Gwamnatin Najeriya ta bayyana alhini a kan mutuwar mutumin da ya zana tutar Najeriya, Pa Taiwo Akinkunmi, wanda ya rasu bayan gajeriyar jinya a gidansa da ke birnin Ibadan.
Wata sanarwa da ministan yaɗa labarai da wayar da kai, Alhaji Mohammed Idris ya fitar ta bayyana marigayin a matsayin wani jigon ƙasa, wanda ba za a iya kankare gudunmawar da ya bayar ga haɗin kan Najeriya daga zukatan al'umma ba.
Tutar Najeriya, kamar yadda ministan ya bayyana, tana ɗaya daga cikin tambarin ƙasar masu daraja, kuma wata kadara ce da Pa Akinwunmi ya rubuta sunansa da ita a cikin kundin tarihin Najeriya.
Taiwo Akinkunmi, wanda ya zana tutar Najeriya, ya rasu yana da shekara 87.
Ɗaya daga cikin 'ya'yansa Akinkunmi Akinwumi ne ya sanar da rasuwar tasa a wani saƙon Facebook a yau Laraba.
"Duk mai rai tabbas mamaci ne, zan iya cewa ka yi rayuwa mai cike da tasiri. Ka huta mahaifina Pa Michael Taiwo Akinwunmi," in ji shi.
Rahotanni sun ce Akinkunmi ya rasu ranar Talata da tsakar dare.