Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ba mu da niyyar ruguza Nijar - Ecowas

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Haruna Kakangi

  1. Bankwana

    Masu bibbiyarmu a wannan shafin da haka muke bankwana da ku a wannan lokaci, sai kuma gobe Asabar da yardar Allah. A tashi lafiya.

  2. Nan da ƙarshen 2024 matatun mai huɗu na Najeriya za su fara aiki

    Sabon ƙaramin ministan man fetur na Najeriya Heineken Lokpobiri ya ce gwamnatinsu na sa rai matatun man fetur ɗin ƙasar guda huɗu za su koma aiki na da ƙarshen shekara mai zuwa.

    Ya ce matakin zai fara tabbata ne da matatar man fetur ta Fatakwal wadda ake kyautata tsammanin za ta fara aiki a farkon watan Disamban bana.

    A baya dai, gwamnatin Najeriya ta ce matatar mai ta Fatakwal za ta fara tace ɗanyen man fetur a ƙarshen 2022, kuma ministocin man fetur da kamfanin NNPPC sun sanar da shirye-shiryen da ba su yi nasara ba, na sake farfaɗowa da bunƙasa matatun man fetur a ƙasar.

    A farkon wannan mako ne, Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Heineken Lokpobiri a matsayin ƙaramin ministan man fetur, inda a yau Juma'a ya je rangadi na aikin gyare-gyaren da ake ci gaba da yi a matatar man fetur ta Fatakwal mai sashe biyu da ke iya tace ganga 210,000.

    "Daga abin da na gani a nan yau, zuwa ƙarshen shekara, ba shakka matatar mai ta Fatakwal za ta fara aiki," in ji shi, ya ƙara da cewa sauran matatun mai biyu na Warri da Kaduna za su fara tace man fetur ko dai a cikin wata uku na farko da kuma a ƙarshen shekara ta 2024.

    Lokpobiri ya ce "burinmu... shi ne tabbatar da ganin nan da 'yan shekaru ƙalilan, Najeriya za ta daina shigar da man fetur cikin ƙasar."

    Najeriya, ita ce ƙasar da ta fi haƙo man fetur a Afirka, amma kusan duk tataccen man fetur ɗinta tana shigar da shi ne daga ƙetare. Tsawon shekaru da rufe matatun man fetur ɗin guda huɗu mallakar gwamnati, inda gaba ɗayansu suna iya tace ɗanyen mai ganga 4450,000 a kullum.

  3. Sifaniya za ta ɗau matakin shari'a kan mutumin da ya sumbaci 'yar wasa

    Gwamnatin Spaniya ta ce za ta dauki matakin shari kan shugaban hukumar kwallon kafa ta ƙasar bayan da ya ce ba zai sauka daga kan muƙamin sa ba kan sumbatar ƴar wasan ƙwallon ƙasar a wasan cin kofin duniya ta mata.

    Jami'in gwamnatin Victor Francos ya ce za su nemi a dakatar da Luwis Rubayiles.

    An yi tsammanin zai sauka daga muƙaminsa, sai dai ya fito ya fadi ba zai sauka ba saboda abin da ya faru da amincewar yar wasan ya faru.

  4. Roma na nazarin dauko Lukaku daga Chelsea

  5. Mozambique ta ce an kashe ɗan ta'addan da aka fi nema ruwa jallo a ƙasar

    Gwamnatin Mozambique ta ce dakarun ta sun yi nasarar kashe shugaban ƙungiyar masu ikirarin jihadi da ke da alaka da IS da ke yaƙi a arewacin ƙasar.

    Ma'aikatar tsaron ƙasar ta ce shugaban da aka fi sani da Ibn Omar ya jagorancin dukkan yaƙin da ake da masu ikirarin jihadin tun lokacin da aka soma yaƙin a shekarar dubu biyu da goma sha bakwai.

    Sanarwar ta ƙara da cewa an akshe shi ne tare da abokanansa guda biyu.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikin na arewacin Mozambique ya tilasta sama da mutane miliyan barin muhallansu.

  6. An wallafa sunayen mutum 400 da suka mutu a wutar dajin Hawaii

    Hukumomin jihar Hawaii sun wallafa sunayen mutane kusan dubu dari hudu da aka nema aka rasa tun bayan da wutar daji ta mamaye tsibirin Mawi a farkon wannan watan.

    Sun ce suna neman duk wanda ya tsira kuma ya ga sunansa da ya sanar da hukumomi don rage yawan adadin mutanen.

    Mutane dari da sha biyar ne suka rasu sakamakan wutar dajin.

    Yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike a garin Lahaina da sauran yankunan.

  7. West Ham za ta ɗauki Mohammed Kudus daga Ajax

  8. Gwamnatin Borno ta musanta zargin sanya siyasa a rabon tallafin abinci

    Gwamnatin jihar Borno ta musanta zargin da wasu ke yi cewa ana nuna bambancin siyasa a rabon tallafin kayan abinci da take bai wa jama'ar jihar.

    Tallafin kayan abincin dai, wani ɓangare ne na gudunmuwar da Shugaba Bola Tinubu ya bai wa jihohin ƙasar don rage raɗaɗin janye tallafin man fetur.

    Bayan samun tallafin naira biliyan biyar daga gwamnatin tarayya, jihar Borno ƙarƙashin jagorancin Babagana Zulum ta sanar da cewa za ta kara yawan mutanen da za su samu tallafin kayan abinci a jihar, daga mutum dubu 300 da aka tsara bai wa tun da farko, zuwa dubu 400.

    To sai dai, kwanaki bayan fara rabon kayan abincin, wasu jama'ar jihar sun ce akwai rashin adalci a rabon abincin da ke gudana.

    Gwamnatin jihar dai ta bakin Mallam Isa Gusau, mai magana da yawun gwamnan, ta musanta wannan zargi.

    Ta kuma ce akwai ɗumbin mutanen da aka bai wa wannan tallafi ba tare da sani ko kamun-kafa ba.

    Gwamnatin jihar Bornon dai ta ce tana da tsari mai kyau na rabon kayan tallafi, ta yadda zai kai ga dukkan masu buƙata.

    A sabon tsarin tallafin dai na naira biliyan biyar ga jihohin Najeriya, gwamnatin tarayya ce za ta samar da kashi 52 na jimillar kudin, yayin da jihohi da ƙananan hukumomi za su samar da sauran kashi 48.

    • Farashin shinkafa zai tashin da bai taɓa ba cikin shekara 12 - MDD
  9. Sojoji masu mulki a Nijar sun kori jakadan Faransa daga ƙasar

    Shugabannin juyin mulkin soja sun bai wa jakadan Faransa a Nijar sa'a 48 ya fice daga ƙasar.

    Wata sanarwa da ministan harkokin wajen Nijar ya fitar ranar Juma'a ta ce hukumomin ƙasar sun yanke shawarar janye amincewarsu ga zaman Sylvian Itte a Niamey don haka suka buƙaci ya bar ƙasar a cikin sa'a 48.

    Sanarwar ta zargi jakadan na Faransa da ƙin amsa wata gayyata da ministan harkokin wajen na Nijar ya yi masa don ganawa a ranar juma'a da kuma sauran matakai na gwamnatin Faransa waɗanda suka saɓa wa muradan Nijar.

    Shawarar ta zo ne bayan jerin sanarwa da zanga-zangar nuna adawa da ƙasar Faransa, tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Shugaba Bazoum Mohamed, wanda suke ci gaba da tsarewa tare da iyalinsa.

    Shugabannin juyin mulkin sun zargi gwamnatin birnin Paris da son amfani da ƙarfin soji a Nijar don sake mayar da Bazoum kan mulki, sun kuma yi iƙirarin cewa tsohuwar uwargijiyar ƙasar a zamanin mulkin mallaka ta sanya Ecowas a cikin aljihu.

  10. Denmark na shirin haramta ƙona Al-Kur'ani

    Ƙasar Denmark na shirin haramta ƙona littafi mai tsarki, bayan da aka samu faruwar hakan da dama da suka hada da ƙona ƙur'ani, lamarin da ya tunzura musliman ƙasar har suka gudanar da zanga-zanga.

    Harmcin zai shafi duk wasu alamomi da ake amfani da su a addinance da suka hada da gicciya da kiristoci ke amfani da ita.

    Sai dai hakan zai shafi gama garin wurare, za kuma a tabbatar da dokar ta karade dukkan ƙasar.

    Ministan shari'ar ƙasar ya ce Peter Hummelgaard ya ce dokar zata tabbatar da ƴancin fadin albarkacin baki.

    Ana sa ran majalisar ƙasar za ta soma mahawara kan dokar cikin wata mai kamawa.

  11. Yadda aka sace mata kimanin 40 a Borno

  12. Ba mu da niyyar ruguza Nijar - Ecowas

    Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Afirka ta Yamma (Ecowas) ta yi watsi da zarge-zargen cewa wasu ne daga ƙasashen waje ke ingiza ta a kan lallai sai tilasta wa sojojin Nijar, mayar da ƙasar kan tafarkin tsarin mulki.

    “Ecowas, ƙungiyar ƙasashe ce mai aiki da dokoki da tsare-tsare, ƙa'idoji da ladubban da suka kafa ta.

    Muradinmu shi ne mu kare haƙƙoƙin al'ummarmu,” Omar Touray, shugaban hukumar Ecowas ya ce a lokacin wani jawabi da ya gabatar a Abuja, babban birnin Najeriya.

    Omar Touray ya ƙara da cewa Ecowas ba ta ƙaddamar da yaƙi a kan al'ummar Nijar ba, yayin da ake fuskantar barazana kan yiwuwar amfani da ƙrfin soji da nufin mayar da shugaban ƙasar wanda aka zaɓa a kan tafarkin dimokraɗiyya.

    Ya ƙara da cewa ƙungiyar ba ta da niyyar mayar da Nijar, ƙasar da za a ruguza. “Ecowas ba za ta taɓa barin al'ummar Nijar su sha wahala a hannun maƙiya a cikin gida da kuma ƙetare ba.

    Kawai dai Ecowas ta damu ne da abin da zai kyautata rayuwar al'ummar Nijar.”

    Omar Touray ya ce Ecowas za ta yi amfani da "duk wata dama da take da ita” don mayar da zaman doka a ƙasar.

    Ya ƙara da cewa sojojin da suka yi juyin mulki a watan Yuli tun farko “sun bijire wa duk wani ƙoƙarinmu na diflomasiyya” kuma ya ce “ba za a taɓa amincewa da” mulkin riƙon ƙwarya tsawon shekara uku da sojojin juyin mulkin suka sanar ba.

    • Gwamnatin riƙon ƙwaryarmu ba za ta wuce shekara uku ba - Tchiani
  13. Kungiyoyin Premier sun kashe fam biliyan 1.95 a cinikin 'yan wasa

  14. An yi jana'izar sojojin Najeriya 20 da 'yan fashin daji suka kashe a jihar Neja

    Rundunar sojin Najeriya ta yi jana'izar dakarunta kimanin 20, waɗanda 'yan ta-da-ƙayar-baya suka kashe cikin jihar Neja.

    Rundunar ta ce a farkon makon jiya ne aka kashe dakarunta guda 36 a lokacin wani harin kwanton-ɓauna a kan titin Zungeru zuwa Tegina kafin daga bisani wani jirgin helikwafta ya rikito ƙasa a kusa da ƙauyen Chukuba na ƙaramar hukumar Shiroro duk dai a cikin jihar Neja.

    Daga cikin manyan jami'an gwamnati da suka halarci jana'izar, akwia sabon ministan tsaro Badaru Abubakar da takwaransa ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle, sai kuma babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa.

    Yayin taron jana'izar a maƙabartar sojoji da ke Abuja, an ambato Christopher Musa ya ce rundunar sojin Najeriya za ta bi kadin kashe dakarunta da aka yi ranar 14 ga watan Agusta a kan titin Zungeru zuwa Tegina.

    Ya ce babu wanda zai kuɓuta cikin waɗanda ake zargi da aikata kashe-kashen, ya ƙara da cewa rundunar za ta yi farautar su ta kowacce hanya.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a cikin waɗanda aka binne a maƙabartar har da: Farabiti Habib Aliyu da Las Kofur Nura Mohammed da AB Suleiman da Las Kofur Sunday Okopi da kuma ƙarin sojoji guda 16.

  15. Masu sa ido sun soki zaɓen Zimbabwe

    Masu sanya idanu daga ƙasashen yankin kudancin Afirka sun soki zaɓen shugaban ƙasar Zimbabwe da a yanzu ake ƙirga ƙuri'u.

    ƙungiyar ƙasashen yankin kudancin Afirka ta SADC ta ce an yi zaɓen cikin lumana, to amma wasu ɓangarori sun gaza cika dokoki da ƙa'idojin ƙasar.

    Fiye da masu sa ido 40 aka kama ranar Laraba, a yayin da suke ƙoƙarin kwatanta lissafin ƙirgen ƙuri'unsu da na hukumar zaɓen.

    Kamen da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil-adama suka yi Allah wadai da shi.

    Shugaban ƙasar Emmerson Mnangagwa na neman wa'adin mulki na biyu a zaɓen, a yayin ƙasar ke fama da matsalar rashin aikin yi, da hauhawar farashin kayayaki.

    Zaɓen dai ya fi zafi tsakaninsa da babban abokin hamayyarsa Nelson Chamisa na gamayyar ƙawancen wasu jam'iyyun adawa.

  16. Gwamnatin Najeriya za ta tattara bayanan talakawan ƙasar

    Ministar harkokin jin-ƙai da kawar da talauci ta Najeriya, Betta Edu ta ce gwamnatin ƙasar za ta yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa da gwamnonin jihohi, da ƙananan hukumomi da kuma shugabannin al'umma domin tantance cikakkun bayanan talakawan ƙasar.

    Misis Edu ta bayyana haka ne ranar Juma'a a lokacin hira da gidan talbijin na Channels.

    Ta ƙara da cewa gwamnati za ta yi hakan ne domin cimma burin ma'aikatar jin-ƙai ta ƙasar na fitar da miliyoyin 'yan ƙasar daga ƙangin talauci.

    ''Abu na farko da za mu fara yi, shi ne tantance rajistar sunayen masu ƙaramin ƙarfi ta ƙasar, domin tabbatar da cewa talakawan ne a cikinta, waɗanda suka cancanci shiga cikin rajistar," in ji Ministar jin -ƙayin.

    Ta ci gaba da cewa a 'yan makonnin baya-bayan nan an yi ta samun ce-ce-ku-ce daga ɓangaren ƙungiyar gamnonin ƙasar da sauran ƙungiyoyi, kan ingancin rajistar.

    "Wasu na cewa ta yi, wasu kuma na cewa ba ta ba, saboda mutanen da ke cikinta, ba su ne suka cancanci shiga cikinta ba, an shigar da siyasa cikin wajen haɗa rajistar", in ji ta.

  17. Rasha ta musanta hannu a mutuwar Prigozhin

    Gwamnatin ƙasar Rasha ta musanta hannu a hatsarin jirgin da ya rutsa da shugaban sojojin hayar ƙasar Yevgeny Prigozhin.

    Mai magana da yawan shugaban ƙasar Rasha, Dmitry Peskov ya shaida wa BBC cewa zarge-zargen da ake yi kan hannun gwamnatin ƙasar a mutuwar Prigozhin "ƙarairayi ne marasa tushe".

    Ranar Laraba da yamma ne wani jirgin sama da ake kyautata zaton Prigozhin na cikinsa ya yi hatsari a arewacin birnin Moscow.

    Cikin watan Yuni ne Mista Prigozhin ya jagoranci wani boren soji da bai yi nasara ba a ƙasar.

  18. Rubiales ya ƙi ajiye aikinsa kan sumbatar 'yar wasa

  19. Monaco na daf da daukar Balogun daga Arsenal

  20. Babu inda Salah zai tafi - Klopp