Sai da safe
Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi.
Mu haɗu da ku gobe don samun wasu sababbi.
Umar Mikail ke muku fatan alheri.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail
Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi.
Mu haɗu da ku gobe don samun wasu sababbi.
Umar Mikail ke muku fatan alheri.
Gwamnatin sojin Nijar ta ce ta bai wa sojojin ƙasar umarnin su kasance cikin babban shiri saboda barazanar hare-hare da ke ƙaruwa.
A cewar wasu majiyoyin tsaro, babban hafsan sojin kasar ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a a wasu bayanan gwamnati da ba a sanar wa jama'a ba.
A watan da ya gabata ne sojoji suka hamɓarar da gwamnatin Mohamed Bazoum, kuma tun lokacin ƙungiyar ƙasashen Afrika ke ƙoƙarin bin hanyoyin sasantawa ta laluma.
Ƙungiyar ta yammacin Afrika ta yi barazanar amfani da karfi idan har ba ba a mayar da zaɓaɓɓen shugaban kasar kan mulki ba.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa sojojin mulkin Nijar sun kori jakadanta Mohammed Sani Usman daga ƙasarsu.
Wata sanarwa daga ma'aikatar ta ce rahotannin da ake yaɗawa cewa a ranar Juma'a sojojin suka bai wa jakadan wa'adin awa 48 ya fice daga ƙasar ba gaskiya ba ne.
"Ma'aikatar Harkokin Waje na tabbatar wa da jama'a cewa wannan labari ƙarya ne kuma ya kamata su yi watsi da shi," in ji sanawar da ta fitar a yammacin yau Asabar.
An yi ta yaɗa labaran ƙarya game da korar jakadu daga Nijar, ciki har da wanda sojojin suka musanta na korar jakadiyar Amurka.
Alaƙar Nijar da wasu ƙasashe ta lalace ne tun bayan da sojojin suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum ta farar hula a watan Yuli kuma Janar Abdourahmane Tchiani ya ayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa.
Ranar 26 ga watan kowane Agusta - irin ta yau ke nan - ne aka ware domin bikin Ranar Hausa.
Albarkacin wannan rana, mun tattauna da matashi Sadar Musa, wanda ya ƙirƙiri baƙaƙe da wasula na Hasua 37 sababbi fil.
Mazaunin unguwar Dala a birnin Kano na arewacin Najeriya, Sadar ɗalibin Hausa ne a Buɗaɗɗiyar Jami'a ta Ƙasa (National Open University) a Najeriya.
Baki dayan masu horar da tawagar kwallon kafa ta mata ta Sifaniya da suka je gasar kofin duniya sun yi murabus in ban da babban koci, Jorge Vilda.
Hakan ya biyo bayan takaddamar da ta bullo, bayan da shugaban hukumar kwallon kafar kasar, Luis Rubiales ya sunbaci 'yar wasa, Jenni Hermoso.
Sifaniya ta ci Ingila 1-0 ta lashe kofin duniya na mata ranar Lahadi a gasar da aka yi a Australia da New Zealand.
Mataimakin koci, Montse Tome da Javier Lerga da Eugenio Gonzalo Martin da mai kula da lafiyar 'yan wasa, Blanca Romero Moraleda da mai horar da masu tsaron raga, Carlos Sanchez, duk sun bar aikin.
Haka kuma wasu da suka shafi tawagar ta mata ta Sifaniya da suka shafi shekaru da ban da ban suma sun ajiye aikin.
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya ce zai raba wa matasan da ke yi wa ƙasa hidima a jihar su 1,215 tallafin 30,000 kowanensu domin rage raɗaɗi.
Zulum ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci sansanin horar da masu yi wa ƙasar hidima ranar Asabar a Maiduguri, inda ya ce zai ware naira miliyan 36.4 domin bai wa matasan tallafin.
Haka kuma gwamnan ya bai wa masu yi wa ƙasar hidima buhun shinkafa 100 da na wake 10 da jarkar man girki 10 domin yi wa matasan abinci a lokacin da suke karɓar horon na mako uku
“Ina son faɗaɗa rabon tallafin rage raɗadi ga masu yi wa ƙasarmu hidima da ke jiharmu. kowane mutum guda a cikinsu zai samu naira 30,000, za kuma a tura muku kudin ne ta asusun ajiyarku na banki", in ji Zulum.
Ya kuma buƙaci matasan da su yi biyayya ga dokokin sansanin wajen zama lafiya tare da aiwatar da duka ayyukan da suka wajaba a kansu, domin ciyar da ƙasarsu gaba.
Gwamnan ya kuma bayyana jin dadinsa ga gwamnatin tarayyar ƙasar wadda ta inganta tsaron jihar domin bayar da dama da matasan domin su yi hidimar ƙasa a jihar.
An dai kwashe shekaru masu yawa ba tare da horar da masu yi wa ƙasaa hidima ajihar ba, sakamakon hare-haren ƙungiyar Boko Haram.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya Fifa ta dakatar da Luis Rubiales daga matsayinsa na shugaban hukumar ƙwalon ƙafar Sifaniya kan sumbatar 'yar wasan ƙwallon ƙafar ƙasar.
Fifa ta dakatar da da Mista Rubiales daga shiga harkokin ƙwallon ƙafar a ƙasar da ma matakin duniya baki ɗaya.
Sumbatar Jenni Hermoso da Rubiales ya yi a leɓenta bayan da Sifaniya ta doke Ingila a wasan ƙarshe na Kofin Duniya ya janyo ce-ce-ku-ce mai zafi a duniyar wasannin.
Inda aka riƙa kiraye-kirayen ya sauka daga muƙaminsa sakamakon sumbatar Hermoso.
To sai dai ya ƙi yin murabus yana mai cewa ya aikata hakan ne a cikin murna, dan haka bai ɗauke shi a matsayin wani abu ba.
A ranar Alhamis ne Fifa ta buɗe bincike a hukumance kan Mista Rubiales mai shekarar 46.
Tun da farko dai ya riƙe gabansa a lokacin da ake murnar kammala wasan.
Rubiales ya nemi gafara ranar Litinin kan sumbatar 'yar wasan kafin Fifa ta buɗe bincike a kansa.
A ranar Juma'a ya nemi afuwa kan cewa ya riƙe gabansa ne a lokacin da yake murna a bangaren VIP na filin wasan Sydney, yayin da Sarauniya Letizia ta Sifaniya da 'yarta mai shekara 16 ke tsaye kusa da shi.
Daga farko dai ya nemi kare kansa daga abin da ya aikata, yana mai cewa ya yi ƙoƙarin jajanta wa Hermoso ne bayan golan Ingila Mary Earps ta kama fanaretin da ta buga.
Ministan harkokin sufurin Kenya ya nemi afuwar 'yan ƙasar sakamakon katsewar wutar lantarki a ilahirin faɗin ƙasar, lamarin da ya sa fasinjoji da dama suka maƙale a filin jirgin saman Nairobi.
Gidaje da dama da kasuwanni sun kasance babu wutar lantarki tun bayan da aka ɗauke ta da maraicen ranar Juma'a.
Babban kamfanin samar da wuta na ƙasar bai yi bayanin cikakken abin da ya haifar da ɗaukewar wutar ba.
Mutane a shafukan sada zumunta sun yi ta sukar ma'aikatar makamashin ƙasar, tare kiraye-kirayen cewa me yasa babu injinan samar da wuta a filin jirgin.
Rahotoni na cewa ɗaukewar wutar lantarki na jefi-jefi ko gajeren lokaci ba sabon abu ba ne a ƙasar, to amma irin wannan lamari da ya shafi duka ƙasar abu ne da ba a saba gani ba.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce tabar wiwi ce ƙwayar da aka fi ta'ammali da ita tsakanin miyagun ƙwayoyi a duniya.
WHO ta ce kimanin mutum miliyan 129 zuwa 190 ne ke ta'ammali da tabar wiwi a faɗin duniya.
A cikin shirin namu na wannan makon Habiba Adamu ta duba shaye-shayen ƙwayar tsakanin mata, da kuma irin illar da shaye-shayen ke yi wa mata.
Hukumar Daƙile Cutuka masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ce jami'anta na ci gaba da sanya idanu tare da lura da sabon nau'in ƙwayar cutar EG.5 da BA.2.86 mai haddasa cutar korona.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa hannun babban daraktan hukumar Dakta Ifedayo Adetifa, NCDC ta ce kawo yanzu cutar ba ta ɓulla a Najeriya ba, amma hukumar na ci gaba da sanya idanu.
A ranar 7 ga watan Agusta ne aka bayyana ɓullar ƙwayar cutar EG.5 a ƙasashen duniya 51 ciki har da China da Amurka da Koriya da Japan da Canada da Australiya da Singapore da Birtaniya da Faransa da Portugal.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta gudanar da bincike tare da gwaje-wajen kan ƙwayar cutar, inda ta gano wasu abubuwa masu yawa game da cutar.
WHO ta ce ƙwayar cutar za ta daɗe ba ta nuna wani sauyi ko alama a jikin mai ɗauke da ita ba.
EG.5 na ɗauke da alamomin da masu cutar korona ke nunawa da suka hadar da zazzaɓi mai tsanani da tari katsewar numfashi, da kasala, da ciwon gaɓoɓi, da ciwon kai da na maƙogoro.
Shirin namu na wannan mako ya tattauna da tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya janar Abdussalami Abubakar mai ritaya.
Wanda shi ne jakadan ƙungiyar Ecowas na masamman kan rikicin da ƙungiyar ke yi da sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar.
Cikin makon da ya gabata ne ya jagoranci tawagar Ecowas zuwa Nijar, inda suka tatauna da jagororin juyin mulkin da kuma hamɓararen shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.
Yau ne, ake bikin Ranar Hausa ta Duniya, wadda ake tunawa da ita duk rana irin ta yau, 26 ga watan Agusta.
Albarkacin wannan rana kuma, mun zanta da Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, shahararren malami a Jami'ar Usman Ɗanfodiyo.
Wanda ya yi bayani kan al'adu da asalin Hausawa
Jami'an hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) sun kama wasu matasa 23 bisa zargin zambatar mutane ta intanet da aka fi sani da 'Yahoo" a jihar Sokoto da ke arewacin ƙasar.
Gidan Talbijin na ƙasar NTA ya ambato mai magana da yawun hukumar reshen jihar Sokoto Kamal Ibrahim na cewa sun kama mutanen bayan samun bayan sirri kan ayyukan da suke aikata.
EFCCn ta ce jami'anta sun riƙa lura da bin sawun harkokokin matasan, inda suka gano suna rayuwa fiye da abin da yakamata ace suna samu a sana'o'in da suke iƙirarin gudanarwa.
An dai kama matasan ne da maraicen ranar Juma'a a rukunin gidajen Bafarawa da ke garin Sokoto da rukunin gidajen Kalkalawa da ke yankin Kalkalawa a jihar, inda a yanzu suka hannun hukumar domin ci gaba da gudanar da bincike.
Abubuwan da aka kama matasan da su, sun haɗar da ƙananan kotoci guda biyu da kwamfutoci da injin bayar da hasken lantarki da mayan wayoyin hannu 30.
Hukumar ta ce za ta gabatar da su a gaban kotu da zarar ta kammala gudanar da bincike a kansu.
An buɗe rumfunan zaɓe a ƙasar Gabon mai arzikin man fetur da ke tsakiyar Afirka, in da shugaban ƙasar Ali Bongo - wanda ya fara mulkin ƙasar bayan mutuwar mahaifinsa Omar Bango a shekarar 2009 - ke neman wa'adin mulkin ƙasar karo na uku.
Shugaba Bango na fafatawa da mutum 13 a zaɓen da ake ganin zai zama mai zafi.
Babban ɗan takarar ƙawancen jam'iyyun adawa Albert Ondo Ossa, da ake ganin na kan gaba-gaba a masu ƙalubalantar Bango a zaɓen, ya ce "Gabon ba kadarar iyalan Bango ba ce".
A zaɓukan da suka gabata an samu ƙorafe-ƙorafe kan hanyoyin da ake gudanar da zaɓen.
Jam'iyyun adawa sun yi zargin tafka magudi a zaɓukan na baya.
A wannan karon an yi wasu sauye-sauye a takardun kaɗa ƙuri'ar da suka janyo ce-ce-ku-ce makonni gabanin zaɓen.
A karon farko masu kaɗa ƙuri'a za su yi amfani da takardar ƙada ƙuri'a guda domin zaɓen shugaban ƙasa da ɗan majalisa.
Masu suka na fargabar cewa hakan ka iya zama barazana ga 'yan takara masu zaman kansu, ciki har da Mista Ondo Ossa, babban ɗan takarar ƙawancen jam'iyyun adawa, wanda shi a ƙashin kansa ba shi da jam'iyya.
Amurka ta ce gwamnatin Nijar ta musanta umartar jakadiyar ƙasar ta gaggauta ficewa daga kasar a lokacin da ta kai ziyara Nijar din a kwanakin baya.
Wasu wasiƙu da aka gani a shafin intanet - da wasu jami'an gwamnatin Jamhuriyar Nijar din suka aika wa jakadojin Amurka da Faransa da Jamus da Kuma Najeriya masu alamun ban hakuri ne - suka tabbatar da hakan.
Tun da farko ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta sanar da cewa sojojin - da suka yi juyin a Nijar din cikin watan da ya gabata - ba su da ikon korar jakadanta da ke ƙasar.
Masu bin mu a shafinmu na kai-tseye, Abdullahi Bello Diginza ke fatan kun wayi gari lafiya.
Barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.
Kuna iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.