Kano ta shirya wa amaren da ta aurar walima

    A jihar Kano a yau ne gwamnatin jihar za ta shirya wa amare da angwayen da aka ɗaura wa aure jiya walima.

    Zawarawa da 'yan mata 1,800 ne gwamnatin ta ɗaura wa aure ƙarƙashin shirin auren gata a ranar Juma'a

    Kuma a yau ne za a yi biki da miƙa masu takardar shaidar ɗaurin auren a gidan gwamnati.

    Ga rahoton Zahraddeen Lawan daga Kano

  18. Isra'ila da Masar sun amince Amurkawa su fice daga Gaza

    Wani Jami'in Amurka ya ce 'yan ƙasar da ke birnin Gaza za su iya ficewa daga birnin ta kan iyakar Masar.

    Za a buɗe kan iyakar daga ƙarfe 12 na rana zuwa 5:00 na maraice agogon ƙasar, bayan cimma wata yarjejeniya tsakanin Isra'ila da gwamnatin Masar.

    Kawo yanzu ba a san ko Hamas - wadda ke iko da Gaza - za ta bar Amurkawan su fice daga birnin ba.

  19. 'Fiye da mutum 2,200 aka kashe yayin da 8,700 suka jikkata a Gaza'

    Ma'aikatar lafiyar Palasɗinu ta ce aƙalla mutum 2,215 ne aka kashe, yayin da mutum 8,714 suka jikkata a birnin Gaza sakamakon hare-hare da ake kai wa birnin.

    Mutum 54 ne aka kashe a Gabar Yamma da Kogin Jordan, yayin da aka jikkata 1,100, kamar yadda ma'aikatar ta bayyana.

  20. Sojojin Isra'ila sun ce Hamas na riƙe da 'yan ƙasar fiye da 120

    Ma'aikatar tsaron Isra'ila ta ce ƙungiyar Hamas na riƙe da 'yan kasarta fiye da 120 da ta kama a lokacin harin da ta kai a makon da ya gabata.

    Cikin wani saƙo da ma'aikatar da wallafa a shafinta na X ta ce ta "tabbatar da cewa akwai fararen hula fiye da 120 da Hamas ke riƙe da su a Gaza''.