Bankwana
Masu bibiyarmu a wannan shafi, da haka muka kawo ƙarshen rahotannin na kai-tsaye.
Sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kai mu za mu kawo muku wasu sababbi.
Umar Mikail da Rabiatu Kabir Runka ke fatan mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Badamasi Abdulkadir Mukhtar and Umar Mikail
Bankwana
Masu bibiyarmu a wannan shafi, da haka muka kawo ƙarshen rahotannin na kai-tsaye.
Sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kai mu za mu kawo muku wasu sababbi.
Umar Mikail da Rabiatu Kabir Runka ke fatan mu kwana lafiya.
Ministan harkokin wajen Birtaniya ya yi maraba da abin da ya kira tsattsauran matakin da Ƙungiyar Ecowas ta dauƙa a kan Nijar.
James Cleverly na magana ne bayan ganawa da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a Abuja, a ziyarar da yake ta kasashe uku a Afirka.
Mista Cleverly ya ce, Birtaniya na son ganin zaman lafiya da dimokraɗiyya sun dawo a Nijar.
A gobe Alhamis ne Sakataren harkokin wajen na Birtaniya zai kammala ziyarar tasa a Zambiya.
Wani harin jirgin sama maras matuki da Rasha ta kai a kan tashar jirgin ruwa ta Danube, ya janyo tashin farashin kayan abinci na awo.
A karo guda, farashin alkama ya ƙaru da kusan kashi biyar cikin ɗari, bayan hari na Izmail, garin da ke kusa da iyaka da Romania.
Ukraine ta ce harin ya lalata sama da tan dubu 40 na, abincin dangin hatsi, wanda za a kai wa ƙasashen Afirka, da China da kuma Isra'ila.
Ana ci gaba da matsa wa Shugaba Valdimir Putin lamba, kan komawa yarjejeniyar fiton kayan abincin ta tekun Bahar-Aswad.
An yanke wa ɗan bindigar da ya hallaka mutum goma sha ɗaya a wani wajen ibadar Yahudawa a birnin Pittsburgh, na Amurka, hukuncin kisa.
Bayan waɗanda suka mutu, akwai mutum bakwai da suka haɗa da 'yan sanda biyar , waɗanda suka samu raunuka a lokacin da Robert Bowers ya buɗe wuta a wajen ibadar na Tree of Life,shekara biyar da ta wuce.
Bakin dukkanin masu taimaka wa alkali yanke hukunci, na tarayya ya zo ɗaya cewa a zartar masa da hukuncin kisa.
Kuma masu gabatar da ƙara sun kafe cewa mutumin ya tsani Yahudawa, kuma bai nuna nadama ba a kan harin.
Yayin da su kuwa lauyoyinsa suka ce yana da matsalar kwakwalwa sosai, a don haka suka bukaci a yanke masa hukuncin ɗaurin na rai da rai, ba tare da damar yi masa afuwa ba nan gaba.
Wannan shi ne hukuncin kisa na farko na tarayya a Amurka, ƙarƙashin gwamnatin Biden.
Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Birgediya JanarTukur Gusau, ya ce manyan hafsoshin tsaronƙungiyar Ecowas za su samar da mafita idan dukkan hanyoyin da aka bi a siyasance ba su yi tasiri ba bayan juyin mulki a Nijar.
"Matakin soji zai zama na ƙarshe da za a ɗauka," kamar yadda ya shaida wa BBC.
Manyan hafsoshin tsaron ƙungiyar ta raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma na tattaunawa a Abuja daga yau Laraba zuwa Juma'a domin tattaunawa kan hanyoyin da za a bi wajen shawo kan sojojin da suka yi juyin mulkin, inda aka hamɓarrar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum a makon da ya gabata.
Manyan hafsoshin tsaron Ghana, da Najeriya, da Benin, da Togo, da Saliyo, da Laberiya, da Gambiya, da Cote D’Ivoire, da Cape Verde ne ke halartar taron.
Sai dai takwarorinsu na Mali, da Nijar, da Guinea Bissau, da Burkina Faso, da Guinea ba su halarta ba sakamakon dakatar da su da Ecowas ta yi daga ƙungiyar saboda juyin mulkin da suka jagoranta a ƙasashensu.
Manyan hafsoshin tsaron za su gabatar da matakin da suka cimma ga shugaban ƙungiyar Bola Tinubu a ranar Juma'a.
Daga nan ne shugaban ƙungiyar zai yanke shawara kan mataki na gaba da za a ɗauka kan sojojin ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani, wanda ya ayyana kan sa a matsayin shugaban Nijar.
Shugabannin ƙungiyar ƙwadago a Najeriya sun kammala ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja.
An yi ganawar 'yan sa'o'i bayan mambobin ƙungiyar sun yi zanga-zangar ƙasa baki ɗaya don yin tir da cire tallafin man fetur.
Yayin zanga-zangar, 'yan ƙwadagon sun shiga zauren Majalisar Dattawan Najeriya, inda Mai Tsawatarwa na Majalisa Sanata Ali Ndume ya tarɓe su.
Zuwa yanzu ba a bayyana abin da ɓangarorin suka tattauna ba, da kuma ko sun cimma wata matsaya.
Majalisar Dattawan Najeriya ta ɗage zaman da take yi na tantance mutanen da Shugaba Tinubu ya aike musu don naɗa su a matsayin ministoci.
Zuwa yanzu Majalisar ta tantance rukunin farko na mutum 28 da Fadar Shugaban Ƙasa ta aika musu tun a makon da ya gabata.
Majalisar ta karɓi cikon mutum 19 a yammacin yau, sannan ta ɗaga zaman zuwa Juma'a don ci gaba da tantance su.
Mutum biyar aka tantance a yau, mutum tara ranar Talata, da kuma 14 a ranar farko.
Ƙarin sunayen ya sa jimillar adadin ministocin ta zama 47.
Bayan sunan mutum 28 da ta aika wa Majalisar Dattawa, Fadar Shugaban Najeriya ta aika ƙarin mutum 19 a yau Laraba domin tantance su a matsayin ministoci.
Ga sunayen da Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya karanto kamar haka:
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya bayyana ƙarin sunayen mutum 19 da Shugaba Bola Tinubu ya aika musu domin naɗa su ministoci.
Cikin jerin har da tsofaffin gwamnoni biyar da suka haɗa da Bello Matawalle na Zamfara, da Atiku Bagudu na Kebbi, da Gboyega Oyetola na Osun.
Sauran tsofaffin gwamnonin su ne Ibrahim Geidam na Yobe, da Simon Lalong na Jihar Filato.
Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Femi Gbajabiamila ne ya kai wa Majalisa sunayen a madadin shugaban ƙasa bayan 28 da ya bayar tun farko.
Majalisar Dattawan Najeriya ta tantance Farfesa Ali Pate a matsayin wanda Shugaba Tinubu ke son naɗawa a matsayin minista.
An haifi Farfesa Muhammad Ali Pate ranar 6 ga watan Satumban 1968 a Ƙaramar Hukumar Misau ta Jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Ƙwararren likita ne a ɓangaren cutuka masu yaɗuwa kuma tsohon ƙaramin ministan lafiya a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan.
Ya fuskanci tambayoyi daga sanatoci game da yadda zai sauya ɓangaren riga-kafi a Najeriya, amma ɗaya ya amsa daga ciki saboda Majalisar ta taɓa tantance shi a baya.
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya, Femi Gbajabiamila ya gabatar wa majalisar dattawa jerin sunaye na biyu, na mutanen da shugaban ƙasar ke neman amincewar ta don naɗa su ministoci.
Femi Gbajabiamila ya miƙa sunayen ga shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, a daidai lokacin da majalisar ke tantance wasu daga cikin mutanen da ke cikin jerin farko na sunayen da aka gabatar mata.
A ranar Alhamis ɗn da ta gabata Gbajabiamila gabatar da sunayen mutum 28 na farko da shugaba Tinubu ke son naɗawa ministoci, ya kuma ce sauran na nan tafe.
Zuwa yanzu shugaban majalisar bai karanta sunayen ba tukun.
An dakatar da dandalin sada zumunta na TikTok a Senegal a bisa zargin amfani dashi wajen tunzura rikici.
Ministan sadarwar ƙasar Moussa Bocar ya ce dandalin ya zamo shafin da masu son yaɗa kalaman ɓatanci da raba kan jama'a ke amfani da shi wajen cimma manufar su.
An ɗauki matakin dakatar da TikTok ɗin ne kwanaki bayan kama jagoran ƴan adawar ƙasar, Ousmane Sonko inda ake zargin shi da tunzura masu zanga-zanga da kuma wasu laifukan.
An kashe mutum uku a birnin Ziguinchor, garin da Ousmane Sonko ke jagoranta a matsayin magajin gari.
Hukumomi a ƙasar sun kuma katse sadarwar intanet na wucin-gadi a makonnan.
A karon farko tawagar Afirka ta kudu ta kai zagaye na biyu na gasar cin kofin ƙallon ƙafa ta mata.
Tawagar ta doke Italiya da ci 3 da 2 a wasan da suka buga.
Kafin fara gasar dai an samu ruɗani a tawagar Afirka ta kudun bayan ƴan wasan sun nemi a biya su kuɗin alawus dinsu.
Sweden, wadda ta ke rukuni ɗaya da Afirka ta kudu ta doke Argentina da ci 2 da nema, kuma ita ma ta tsallake zuwa zagayen na biyu.
Majalisar Dattawan Najeriya ta tantance Dele Alake daga jihar Ekiti.
A lokacin tantance shi, ƴan majalisar sun yi wa Dele Alake tambayoyi da suka shafi harkar yaɗa labarai, ɓangaren da ya fi ƙwarewa kuma ya bayar da amsa.
Dele Alake tsohon kwamishinan yaɗa labarai da tsare-tsare ne a jihar Legas daga shekarar 1999 zuwa 2007 lokacin shugaba Bola Tinubu yana gwamnan jihar.
Ya kuma taɓa zama mai bayar da shawara kan yaɗa labarai ga Chief Moshod Abiola.
Kamfanin sarrafa barasa na Najeriya ya ce zai ƙara farashin barasar daga ranar 10 ga watan Agustan 2023.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, kamfanin ya kafa hujja da tashin farashin kayan haɗa barasar wanda ya ce kai tsaye ya shafi aikin sa.
“Muna sanar da ku cewa farashin kayan mu zai canza daga ranar 10 ga watan Agustan 2023.”
Matakin da kamfanin ya ɗauka dai zai iya sa takwarorinsa su ɗauki irin sa kasancewar shi jigo a cikin harkar. Zai kuma iya kawo raguwar masu shan barasar a Najeriya.