Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Yan ƙwadago sun sanar da aniyar shiga yajin aiki a Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi and Zulaiha Abubakar

  1. Tinubu ya amince da sayo wa sojojin kasa jiragen helikwafta 12

    Shugaba Bola Tinubu ya amince da fitar da kudi don sayo jiragen helikwaftan kai hari guda 12 ga rundunar sojin kasa ta Najeriya.

    Babban hafsan rundunar, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ne ya sanar da haka yayin bude wani taron kara wa juna sani kan harkokin sufurin sama a rundunar sojin kasan Najeriya ranar Talata a Abuja.

    Ya ce jiragen helikwafta samfurin MD 530F Cayuse na kai farmaki zai ba da damar fara aiki ga sashen sufurin sama na rundunar sojin kasan Najeriya, wanda aka kafa don bunkasa zafin nama ga dakarun kasa da kai dauki da tasiri a lokatun ayyukan soja.

    Laftanal Janar Lagbaja ya yi bayanin cewa dakarun sashen sufurin sama daban ne da rundunar sojin saman Najeriya, amma dai galibi ana tanadar musu da jiragen helikwafta da kananan jiragen da ke tallafawa ayyukansu.

    Ya yaba wa shugaban kasa saboda amincewa da bukatar rundunar sojin kasa na samar mata da sashen dakarun sufurin sama mai kayan aiki, da zai rika tallafa wa dakarun kasa a lokacin ayyukansu.

  2. Najeriya ta ce ta fitar da naira biliyan 1.3 don biyan iyalan 'yan sandan da suka mutu

    Babban Sufetan ƴan sandan Najeriya na riƙo, Mr Olukayode Egbetokun, ya mika cakin kuɗi da ya kai naira biliyan 1.3 ga iyalan ƴan sandan da suka mutu a bakin aiki.

    Mista Olukayode Egbetokun, ya ce " cakin kuɗin na shekarar 2021 zuwa 2023 ne ƙarƙashin dokar inshorar ƴan sanda ta Najeriya."

    Ya ce taron ya ƙunshi kaddamar da shirin inshorar babban sufetan ƴan sanda na kyautata rayuwar iyali.

    Mista Egbetokun, ya ce shiri ne da gwamnatin Najeriya ke ɗaukar nauyinsa.

    "Manufar shirin ita ce domin samar da sassauci ga rayuwar iyalan ƴan sandan da suka mutu, kuma yanzu haka kuɗin na ƙasa domini fara biyan su." in ji Mista Egbetokun

    Ya ƙara da cewa hukumar yan sanda ta yi amannar cewa rayuwar kowanne ɗan'adam na da matuƙar muhimmanci.

    Ya yi kira ga jagororin shirin a kan su tabbatar da shirin ya kai ga inda ake buƙata ba tare da nuna ɓangaranci ba.

  3. An ba da umarnin rage wa mutane kudin ruwan famfo a Birtaniya

    An umarci kamfanonin samar da ruwan sha su mayarwa abokan huldarsu fam miliyan 114 ta hanyar rage musu kudin ruwan da suka sha, bayan kamfanonin sun gaza cimma burin da aka sanya musu.

    Hukumar kula da kamfanonin samar da ruwa a Birtaniya Ofwat, ta ce kamfanonin sun "gaza" a mizanin kwazonsu wajen kula da tsiyayar bututun ruwa da kawo ruwan da kuma rage bayar da ruwa gurbatacce.

    Ta ce bayan wani nazari da aka yi, za a mayar wa masu gidaje miliyoyin fam ta hanyar rage musu kudaden ruwan da suka sha.

    Ofwat ta sanar a cikin rahoton kididdigar da ta fitar cewa babu kamfani ko guda daya da ya taba cimma mizani mafi girma a kwazon aikinsa.

    Hukumar ta tantance kamfanonin ruwa ne a Ingila da Wales a kan inganta ayyukansu kamar yadda aka sanya musu buri daga shekara ta 2019 a tsawon wa'adin shekara biyar.

    • Garin da mata suke kin auren mazan da babu ruwan famfo a gidajensu
  4. Wanne tasiri kotun tafi da gidanka ta mata za ta yi a Najeriya?

    Masu rajin kare 'yancin mata a Najeriya sun yi maraba da matakin kafa kotunan tafi-da-gidanka da ministar mata ta Najeriya ta ce za ta tabbatar da ganin an bullo da su domin shawo kan matsalar cin zarafin mata a kasar.

    Ta ce "Gwamnatin na kashe maƙudan kuɗi domin magance matsalar amma har yanzu ba ta sauya zani ba.

    Latsa hoton da ke ƙasa domin jin ƙarin bayani a tattaunar da Raliya Zubairu ta yi da wata 'yar fafutuka kuma shugabar kungiyar global initiaive for women and children, Hajiya Hafsat Mohammad Baba.

  5. Gwamnatin Myammar na kone mutane da ransu a kasar - MDD

    Ofishin kare 'yancin ɗan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ya zargi shugabannin mulkin soja na kasar Myanmar kan abin da ya kira da 'nuna tsabagen rashin tausayi' irin wanda suka saba a kan fararen hula.

    Shugaban ofishin na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk ya shaida wa majalisar kare hakkin dan'adam cewa jagororin mulkin sojin na amfani da hanyoyin rashin imani da suka hadar da sare kawunan mutane da kona mutum da ransa a kokarinsu na murkushe tawaye.

    Ya ce suna amfani da luguden bama-bamai ta sama da aikata kisan kare dangi da kuma kone kauyuka sannan suna shiga garuruwan da jama'a ba su gudu ba, su kashe su.

    Mista Turk , ya kuma ƙara da cewa kananan yara na cikin wadanda ake azabatarwa, inda ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniyar ta hukunta shugabannin mulkin sojin.

  6. Shugaba Biden ya kafa tarihin shiga sahun ma'aikatan da ke zanga-zanga

    Shugaban Amurka Joe Biden ya goyi bayan ma'aikatan kamfanonin kera mota da ke yajin aiki a Michigan yayin wata ziyara da ya kai wata cibiya da suka datse.

    A wani mataki na farko da Shugaban Amurka ya yi.

    Mista Biden ya ce ma'aikatan sun "cancanci" karin albashi da kuma sauran ragwamen da suke nema.

    Ziyarar ta zo ne kwana guda kafin mutumin da ke kokarin samun tikitin tsayawa takara don kalubalantar sa, Donald Trump, ya isa wurin masu yajin aikin.

    Sai dai ma'aikatan sun fada wa BBC cewa suna jin cewa abokan hamayyar biyu suna iya mayar da yajin aiin nasu batun siyasa, don haka suka bukaci kawai "su janye jiki".

    A wani jawabi takaitacce ga ma'aikatan da suka rufe cibiyoyin ranar Talata, shugaban kasar na jam'iyyar Dimokrat ya ce sun "cancanci samun gagarumin karin albashi da kuma sauran bukatu".

    Ya kara da cewa kamata ya yi ma'aikata su kasance "masu matukar bunkasa" kamar kamfanonin da suka dauke su aiki.

    Gabanin ziyarar, wasu ma'aikatan an ji tamkar gwiwarsu ta yi sanyi game da ziyarce-ziyarcen.

  7. Yaushe za a fara Gasar Cin Kofin Afirka ta 2023?

  8. Majalisa ta tabbatar da nadin sabon gwamnan CBN Dr Olayemi Cardoso

    Sabon Babban Bankin Najeriya Olayemi Cardoso ya ce babban abin da zai fi bai wa fifiko shi ne ya tabbatar da biyan dumbin kudaden waje da masu bashi na cikin gida ke bin bankin, wanda aka kiyasta zai iya kai wa har dala biliyan bakwai.

    Daukacin 'yan majalisar dattijai ne suka amince da nadin Cardoso a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya bayan ya bayyana gaban 'yan majalisar don tantancewa.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce majalisar ta kuma tabbatar da nadin mataimakan gwamnan bankin su hudu.

    Sun hadar da Mrs. Emem Nnana Usoro da Muhammad Sani Abdullahi Dattijo da Mr. Philip Ikeazor da kuma Dr. Bala M. Bello,

    Olayemi Cardoso ya yi alkawarin zai inganta gudanar da ayyuka a fayyace da gyara tsarin gudanar da harkoki sannan ya dawo da kwarin gwiwar da ke raguwa cikin harkokin babban bankin da kuma kimarsa.

    Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin gudanar da wani gagarumin garambawul cikin manufofin gudanar da harkokin kudi lokacin rantsar da shi a watan Mayu bayan ya soki lamirin yadda tsohon gwamnan babban bankin ke tafiyar da harkokin kudi.

    Cardoso ya ce da zarar bankin ya gama tantance bashin da ake bin sa, zai sam hanyar da zai fara biyan kudaden cikin gaggawa.

  9. Kotu ta tabbatar da nasarar zaben Gwamna Inuwa Yahaya

    Kotun sauraron kararrakin zabe ta tabbatar da nasarar Gwamna Inuwa Yahaya, bayan ta kori korafe-korafen 'yan takarar PDP da na ADC.

    Dan takarar jam'iyyar PDP Jibrin Barde da kuma na jam'iyyar ADC Nafiu Bala sun kalubalanci sake zaben Inuwa Yahaya na jam'iyyar APC ne bayan zaben watan Maris.

    Sai dai ayarin alkalan kotun mai mutum uku gaba daya ya yi watsi da korafe-korafen biyu saboda rashin tushe. Jam'iyyar PDP ta yi zargin cewa an tafka magudi, kuma Inuwa Yahaya bai ci zaben da rinjayen halastattun kuri'u ba.

    Kotun amma ta yi watsi da korafin saboda a cewarta masu karar sun gaza kawo shaidun da za su tabbatar da bahasin da suka yi.

  10. An zargi Shakira da kauce wa biyan haraji a karo na biyu

    Gwamnatin Sifaniya ta tuhumi tauraruwar kade-kaden pop 'yar kasar Columbia, Shakira da kaucewa biyan haraji a karo na biyu.

    Masu shigar da kara a Sifaniya sun yi zargin cewa mawakiyar ta damfari kasar yuro miliyan 6.7 a shekara ta 2018.

    Sun ce hakan ta faru ne lokacin da ta gaza bayyana miliyoyin kudin da ta samu a matsayin kafin alkalami daga rangadin raye-rayen da ta yi na El Dorado World, da kuma sauran kudaden da ta samu.

    Masu shigar da kara a Sifaniya sun fara gudanar da bincike a karo na biyu a watan Yulin 2023, amma dai sai a ranar talatar nan suka fitar da karin bayani.

    Tashar talbijin ta Sifaniya RTVE ta ce mawakiyar 'yar shekara 46 tana sane da sabbin tuhume-tuhumen, ammai dai kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa lauyoyin Shakira a Miami - inda take zaune a yanzu - ba a sanar da su ba tukunna.

    Maimakon haka suna "mayar da hankali ne don shiryawa shari'ar shekarun 2012 zuwa 2014, da za a fara ranar 20 ga watan Nuwamba," kamar yadda suka fada wa Reuters a wata sanarwa.

  11. Kenya za ta fara gina tashar makamashin nukiliya a 2027

    Kenya za ta fara gina wata tashar makamashin nukiliya a shekara ta 2027, hukumomin kasar ne suka bayyana hakan a wani alkawari na baya-bayan nan game da shirin.

    Tashar mai karfin megawat 1,000, ta shafe tsawon shekaru ana shirin kafa ta, a wani bangare na burin da kasar take da shi na komawa amfani da makamashi mai tsafta da bunkasa samar da makamashi.

    A baya, an fitar da irin wannan sanarwa game da yiiwuwar fara aikin gina tashar.

    Shugaban riko na Hukumar Samar da Makamashi da Nukiliya, Justus Wabuyabo ya fada wa jaridar Business Daily ta kasar Kenya cewa hukuma a yanzu tana gudanar da kididdiga a wurin da ake sa ran gina tashar da kuma kammala shirye-shirye don bude damar samun aikin gina tashar nukiliyar.

    Justus Wabuyabo ya ce tashar za a gina ta ne yankin gabar ruwan Kenya tsawon sama da shekara shida zuwa goma, inda ake sa ran fara aikace-aikace a shekara ta 2034.

  12. Muhimmiyar tattaunawa tsakanin Saudiyya da Isra'ila na gudana don kulla alaka

    Wani ayarin manyan jami'an Saudiyya yana yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan da ke karkashin mamaya karon farko tun bayan kwace yankin da Isra'ila ta yi daga kasar Jordan a yakin 1967.

    Sa'o'i bayan isar jami'an, ministan yawon bude ido na Isra'ila shi ma ya sauka a Saudiyya, don halartar wani taron Majalisar Dinkin Duniya.

    Haim Katz ya zama ministan Isra'ila na farko da ya jagoranci wani rukunin jami'an kasar zuwa wata ziyara a kasar Saudiyya, kamar yadda ofishinsa ya ce.

    Muhimman ziyarce-ziyarcen na zuwa ne bayan shugabannin Saudiyya da na Isra'ila sun furta kalaman alheri game da kokarin kulla alakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

    Amurka a baya-bayan nan ta shiga tsakani don cimma sasantawa mai sarkakiya tsakanin manyan kawayenta biyu na yankin.

    Wata yarjejeniya tsakanin kasashen mafi karfi a yankin za ta kawo wani sauyin bagtatan a siyasar Gabas ta Tsakiya kuma za ta samar da wata babbar nasara a manufar Amurka ta hulda da kasashen waje.

    A ranar Talata da safe, babban jakadan Saudiyya na farko a yankin Falasdin, Nayef al-Sudairi wanda kuma shi ne jakadan kasar Jordan ya tafi a mota zuwa Gabar Yamma da Kogin Jordan ta mashigar Karama a wata ziyarar kwana biyu.

    Isra'ila ce take iko da mashigin a kan iyaka, kuma sai ta bayar da izini gabanin isarsa. Ma'aikatar harkokin wajen Falasdin ta bayyana lamarin a matsayin "wani muhimmin abin tarihi" a huldar da ke tsakaninsu da gwamnatin Riyadh.

    An yi wa jami'in diflomasiyyar na Saudiyya maraba da kade-kade a Ramallah, inda Hukumar Falasdin take da shalkwata.

    A fadar shugaban, Nayef a-Sudairi ya duba faretin ban girma daga dakarun da suka jeru a layi don gaishe shi, yayin da aka buga taken kasar Saudiyya da na al'ummar Falasdin.

    Daga nan sai ya mika takardun kama aikin jakadanci ga Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas yayin wani biki. Da yake jawabi ga manema labarai,

    Mallam Sudairi ya yi kokarin jaddada tabbaci ga al'ummar Falsdinawa a kan duk wani ci gaba. Ya buga misali da wata hirar da ba-sabon-ba da Yarima Mai jiran Gado Mohammed bin Salman ya yi da tashar talbijin ta Fox News.

    Yarima Mohammed ya ce "kullum muna kara kusantar" cimma yarjejeniya don daidaita alaka tsakanin kasarsa da Isra'ila, inda ya kara da cewa batun al'ummar Falasdin har yanzu yana da "matukar muhimmanci" a wani bangare na tattaunawa.

    • Majalisar Ɗinkin Duniya ta nemi jin matsayin kotun duniya kan mamayen Isra'ila a Falasɗinu
  13. Labarai da dumi-dumi, 'Yan kwadago sun sanar da shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a Najeriya

    Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun ba da sanarwar shiga yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Talata 3 ga watan Oktoba a fadin kasar.

    Kungiyoyin NLC da TUC sun bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka kira da yammacin ranar Talata a babban birnin kasar, Abuja.

    Sun bukaci rassansu na jihohi su harhado kan 'yan kwadago da sauran jama'a don gudanar da jerin zanga-zanga da maci a fadin Najeriya.

    Kafofin labarai a Najeriya na cewa sun fahimci cewa shugabannin kungiyoyin kwadagon biyu sun warware bambance-bambancen da suka sanya kungiyar NLC shiga wani yajin aikin gargadi tsawon kwana biyu, ba tare da takwararsu ta TUC ba.

    NLC ta kaurace wa aiki a ranakun 5 da kuma 6 ga watan Satumba da muke ciki don matsa lamba ga gwamnatin kasar a kan ta shawo kan wahalhalun da 'yan Najeriya, musamman ma'aikata ke ciki, sakamakon cire tallafin man fetur.

    A cewar sanarwar da sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja ya fitar, kungiyoyin na gudanar da taron ne ta intanet.

    A lokaci guda kuma, ministan kwadago, Mista Simon Lalong ya roki shugabannin NLC su dakatar da shirinsu na tafiya yajin aikin, inda ya ba su tabbacin cewa gwamnati na nan a kan kudurin magance damuwar da suka bijiro da ita.

    Ministan - kamar yadda tashar Channels TV ta ruwaito - ya kuma nunar da cewa daya daga cikin manyan bukatun NLC a taron da suka yi na baya, tuni an cimma ta, inda ta ba da umarnin sakin shugaban kungiyar ma'aikatan sufurin mota a kasar.

    • Kalaman 'yan Najeriya bayan sake ƙara kuɗin man fetur
  14. Ma'aikata na ɗaukar hutun rashin lafiya fiye da kowane lokaci cikin shekara 10

    Binciken Cibiyar kula da ma'aikata da ci gaba (CIPD) ya nuna cewa ma'aikata a Birtaniya suna daukan hutun rashin lafiya daga wajen ayyukansu a wanna shekarar, fiye da yadda suke yi a cikin shekaru goma da suka gabata.

    Cibiyar ta ƙara da cewa ma'aikata suna daukar hutun rashin lafiya aƙalla kwana 7 zuwa 8 a cikin shekarar da ta gabata, daga kwanaki 5 zuwa 8 kafin barkewar cutar korona.

    Ana danganta karuwar rashin lafiya da abubuwa kamar damuwa da ci gaba da kasancewar cutar korona da kuma rikicin tsadar rayuwa.

    Wannan yanayin yana haifar da damuwa kuma yana tasiri sosai ga jin daɗin mutane.

    Binciken ya kuma yi nazarin addadin ma'aikatan da ba sa zuwa aiki sakamakon rashin lafiya a ma'aikatu sama da 900 da cewa za su kai ma'aikata miliyan 6.5.

    Binciken, wanda kamfanin kiwon lafiya na Simplyhealth ya gudanar, ya nuna cewa ƙananan cututtuka su ne babban dalilin da ke haifar da matsalar, yayin da wasu rashe-rashen lafiyar suka biyo baya, sai kuma matsalar kwakwalwa.

    • 'Yan Najeriya na cikin ƙarin hatsarin kamuwa da mashaƙo - Rahoto
    • Masana sun samo hanyar gano kansar mafitsara cikin sauri
  15. An kashe tsuntsayen jan-baki miliyan biyar a Tanzaniya

    Hukumomin Tanzaniya sun bayar da rahoton samun nasarar kashe sama da tsuntsayen jan-baki miliyan biyar.

    Tsuntsayen sun mamaye gonakin shinkafa sama da eka 1,000 a yankin Manyara, wanda ya haifar da gagarumar asarar kayan amfanin gona.

    Ta hanyar amfani da jirage marasa matuki, jami’ai sun kwashe tsawon kwanaki hudu suna fesa wa tsuntsayen wasu sinadaran magani don magance matsalar.

    Tsuntsayen za su iya cinye fiye da tan 50 na kayan amfanin gona a kullum, kamar yadda Gadman Mbuko daga Hukumar Kula da Lafiyar Tsirrai da Magungunan ƙwari ta Tanzaniya ta lura.

    Tsuntsayen jan-baki, daya daga cikin nau'in tsuntsayen da suka fi yawa a duniya, sukan lalata kayan amfanin gona kamar shinkafa da alkama.

    A cikin shekarar 2021, Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta kiyasta asarar kayan amfanin gona na kusan dala miliyan 50 a kowace shekara, musamman a yankin kudu da hamadar Sahara, sakamakon wadannan tsuntsaye.

    • Yadda tsuntsaye ke cinye wa manoman Kenya amfanin gona
    • “Ƴan bindiga na ƙona mana amfanin gona idan ba mu ba su kuɗi ba”
  16. Wutar lantarki ta kashe mutum takwas a inda aka yi ambaliya

    Mutum takwas ne wutar lantarki ta hallaka yayin da kuma aka kwashe wasu daruruwa daga gidajensu bayan iska mai karfi da ruwan sama kamar da bakin kwarya a lardin Western Cape na Afirka ta Kudu sun haifar da ambaliyar ruwa.

    An kuma kwashe mazauna wani kauye da ke yankin.

    Zabtarewar kasa da fadowar duwatsu sun tilasta rufe wasu manyan titunan da ke shiga birnin Cape Town.

    Ruwan sama mai yawa da aka ci gaba da yi har zuwa daren jiya ne ya yi sanadiyyar ambaliyar koguna da dama wanda ya lalata kayayyakin more rayuwa da kuma katsewar wutar lantarki.

    Hukumomi sun ce sama da gidaje dubu daya ne ambaliyar ta mamaye a yankunan da suka hada da Houtbay da Bo-Kaap da Belville South da Macassar da Strand da kuma Gordon’s Bay.

    Makarantu 152 ne a rahotanni daban-daban suka lalace.

    • NEMA ta yi Gargadin fuskantar ambaliyar ruwa a Najeriya
    • Wutar lantarki ta kashe mutum 10 a Zaria
  17. Ƴan sanda sun gargadi masu ɗaukar doka a hannu kan waɗanda ake zargi da satar al'aura

    Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Babban birnin tarayya ta gargaɗi mazauna yankin kan ɗaukar doka a hannu kan waɗanda ake zargi da aikata laifuka, domin gudun tayar da zauna tsaye.

    A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun jami'arta ta yaɗa labaru da hulɗa da jama'a, SP Josephine Adeh, ta ce ta yi gargaɗin ne bayan yunƙurin da wasu mutane suka yi na hukunta wani mutum da aka zarga da satar al'aura a yankin Karshi na babban birnin tarayyar.

    Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata, inda wasu maza uku suka ce sun ji wani yanayi da ba su gane ba a al'aurarsu bayan haɗa jiki da mutumin.

    Bayan hakan ne dandazon mutane suka far wa wanda ake zargin, sai dai jami'an ƴan sanda sun ceci shi sa'ar da suka isa wurin, jim kaɗan bayan bayan fara ɗaukar matakin.

    Dalilin haka ne kwamishinan ƴan sanda na yankin birnin tarayyar, CP Haruna G. Garba ya buƙaci jama'a da su guji ɗaukar irin wannan mataki.

    A cikin kwanakin nan an riƙa yaɗa labaru, waɗanda ba a tantance ba kan ɓullar mutane masu satar al'aura bayan haɗa jiki ko kuma shan hannu da al'umma.

    • Najeriya: Yadda 'yan sanda ke kama makusantan masu laifi su tsare
    • Yadda ake kashe masu laifi a ɓoye a Saudiyya tare da barin iyalansu cikin duhu
  18. Gwamnatin Kamaru za ta hukunta masu yaɗa jita-jitar juyin mulki

    Ministan sadarwa na ƙasar Kamaru, Rene Emmanuel Sadi, ya yi gargadi game da raɗe-raɗin da ake yi cewa kasar na iya fuskantar juyin mulki, a daidai lokacin da ake fama da matsalar a ƙasashen Afirka waɗanda Faransa ta yi wa mulkin mallaka.

    A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnatin kasar ya fitar, ya bayyana Kamaru a matsayin ƙasa ta masu bin doka tare da barazanar kamawa da hukunta masu hasashen juyin mulki a ƙasar.

    "Saboda haka gwamnati ta buƙaci mutane da su yi taka-tsan-tsan don kada su yaɗa jita-jitar juyin mulki da kuma hasashen makomar Kamaru, lamarin da zai iya tayar da zaune tsaye a ƙasar" in ji shi.

    Tun bayan da sojoji a Gabon suka kwace mulki daga hannun Ali Bongo a ranar 30 ga watan Agusta, masu sharhi kan shafukan sada zumunta ke ci gaba da ƙara nuna yiwuwar juyin mulki a makwabciyarta, kasar Kamaru.

    Shugaba Paul Biya mai shekaru 90 wanda ya tsallake rijiya da baya a yunƙurin juyin mulki a ƙasar a shekarar 1984 ya shafe shekaru 41 yana mulkin Kamaru.

    Magoya bayansa na neman ya sake tsayawa takara a zaben 2025.

    • Ƙasashen da aka samu dawowar juyin mulki baya-bayan nan a Afirka
    • Juyin mulkin Mali: Shugabannin kasashen Afirka biyar da aka kora daga mulki
  19. An zartar da hukuncin kisa ga mutum huɗu a Iran kan raba wa mutane barasa

    Kafofin yada labaran ƙasar Iran sun ce an zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane huɗu bayan da mutum goma sha bakwai suka mutu sannan wasu kimanin 200 suka makance sakamakon shan gurɓatacciyar barasa.

    An samu mutanen hudu da laifin haɗawa da kuma raba barasa mai illa a lardin Alborz da ke arewacin kasar.

    Hakazalika an kama wasu mutum hudu a cikin watan Yuni bisa wani laifi makamancin wannan.

    Shan barasa dai haramun ne a Iran wanda hakan ya haifar da yawaitar sayar da su a ɓoye.

    • Jerin mutanen da ke jira a aiwatar musu da hukuncin kisa a Iran
    • An gurfanar da mutum 1,000 a kotu kan zanga-zangar Iran
  20. Gwamnatin Najeriya ta bayar da hutu domin bikin Maulidi

    Gwamnatin Najerya ta ayyana ranar Laraba, 27 ga Satumban 2023 a matsayin ranar hutu domin bikin Maulidi, wato zagayowar ranar haihuwar annabi Muhammad (SAW), kamar yadda ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana.

    Yayin da yake bayyana hakan a Abuja, ya taya daukacin al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar.

    "Shawarar sa ga ƴan Najeriya ita ce su tsarkake zuciya tare da nuna soyayya da hakuri da juriya wadanda su ne kyawawan dabi'un da annabi Muhammad (SAW) ya nuna," in ji babban sakataren ma'aikatar, Oluwatoyin Akinlade a cikin wata sanarwa.

    “Mai girma Minista ya bukaci ‘yan Najeriya musamman matasa da su rungumi dabi’ar aiki tukuru da kuma zaman lafiya da juna, ba tare da la’akari da addini da aƙida ko kuma kabilanci ba."

    • Falalar bikin Maulidin manzon Allah
    • Eid Maulud: Muhimman abubuwan da ake so Musulmi ya yi a ranar Maulidi