Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Tinubu ya naɗa Jamila Bio Ibrahim ministar matasa

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Buhari Muhammad Fagge

  1. Mu kwana lafiya

    Nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotannin namu na yau.

    Muhammad Buhari Fagge ke fatan mu kwana lafiya daga nan BBC.

  2. Mene ne gaskiyar batun juyin mulki a Congo Brazzaville

    Gwamnatin Jamhuriyar Congo ta musanta labaran da ta kira na "Ƙanzon kurege" a kafafen sada zumunta wanda suke cewa an yi Juyin mulki a ƙasar. Wasu labarai marasa tushen sun ce ana shirin gudanar da wani abu a Brazzaville.

    Gwamnati ta musanta waɗannan labarai. "Muna tabbatarwa da mutane babu wani abun tashin hankali kuma muna ba su shawarar kowa ya koma ya ci gaba da harkokinsa na yau da gobe," kamar yadda kakakin gwamnati Thierry Moungala ya wallafa a shafin X da a baya aka fi sani da Twitter.

    Juyin mulki a yankin Yammacin Afrika na neman zama ruwan dare a 'yan shekarun nan.

    Sojoji ne ke shugabantar ƙasashen Mali da Burkina Faso da Guinea da Nijar da kuma Gabon, suna kafa hujja da cewa shugabannin da suka hamɓarar sun gaza kawo ƙarshen matsalar tsaro musamman a ƙasashen yankin Sahel.

    Congo Brazzaville ba ta cikin yankin Sahel, inda barazanar masu jihadi iƙirarin jihadi ta zama jiki, kuma wataƙila wannan raɗe-raɗin ya samo asali ne saboda daɗewar shugaban ƙasar na yanzu a kan mulki, ina ya jagoranci ƙasar a tsakanin shekarar 1979 zuwa 1992 sai kuma ya ci gaba daga 1997 har ya zuwa yanzu.

    Ana sa ran Shugaba Denis Sassou-Nguesso zai halarci taron MDD na 78 wanda za a yi a Amurka daga ranar 18 zuwa 19 ga watan Satumba.

  3. Ana duba yiwuwar ƙarawa ma'aikatan jirgin ƙasa albashi a Najeriya

    Ministan sufuri na Najeriya Sanata Sa'idu Alƙali, za a bai wa umarnin shugaban ƙasa muhimmanci na amincewa da ya yi a duba yiwuwar ƙarawa ma'aikatan jirgin ƙasa albashi.

    Ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen bunƙasa jindadin ma'aikatar jiragen ƙasa na Najeriya, sannan a kyautata yanayin aikinsu.

    Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai hedikwatar hukumar da ke Ebute-Meta a Legas.

    A cewarsa wannan wata ziyara ce domin ganin yadda ayyukan hukumar suke gudana da kuma nisan da aka yi a ayyukan da take kan yi, yana buga misali da aikin dogo na Legas zuwa Ibadan da na Kano zuwa Maraɗi.

  4. 'Ambaliyar Libya ta lalata kusan kashi ɗaya bisa huɗu na gine-gine a birnin Derna'

    Gwamnatin Libya da MDD ta amince da ita, ta ce ambaliya ta lahanta kusan kashi ɗaya bisa huɗu na gine gine a Derna.

    Kusan gine gine 900 a birnin suka lalace.

    Akwai dubban mutane da suka salwanta ba a gani ba, yayin da jami'an agaji ke ci gaba da kokarin gano gawawwaki.

    An samu isar da kayan agaji inda za a mayar da hankali wajen taimakawa wadanda suka tsira da abinci da ruwan shada da kuma matsuguni.

    Wakilin BBC a Derna ya ce akwai bukatar babban taimako diba girman ɓarnar da ambaliyar ta yi

  5. Rasha ta ce Ukraine ta kai hari yankin Crimea

    Rasha ta ce ta daƙile wani harin jirgi da Ukraine ta yi ƙoƙarin kai wa yankin Crimea a safiyar Lahadi, yayin da jirage marasa matuƙa ke kai hari Moscow da tayar da hankalin babban birnin suka kuma cinna wuta a defo ɗin ta da ke kudanci - a yammacin ƙasar.

    A ƴan kwanakin nan, Ukraine ta kaddamar da jerin hare-hare kan sansanonin sojan Rasha da ke yankin Crimea da aka yi wa ƙawanya.

    Cikin sansanonin da aka kai wa hari, har da wanda ke Tekun Bahar Rum, inda take ƙoƙarin dakushe nasarar da Rasha ke samu.

  6. Shugabar HukumarTarayyar Turai ta ziyarci Italiya kan matsalar 'yan cirani

    Shugabar Tarayyar Turai Urusla von der Leyen ta kai ziyara cibiyar 'yan cirani da ke tsuburin Lampedusa a Italiya, bayan firaiministan ƙasar ya nemi taimakon Tarayyar game da 'yan ciranin da ke isa yankin a kwale-kwale.

    Sama da 'yan cirani 8,000 ne suka isa tsuburin a cikin kwana uku da suka gabata.

    Firaiminista Giogia Meloni ta ce Italiya na fuskantar matsin lambar da ba za ta iya jura ba.

    Von der Leyen ta ce "Matsalar ta Turai ce don haka ana buƙatar Tarayyar Turai ta yi wani abu a kai".

    A yayin wani taron manema labarai ta yaba wa mutanen Lampedusa kan taimakon da suke bai wa 'yan ciranin, waɗanda ta ce "suna zuwa tsuburin ne domin sauƙin isa".

    Ta kuma yi alƙawarin ninkaƙoƙarin da suke yi game da yadda ake safarar mutane da kuma waɗanda ke tafiyar cirani mai cike da haɗari.

  7. Mutum biyar sun mutu 12 sun jikkata a wani haɗarin mota a Najeriya

    Akalla mutane biyar ne aka tabbatar sun mutu bayan wani taho mu gama da wata motar ɗaukar da wata babbar mota kan babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa kakakin Hukumar Kare Haɗura ta ƙasar a jihar Ogun, Florence Okpe ce ta tabbatar da faruwar lamarin lokacin da take zantawa da manema labarai a Abeokuta babban birnin jihar.

    Okpe ta ce haɗarin ya faru ne a safiyar ranar Lahadi da misalin ƙarfe 6 na safe.

    Ta ce motar ɗaukar kayan ta samu matsala ne lokacin da ɗaya daga cikin tayoyinta ta fashe saboda gudun da take yi na wuce sa'a, wanda daga baya haifar da mummunan haɗari.

    Ta ce mutum 21 abin ya rutsa da su, fasinjoji biyar sun mutu yayin da wasu 12 na daban suka jikkata.

    Ta kuma ƙara da cewa waɗanda suka raunatan an garzaya da su asibiti da ke kusa domin duba lafiyarsu.

  8. Karon farko cikin sama da shekara Greenwood ya buga wa Getafe wasa

    Mason Greenwood ya koma buga wasa a babbar ƙungiyar ƙwallon kafa bayan share sama da 20 yana fuskantar zargi.

    Tsohon ɗan wasan Manchester United ya shiga wasan da Getafe ta doke Osasuna da ci 3-2 ne a matsayin canji.

    Rabon da ɗan wasan ya buga wasa tun watan Janairun 2022, lokacin da aka kama shi ana zarginsa kan wasu bayanansa da aka wallafa a intanet.

    An tuhume sa da aikata fyaɗe da cin zarafi, sai dai an wanke shi kan hakan a watan Fabirairun 2023.

    Ya sanya hannu kan tafiya Getafe a matsayin ɗan wasan aro bayan fuskantar bincike na wata shida a United, inda Greenwood da Ƙungiyarsa suka maince ya ci gaba da taka leda a wani wajen maimakon Old Trafford.

  9. Tinubu ya tafi Amurka taron MDD

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tafi Amurka domin halartar Babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 da za a gudanar a birnin New York.

    Wannan ne karon farko da Tinubu zai halarci taron a matsayin shugaban ƙasa.

    Cikin sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar, ta ce Tinubu zai gabatar da jawabi a zauren ranar Talata 19 ga watan Satumba.

    Zai kuma gana da manyan shugabanni domin tattauna batutuwan da suka shafi muradun ƙarni da batun sauyin yanayi, da ayyukan jin-ƙai a fadin duniya.

    Shugaba Tinubu zai kuma gana da shugabannin ƙasashen duniya, ciki har da shugaban hukumar gudanarwar tarayyar Turai, da shugaban Brazil da na Afirka ta Kudu, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

  10. Taliban za ta yi aiki da wani kamfanin Turkiyya don aikin gina madatsar ruwa

    Gwamnatin Taliban da ke Afghanistan ta ƙulla yarjejeniya da wani kamfanin Turkiyya don kammala aikin gina madatsar ruwa a lardin Helmand.

    Kafar yaɗa labaran Afghanistan RTA ta ruwaito cewa jami'ai daga ma'aikatar makashi da ruwan sha na Afghanistan za haɗa hannu da jami'an kamfanin '77 construction' wajen gudanar da aikin.

    "Ma'aikatar makamashi da ta ruwan sha sun tsara gudanar da manyan ayyuka 411 a cikin shekara guda, kuma tuni an fara wasu daga ciki, yayin da za a ƙaddamar da sauran idan aka samu kudin gudanarwa", in ji Abed.

    Masu sharhi na kallon wannan aiki a matsayin damar samun ayyukan yi tare da bunƙasa masana'antu da haɓaka fannin noma a ƙasar.

  11. Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu

    Haruna Shehu Tangaza tare da Aisha Sharif Bappa ne, suka gabatar da shirin na wannan mako

  12. Tinubu ya naɗa Jamila Bio Ibrahim ministar matasa

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da naɗin Dakta Jamila Bio Ibrahim a matsayin babbar ministar matasa a ƙasar.

    Haka kuma Tinubu ya amince da naɗin Mr. Ayodele Olawande a matsayin ƙaramin ministan matasa.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce za a tura sunayen mutanen biyu zuwa majalisar dattawan ƙasar domin tantance su.

    Dakta Jamila Bio Ibrahim - matashiyar likita - a baya-bayan nan ta riƙe muƙamin shugabar mata ta matasan jam'iyyar APC mai mulki.

    Ta kuma riƙe muƙamin babbar mai taimaka wa gwamnan Kwara kan cimma muradun ƙarni.

    Shi kuwa Mista Ayodele Olawande shi ne shugaban matasa na jam'iyyar APC.

    A baya-bayan nan ya yi aiki a ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin ƙirƙire-ƙirƙire daga 2019 zuwa 2023.

  13. Najeriya ta ƙulla yarjejeniya da Cuba don samar da abinci

    Gwamnatin Najeriya ta ƙulla yarjejeniya da ƙasar Cuba don samar da abinci da fasahar ci gaban harkokin noma.

    Ministan albarkatun noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ne ya sanya hannu a madadin gwamnatin Najeriya a lokacin taron ƙungiyar ƙasashen G-77 ta ƙasashe masu tasowa da ka gudana a birnin Havana na ƙasar Cuba.

    Cikin saƙon X da mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima - wanda ke wakiltar shugaban ƙasar a taron - ya wallafa ya ce, yarjejeniyar za ta ƙarfafa dangantakar harkokin noma tsakanin ƙasashen biyu.

    Sanata Abubakar Kyari ya yaba wa gwamnatin Cuba kan ƙulla yarjejeniyar, yana mai cewa duka ƙasashen biyu na da buri iri ɗaya kan al'umominsu.

    Ministan ya nuna jin daɗinsa kan wannan yarjejeniya da ya ce za ta taimaka wajen magance tarin matsalolin da Najeriya ke fuskanta a ɓangaren abinci da harkokin noma.

    Ya ce Najeriya a shirye take ta haɗa hanu da Cuba a ɓangarorin kiwon kaji da na manyan dabbobi da kiwon kifi.

    Ɓangarorin da yarjejeniyar za ta mayar da hankali sun haɗar da batun samar da magungunan dabbobi, da samar da riga-kafin dabbobi da yi wa dabbobi baye da sauran fannoni.

  14. Taliban ta kama malamin Qur'ani kan zargin zane almajirinsa

    Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta kama wani malamin makarantar haddar Alqur'ani a lardin Faryab bisa zargin zane almajirinsa.

    Cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta a makon da ya gabata, an ga wani mutum da ake zargin malamin ne, na zane wani almajirin da ke haddar Alqur'ani.

    Babban jami'in ma'aikatar yaɗa labaran Taliban, Shamsuddin Mohammadi ya shaida wa cewa gwamnatin Taliban ta kama malamin, ana kuma gudanar da bincike kan batun.

    Kafar yaɗa labari ta TOLO da ke birnin Kabul ta ce almajirin ɗan asalin ƙauyen Koh Sayad ne daga gundumar Shirin Tagab a lardin na Faryab.

  15. Shin kun san me ake nufi da agogon GMT?

    Ibrahim Yusuf Muhammad ne ya gabatar da shirin na wannan mako

  16. Nijar da Mali da Burkina Faso sun kafa sabuwar ƙungiya

    Ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso sun ƙaddamar da sabuwar ƙungiyar ƙawancen sojin ƙasashen yankin Sahel.

    Ƙasashen sun amince da kafa ƙungiyar 'Alliance of States of the Sahel' (AES) wato 'Ƙawancen ƙasashen yankin Sahel', bayan wani taro da suka gudanar a birnin Bamako na ƙasar Mali.

    Taron - wanda ya samu halartar shugaban gwamnatin mulkin sojin Mali Kanal Assimi Goita, da ministocin ƙasashen wajen Mali da Burkina Faso da mai magana da yawun gwamnatin mulkin sojin Nijar - ya amince da kafa ƙungiyar don kare ƙasashen yankin Sahel.

    Manufar kafa ƙungiyar ita ce samar da tsaron 'haɗin gwiwa' tsakanin ƙasashen uku, ta hanyar yin aiki tare domin yaƙar 'ta'addanci' da 'yan tawaye a cikin ƙasashen uku.

    Haka kuma ƙungiyar ta amince da kai wa juna agaji idan ta samu farmaki daga waje.

    “Duk wani hari da aka kai wa ɗaya daga cikin ƙasashen ƙungiyar , AES za ta ɗauke shi ne tamkar hari a kan duka mambobinta, don haka za ta ɗauki matakin ramuwar gayya, a ƙungiyance ko daban-daban, ciki har da amfani da ƙarfin soji domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasashe mambobin ƙungiyar," kamar yadda yarjejeniyar ta nuna.

    Ana kallon kafa wannan ƙawance tamkar martanin ƙasashen uku ne, kan barazanar da Ecowas ke yi na amfani da ƙarfin soji, don mayar da Nijar kan tafarkin dimokraɗiyya bayan da sojojin ƙasar suka kifar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Mohamed bazoum cikin watan Yuli.

  17. Hatsarin jirgin sama ya kashe mutum 14 a Brazil

    Mutum 14 ne suka mutu sakamakon faduwar jrgin sama a yankin Amazon na Brazil. Karamin jirgin na kan hanyar zuwa Manaus na jihar Amazona, ya kuma fado sakamakon ruwan sama mai karfin gaske, daidai lokacin da ya fara ketara sararin Barcelos.

    Dukkan fasinjoji 12 da ma'aikata 2 sun rasu, wanda yawanci 'yan yawon bude ido ne da ke hanyar zuwa wasan kamun kifi.

    Barcelos dai fitaccen yanki ne da ke daukar hankalin 'yan yawon bude ido, wanda ke kusa da wurare masu ƙayatarwa da ban sha'awa.

  18. 'Yan Ci-rani: EU za ta yi nazari kan tsuburin Lampedusa

    Nan gaba a yau ake sa ran shugabar hukumar gudanarwar tarayyar turai Ursula von der Leyen, za ta kai ziyara tsibirin Lampedusa na Italiya.

    Hukumomi a tsuburin Lampedusa sun ce , 'yan cirani 160 ne suka isa wurin cikin kananan kwale-kwale 4, ana kuma sa ran wasu karin jiragen biyu na kan hanya ɗauke da mutum 80.

    Nisan kilomita 150 ne tsakanin ɗan karamin tsibirin na Lampedusa da ƙasar Tunusia.

    Tsuburin ya kasance hanyar da 'yan cirani daga yankin Afirka da Asiya ke amfani da ita domin isa Turai.

    Firai ministar Italiya Geogia Meloni ce ta yi kiran a kawo wa ƙasar dauki.

  19. Saudiyya da Kuwait sun aike da kayan agaji zuwa Libya

    Jiragen ruwa maƙare da kayan agaji daga ƙasashen Saudiyya da Kuwait da Italiya sun isa tashar ruwan birnin Derna na Libya.

    Jiragen dai shake suke da Tantuna, da barguna da kayan abinci, da ruwan sha mai tsafta.

    Hukumar lafiya ta duniya WHO ma ta ce tuni magungunan da ta aika suka isa birnin, da ambaliyar ruwa ya ɗaiɗaita a makon da ya wuce.

    Inda madatsun ruwa da dama suka ɓalle.

    Sama da mutum 12,000 suka mutu a mummunar ambaliyar ɗauke da ruwan sama da guguwa, yayin da kawo yanzu ba a san inda sama da mutum 10,000 suke ba.

  20. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a fadin duniya.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.