Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ko da sauyin kuɗi ko babu mun san za mu ci zaɓe - Tinubu

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawo wa domin kawo muku sabbin labarai.

    Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. 'Buhari bai hana Tinubu binciken jami'an gwamnatinsa ba'

    Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bai hana sabon shugaban ƙasar Bola Tinubu binciken jami'an gwamnatinsa ba.

    Cikin wani saƙo da mai magana da yawun tsohon shugaban Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa ta twitter ya ce, labaran da ke yawo a shafukan sada zumunta, waɗanda ke cewa Buharin ya nemi Tinubu da kada ya binciki jami'an gwamnatinsa, labarai ne na ƙanzon-kurege.

    Gabanin babbar salla ne Bola Tinubu ya gana da Buhari a wata ziyara da ya kai gidansa da ke Landan lokacin wata ziyarar ta ƙashin ƙai da Tinubun ya kai Landan bayan taron harkokin kuɗi na duniya da ya halarta a birnin Paris.

    To amma Mallam Garba Shehu ya ce a lokacin ziyarar Buhari da Tinubun ne kawai suka gana babu wani mutum a ɗakin da suka gana, dan haka babu wanda ya san me suka tattauna.

    Sanarwar ta kuma ce Buhari ya zaɓi fita daga Najeriya ne saboda gudun tsoma wa sabuwar gwamnati baki a al'amuranta.

    ''Da farko ya zaɓi ya zauna a gidansa da ke Daura domin samun hutu da nutsuwar da yake buƙata, to amma hakan bai samu ba, kasancewar a kullum, dare da rana, safe da yamma ɗimbin mutane ne ke ziyartarsa'', in ji Mallam Garba Shehu cikin saƙon da ya wallafa.

    Ya ƙara da cewa tsohon shugaban ya tafi Landan ne domin samun hutun da yake buƙata, sannan kuma hakan zai bayar da dama ga sabuwar gwamnatin Tinubu ta gudanar da ayyukanta wajen cika alƙawuran da suka ɗaukar wa talakawan Najeriya.

  3. Binciken BBC ya gano har yanzu Wagner na ɗaukar mayaƙa

    Kungiyar dakarun sojin hayar Rasha ta Wagner na ci gaba da ɗaukar mayaƙa tare da horar da su a faɗin kasar Rasha, kwanaki bayan da kungiyar ta gudanar da tawaye a kasar

    BBC ta yi amfani da lambar wayar ƙasar Rasha, inda ta kira gwamman cibiyoyin ɗaukar mayaƙan da ke ƙasar.

    BBC na kiran wayar ne a madadin wani ɗan uwanmu da ke neman aikin.

    Kuma duk cibiyoyin da muka tuntuɓa sun tabbatar mana da cewa ana gudanar da aiki.

    Kama daga yankin Kaliningrad da ke yamma zuwa Krasnodar da ke kudu ba a ma san cewa gwamnati ta raba gari da ƙungiyar ba.

    A birnin Arctic na birnin Murmansk, wata mata ta tabbatar mana da cewa har yanzu ana ɗaukar mayaƙa domin turasu Ukraine.

    "Dama don can muke ɗaukar mayaƙan, dan haka idan mutum ya yadda zai je, kawai ya kirani, domin shirya hakan,'' in ji ta.

    Mutane da dama da BBC ta tattauna da su a waya sun tabbatar da cewa matasa da dama na ci gaba da shiga ƙungiyar, fiye da ma'aikatar tsaron ƙasar.

  4. Hotunan yadda 'yan sanda suka yi arangama da masu zanga-zanga a Faransa

  5. Ko da sauyin kuɗi ko babu mun san za mu ci zaɓe - Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce tun asali dama yana da ƙwarin gwiwar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar cikin watan Fabrairun da ya gabata, duk kuwa da tsarin sauyin kuɗi da CBN ya ɓullo da shi.

    Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa a ziyara da ya kai wa sarakunan gargajiya na jihar Ogun da ke kudu maso yammacin ƙasar.

    Yayin da yake magana kan matsalolin da ya fuskanta a zaɓen shugaban ƙasar da ya kai shi ga nasara, shugaba Tinubu ya bayyana damuwarsa kan matakin taƙaita yawan kuɗi da batun sauyin kuɗi da CBN ya ɓullo da shi, wanda Tinubu ya ce ''bai yi nasara ba''.

    Tinubu ya kuma gode wa sarkin Ijebu bisa shawarar da ya ba shi, game da yadda zai ɓullo wa ƙalubalen a lokacin da ya ziyarci fadarsa a baya.

    Ya ce ya yi amfani da ƙwarin gwiwa da sarkin ya nuna masa domin magance ƙalubalen da ya fuskanta a zaɓen.

    "An riƙe mana kuɗaɗenmu, batun sauyin kuɗi bai yi nasara ba, abin ya tayar da hankali a lokacin. Ina tuna lokacin da na zo jihar domin samar wa kaina mafita, kamar yadda taken jihar Ogun yake, don haka ko da sauyin kuɗi ko babu za mu yi nasara a zaɓen'', in ji Shugaba Tinubu.

    Matakin sauyin kuɗi da CBN ya ɓullo da shi cikin watan Oktoban shekarar da ta gabata ya haifar matsaloli masu tarin yawa da wahalhalu ga 'yan ƙasar.

    Lamarin da ya sa wasu gwamnonin jihohin ƙasar suka gurfanar da CBN gaban kotun Kolin ƙasar, wadda ta yanke hukuncin ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudin har zuwa watan Disamban 2023.

    Sai dai tsohuwar gwamnatin ta ce wasu daga cikin dalilan da suka sanya ta ɓullo da tsarin su ne domin rage yawan amfani da tsabar kuɗi tsakanin al'umma da hana amfani da kuɗi wajen sayen ƙuri'a da kuma bunƙasa tsaro.

    A farkon watan nan ne dai shugaba Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin ƙasar Godwin Emefiele daga kan kujerarsa, inda jami'an taron DSS suka kama shi tare da tsare shi a hannunsu.

  6. Yanayin zafi ya zarce maki 40 a Saudiyya

    Hukumar lafiya ta Saudiyya ta ce akalla mahajjata bakwai ne suka mutu sakamakon tsananin zafin rana da ake fuskanta a ƙasar, wanda ya haura maki 40 a ma'aunin salshiyos.

    Mai magana da yawun ma'aikatar ya ce a ranar Laraba kaɗai an samu mutum 2200 da zafin ranar ya yi musu illa, ciki har da fiye da mutum 250 da zafin ya kayar da su.

    Hukumomin Saudiyya sun ce sun samar da kwalaben ruwa da fankokin da ke yayyafa wa mutane ruwa, baya ga mutum 32,000 haɗi da masu bayar da taimako na ƙashin kansu, don taimakawa magance matsalolin da zafin ranar ka iya haifarwa.

  7. Akwai yiwuwar farashin litar man fetur ya yi tashin gwauron-zabi - IPMAN

    Ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu a Najeriya ta ce akwai yiwuwar nan da lokaci kaɗan farashin man fetur zai zarce naira 600 a kan kowace lita.

    IPMAN ta ce hakan zai faru ne sanadiyyar rashin tabbas kan samuwar dala ga ƴan kasuwa masu shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen waje.

    Bayanai sun nuna cewa da zarar 'yan kasuwa masu zaman kansu suka fara shigo da man fetur a wata mai kamawa, farashin litar mai zai haura sama a faɗin ƙasar.

    A lokacin da yake tabbatar wa BBC da wannan batu, shugaban ƙungiyar dillalan man fetur ɗin a yankin Arewacin Najeriya, Bashir Dan-Mallam ya ce dole ne sai gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace domin hana faruwar hakan.

    Dan-Mallam ya ce samuwar dalar a wadace ga ƴan kasuwa za ta hana hauhawar farashin na litar mai.

    A yanzu dai kamfanin man fetur na ƙasar NNPC ya ce zai riƙa shiga da kashi 30% na man fetur ɗin da ƙasar ke buƙata, yayin da ƴan kasuwa za su shigar da sauran.

    A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, wani lamari da ya haifar da tashin farashin litar man fetur a faɗin ƙasar.

  8. Birtaniya za ta ɗaukaka ƙara kan haramta mata tura ƴan ci-rani Rwanda

    Gwamnatin Birtaniya ta ce za ta ɗaukaka ƙara game da hukuncin da kotu ta yanke na bayyana shirin ƙasar na tura ƴan ci-rani da masu neman mafaka zuwa Rwanda a matsayin wanda ya saɓa wa doka.

    Kotun ta bayyana cewa Rwanda ba ta cika ƙa'idojin da za ta zama amintaccen wuri ga ƴan ci-ranin ba.

    Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak a martanin da ya mayar game da hukuncin ya ce 'bai amince da hukuncin kotun ba' kuma gwamnati za ta ɗaukaka ƙara.

    Sunak ya ce duk da yana martaba hukuncin kotu, amma zai yi iyakar iyawarsa wajen ganin ya dakatar da ayyukan ƴan ta'asa masu amfani da kwale-kwale suna tsallakawa da mutane cikin Birtaniya.

    Ya ƙara da cewa "Ina da yaƙinin cewa Rwanda ta tabbatar mana da cewa babu yiwuwar gwamnati za ta yi yunƙurin mayar da masu neman mafaka da za a kai su ƙasar zuwa wata ƙasar ta daban."

    "Rwanda ƙasa ce mai tsaro. Yanzu za mu nemi izinin ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke.

    Ita ma gwamnatin Rwanda ta dage kai da fata cewar tana daga cikin ƙasashe mafiya aminci a cikin ƙasashen duniya masu tasowa.

  9. Ghana na tattaunawa game da ƙaƙaba tsauraran dokoki kan masu luwaɗi da Maɗigo

    Majalisar Dokokin Ghana na sa ran tattaunawa a yau kan shawarwarin wani kwamitinta da ke neman a samar da wata doka da za ta tsananta wa masu luwaɗi da maɗigo a ƙasar.

    Tanade-tanaden dokar na farko sun haɗa da hukuncin ɗaurin shekara biyar ga masu aikata luwaɗi da maɗigo da kuma ɗaurin shekara goma ga masu hanƙoron kare haƙƙin ƴan luwaɗin da maɗigo.

    Dokar kuma ta ƙunshi batun sauya tunanin ƴan luwaɗin domin su dawo daidai, sannan kuma za a haramta yaɗa abubuwan da ke nuna goyon baya ga ƴan luwaɗi a kafafen yaɗa labaru da kafofin sada zumunta.

    Shugaban Ghana Nanna Akufo-Addo ya ce gwamnatinsa ta tsoma domin gyara wasu ɓangarori na dokar.

    • Gwamnatin Ghana ta hana cin nama tsawon wata ɗaya a wani yanki
    • Yadda jarirai suka mutu a asibiti sanadiyyar yanke wutar lantarki
  10. ICRC ta taimaka wajen karɓo sojojin Sudan daga hannun mayaƙan RSF

    Ƙungiyar bayar da agaji ta ICRC ta ce ta taimaka wajen ganin an karɓo sojojin Sudan 125 daga hannun mayaƙan RSF.

    ICRC ta ce an ɗauki sojojin - waɗanda da dama daga cikin su suka samu rauni - a cikin motocin bas daga Khartoum zuwa birnin Wad Madani da ke kudanci.

    Rikicin tsakanin dakarun gwamnatin Sudan da mayaƙan RSF ya haifar da tagayyarar kusan miliyan mutum miliyan uku.

    • Me za a yi da gawawwakin mutanen da aka kashe a Khartoum?
    • Tuwo na fara nema bayan dawowa gida daga Sudan- Ɗaliba
  11. NAFDAC ta gargaɗi mutane kan shan lemon kwalba na 'Sprite'

    Hukumar tabbatar da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya ta ce tana gargaɗin al'ummar ƙasar game da shan lemon kwalba na 'Sprite' bayan da ta gano gurɓataccen irin wannan lemo a kasuwa.

    Hukumar ta NAFDAC ta ce ta gano lemon ne bayan binciken da ta yi sanadiyyar koken da ta samu daga wasu masu amfani da lemon.

    NAFDAC ta ce binciken nata ya gano kiret biyar na irin wannan lemo a kwalba mai girman 50cl, inda aka ga ɓurɓushin wani abu na yawo a cikin lemon.

    Tuni aka tura wannan gurɓataccen lemo zuwa ɗakin bincike na hukumar domin tantancewa.

    Haka nan hukumar ta ce ta bayar da umarnin zagayawa domin ƙwato irin waɗannan samfuri na lemon.

    Haka nan an buƙaci kamfanin da ke yin wannan lemo ya dawo da duk irin wannan kwalba da ya sayar, sannan ya kai wa hukumar cikakkun bayanai.

    NAFDAC ta kuma buƙaci duk wanda ya sha irin wannan lemo ko ya san wanda ya sha kuma yake jin ba daidai ba game da lafiyarsa, ya nemi agajin likitoci.

    Bayanin lemon da aka gano yana ɗauke da datti a cikinsa shi ne:

    BN:AZ6 22:32

    MFD:180423

    BB:180424

    • NAFDAC ta kama manyan motoci biyu cike da Tramadol
  12. Tsananin zafi ya kwantar da mahajjata 6,700 a Saudiyya zuwa yanzu

    Cibiyoyin kula da waɗanda zafin rana ya illata a wuraren ibada masu tsarki na ƙasar Saudiyya na ci gaba da samun hauhawar mutanen da ake kwantarwa saboda jigata.

    Ana alaƙanta lamarin da gazawar mahajjata wajen bin ƙa'idojin kare kai daga tsananin zafin rana.

    Ma'aikatar Lafiya ta Saudiyya ta faɗakar da mahajjata game da hatsarin tsananin zafin rana, inda ta buƙace su da su riƙa sanya ɓaƙin tabarau da kuma shan ruwa sosai, sannan su guje wa zirga-zirgar da ba ta wajaba ba.

    Haka nan ma'aikatar ta buƙaci maniyyatan da su guje wa tsayuwa na tsawon lokaci.

    Ma'aikatar ta ce a halin yanzu waɗanda tsananin zafin ranar ya kwantar sun kai 6,700 tun bayan fara aikin hajjin bana.

    A jiya an samu irin wannan matsala mafi yawa, inda zafin ya illata mutum 2,200, cikinsu har da mutum 261 waɗanda suka shiga mummunan yanayi.

    • Hotunan yadda aka yi hawan Arfa na hajjin bana - 2023
    • Saudiyya ta kama wanda ya taimaka wa Bayahude shiga Makka da hawa Dutsen Arfa
  13. Shirin Birtaniya na tura masu neman mafaka zuwa Rwanda ya saɓa wa doka

    Gwamnatin Birtaniya ta sha kaye a shari'ar da ake yi kan ko shirinta na tura masu neman mafaka zuwa ƙasar Rwanda ya halasta a doka.

    A hukuncin da ta yanke, wata Kotun ɗaukaka ƙara a Birtaniya ta goyi bayan ƴan ci-rani waɗanda suka isa Birtaniya ta kwale-kwale da kuma wata ƙungiya mai zaman kanta wadda ke taimaka wa masu neman mafaka, waɗanda suka ce shirin na Birtaniya ba halastacce ba ne.

    Masu yanke hukunci biyu daga cikin uku sun amince cewar Rwanda ba ta cika ƙa'idojin da suka kamata ta karɓi irin waɗannan baƙi ba.

    Akwai yiwuwar cewa gwamnatin Birtaniya ta ƙalubalanci hukuncin a kotun ƙoli.

    • Birtaniya za ta haramta wa ɗaliban ƙasashen waje kai iyalansu ƙasar
    • Ciwon sanyi na jima'i ya tsananta a Ingila
  14. Maroko ta mayar da jakadanta a Sweden gida bayan gangamin ƙona Al-ƙur'ani

    Ƙasar Maroko ta yi wa jakadanta da ke Sweden kiranye bayan wani gangami da aka yi na ƙona littafi mai tsarki na Al-ƙur'ani a birnin Stockholm na ƙasar Sweden.

    Ma'aikatar harkokin wajen Maroko ta bayyana gangamin a matsayin cin fuska da kuma rashin hankali a lokacin da al'ummar Musulmin duniya ke bikin babbar Sallah.

    Yanzu haka ana gudanar da bincike kan mutumin da ya assasa gangamin, Salwan Momik, wanda ɗan asalin ƙasar Iraqi ne.

    Ana dai zargin sa da ƙoƙarin tayar da husuma da kuma rura wutar ƙiyayya.

    Wata kotu a ƙasar Sweden ne ta tabbatar da ƴancin yin zanga-zangar da sunan ƴancin faɗin albarkacin baki.

    • Matakan da ake bi wajen buga Al Ƙur'ani
    • Yadda ake tantance kura-kurai a Qur'ani a Saudiyya
  15. Ana arangama tsakanin al'umma da ƴansanda kan kisan matashi a Faransa

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron na gudanar da taron ministocinsa na gaggawa bayan kwashe dare ana ɗauki-ba-daɗi tsakanin fararen hula da jami'an tsaro sanadiyyar kisan da wani ɗansanda ya yi ma wani matashi.

    A farkon zaman, Macron ya ce babu dalilin da zai sa mutane su rinƙa kai wa gine-ginen gwamnati farmaki.

    Sama da mutum 150 ne aka kama zuwa yanzu saboda zanga-zangar a wasu manyan biranen ƙasar.

    Matashin da aka kashe mai suna Nael, ɗan shekara 17 yana da alaƙa da baƙi mazauna ƙasar.

    Lamarin ya faru ne a ranar Talata, inda wani jami'in ɗan sanda ya ɗauke shi da bindiga a kusa-kusa.

    Yanzu haka an nemi agajin ƴansanda da suka ƙware wajen tarwatsa masu zanga-zanga domin shawo kan lamarin.

  16. Ana bincike kan mutumin da ya tunkari ofishin jakadancin Amurka ɗauke da bindiga

    An harbe wani mutum dauke da makami a wajen karamin ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Jeddah na kasar Saudiyya.

    An kuma kashe wani jami'in tsaro dan asalin kasar Nepal yayin afkuwar lamarin.

    Hukumomin Saudiyya sun ce mutumin ya fito ne a cikin mota kuma ya nufi ginin dauke da bindiga.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce babu wani Ba'amurke da ya jikkata a lamarin.

    Hukumomin Saudiyya sun kaddamar da bincike.

    A shekarar 2016 ne wani dan kunar bakin wake ya kai wa ofishin jakadancin hari a ranar ‘yancin kai na Amurka.

  17. Barka da waraha!

    Da fatan ana ci gaba da shagulgulan sallah lafiya.

    A wannan shafi za mu riƙa kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance tare da mu har zuwa ƙarshen wannan rana.

    Ku je shafukanmu na BBC Hausa facebook da twitter da instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan abubuwan da muke wallafawa.