Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Za mu farfaɗo da yardar 'yan Najeriya a kan 'yan sanda'

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Haruna Kakangi, Ibrahim Yusuf Mohammed and Mukhtar Adamu Bawa

  1. , Ban kwana

    To, masu bibiyarmu a nan ne muka kawo ƙarshen labarai da rahotannin da muke gabatar muku. Da fatan kun ji daɗin kasancewa da mu.

    Sai ku tara gobe Asabar don samun wasu labarai da rahotannin daga sassan duniya. A madadin duka sauran abokan aikina, ni Ibrahim Yusuf Mohammed ke muku fatan alheri.

    Amma kuna iya ci gaba da duba labaran da muka rigaya muka wallafa muku a ƙasa!

  2. Sojoji sun ƙwace fasfon mashahurin malamin Musulunci a Mali

    A ranar Alhamis ɗin da ta wuce ne gwamnatin Mali ƙarƙashin jagorancin sojoji masu mulki an kasar ta kwace fasfo din diflomasiyya na fitaccen malamin nan na musuluci Mahmoud Dicko, wanda ke matukar sukar gwamnatin mulkin soja.

    Gidan rediyon al'umma mai suna Nostalgie ya ruwaito cewa hukumomi sun kwace fasfo din Mista Dicko a filin tashi da saukar jiragen sama da ke Bamako babban birnin kasar bayan ya dawo daga makwabciyar kasar Mauritania.

    Gwamnatin marigayi shugaba Ibrahim Boubacar Keïta ta bai wa Mr Dicko fasfo din.

    Tashar talabijin ta Renouveau TV mai zaman kanta ta ruwaito cewa " Kasa da mako daya bayan da ya yi kakkausar suka ga gwamnatin rikon kwarya, hukumomi san yi matukar sanya wa Dicko ido fiye da kowane lokaci''

    A watan Mayu, Mr Dicko da wasu kungiyoyin addinin Islama sun kaddamar da wani yunkuri na nuna adawa da shirin ayyana kasar a matsayin kasar da ba ta karkasjhin kowanne addini kamar yadda aka tsara a daftarin tsarin mulki.

    Mista Dicko ya kuma taka rawa a cikin zanga-zangar da ta haifar da hambarar da Mista Keita a shekarar 2020.

  3. Sudan ta Kudu 'ba ta shirya' wa 'yan gudun hijirar Sudan ba

    Ministan harkokin wajen Sudan ta Kudu, Deng Dau Deng ya shaida wa BBC cewa Sudan ta Kudu ba ta shirya wa ƙwararar 'yan gudun hijirar da suka ketara iyakokin ƙasar bayan ɓarkewar rikici a makwabciyarta Sudan cikin watan Afrilu ba.

    Da yake bayyana lamarin a matsayin ƙalubale, Mista Deng ya ce "Buƙatun abubuwan jin ƙai na da yawa" musamman abinci, da kula da lafiya da kuma matsugunnai.

    Ya ƙara da cewa ya zuwa yanzu, kimanin mutum 150,000 ne suka tsere daga Sudan zuwa Sudan ta Kudu, waɗanda akasari 'yan ƙasar ne da suka dawo.

    Ya kuma musanta rade-raɗin cewa Sudan ta Kudu ta rufe iyakokinta ga 'yan gudun hijirar Sudan..

  4. Zan yi aiki bisa adalci kuma zan sakawa sojoji masu ƙwazo - Janar Lagbaja

    Sabon babban hafsan sojojin ƙasan Najeriya (COAS), Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya karɓi aiki a matasayin babban hafsan sojin ƙasa na 23 inda ya yi alkawarin sauke nauyin da aka ɗora masa bisa adalci.

    Lagabaja ya karbi aiki ne a hannun Laftanar Janar. Faruk Yahaya wanda ke kan kujerar tun watan Mayun 2021.

    Ya ce burin kowanne sojan yaƙi shi ne ya samu damar zama shugaban sojojin Najeriya.

    Ya kara da cewa zai yi la'akari da cancanta da aiki tuƙuru tsakanin sojoji inda ya ce zai kyautata daidai gwargwado tare da ɗaukar matakan da suka dace wajen dawo da wadanda suka kauce hanya.

    Lagbaja ya yaba wa tsohon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya, Janar Faruk Yahaya bisa jagoranci da kuma taimaka masa wajen gudanar da aiki.

    A cewarsa, a karkash jagorancin Janar Yahaya, ‘yan bindigan da suka tuba sun mika wuya fiye da yadda aka taɓa gani a baya inda ya tabbatar da cewa aikin da ya yi a ƙarƙashinsa zai taimaka masa wajen gudanar da ayyukansa na babban hafsan sojin ƙasa.

    Tun da farko, Laftanar-Janar Yahaya ya ce ya bar rundunar sojin Najeriya ne a matasayin da ya fi yadda ya same ta.

    Ya kara da cewa rundunar ta samu gagarumar nasara a yaƙin da take yi da ayyukan rashin tsaro.

    Ya ce a halin yanzu masu ta-da-ƙayar-baya na cikin ruɗani a duk filayen daga, kuma ya bukaci sojoji da kada su sassauta ƙoƙarinsu.

    Shugaba Bola Tinubu ne ya naɗa Manjo Janar Taoreed Lagbaja da sauran manyan hafoshin sojan Najeriya a ranar Litinin bayan ya sauke hafsoshin da ke kan ragama.

  5. ''Yan Najeriya ne za su yanke shawara a kan makomar kocin Super Eagles'

    Kocin Najeriya, Jose Peseiro na fuskantar babban ƙalubale wajen ci gaba da aikinsa yayin da aka bai wa magoya bayan tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, damar yanke shawarar ko zai ci gaba da zama kocin kungiyar Super Eagles

    Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya (NFF), Ibrahim Gusau, ya yi alƙawarin zai saurari ra'ayoyin 'yan Najeriya kafin yanke hukuncin karshe game da kocin.

    Tsohon kocin na ƙungiyar Porto da Sporting Lisbon da kuma Al Ahly, Peseiro, wanda kuma ya taɓa horas da Saudiyya da Venezuela, a hukumance ya karbi ragamar horar da zakarun Afirka sau uku a cikin watan Mayun 2022 kuma kwanturaginsa da NFF zai kare a ranar 30 ga watan Yuni.

    Super Eagles a hannunsa ta yi nasarar lallasa Sao Tome da Principe 10-0 da kuma kashin da suka sha a gida 1-0 yayin karawa da Guinea-Bissau.

    A ranar Lahadin da ta gabata, Najeriya da kyar ta ci Saliyo 3 - 2 ana gab da tashi, abin da ya ba ta damar samun tikitin shiga gasar cin kofin Afirka na baɗi a Ivory Coast.

    Duk da haka, kafofin watsa labarai na cikin gida da magoya baya sun soki kocin ɗan ƙasar Portugal ɗin saboda abin da wasu ke gani rashin kyawun zabar 'yan ƙwallo da kuma wasanni marasa ƙayatarwa.

  6. Ambaliyar ruwa ta mamaye gidaje Abuja

    Ambaliyar ruwa ta mamaye gidaje da dama a fitaccen rukunin gidaje na Trademore Estate dake Lugbe a babban birnin tarayya Abuja.

    Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ambaliyar ta lalata kadarori na miliyoyin naira sakamakon ruwan sama da aka yi a safiyar ranar Juma'a.

    Hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA ta bayyanawa manema labarai cewa, ambaliyar ruwan ta tafi da direban wata mota kirar Peugeot 406 a kan titin Imo dake cikin rukinin gidajen, yayin da aka ceto wasu mutane 4 wadanda aka tabbatar cewa suna cikin koshin lafiya.

    An ga mazauna yankin a lokacin da ake ruwan, suna kokarin ceton rayukansu da dukiyoyinsu bayan da ruwan ya mamaye masu gidaje.

    Rukunin gidajen Trademore ya shafe shekaru yana fama da munanan matsaloli na ambaliya wanda ya haddasa rashin rayuka da kuma asarar dukiya.

  7. Shugaban Kamfanin jirgin zuwa ƙasan teku bai ji gargaɗin da aka yi masa ba

    Babban jami'in kamfanin OceanGate, Stockton Rush ya yi watsi da gargadin da wani ƙwararre mai bincike-bincike a ƙarƙashin teku ya yi masa game da amincin jirgin ruwan Titan, wanda ya ɓata yayin da yake ɗauke da wasu 'yan yawon buɗe ido a tekun Atalantika.

    A sakonnin imel da BBC ta gani, Rob McCallum ya shaida wa shugaban kamfanin na OceanGate, Stockton Rush cewa yana iya jefa abokan huldarsa cikin hatsari, kuma ya buƙaci ya daina amfani da jirgin ruwan har sai wata ƙungiya mai zaman kanta ta tantance shi.

    Mista Rush ya amsa cewa "ya gaji da wadanda ke ƙoƙarin yin amfani da hujjar tabbatar da inganci wajen dakatar da sabbin ƙirkire-ƙirkire".

    An kawo ƙarshen ce-ce-ku-cen ne bayan lauyoyin OceanGate sun yi barazanar ɗaukar matakin shari'a, in ji Mista McCallum.

    A cikin sakonnin, Mista Rush ya bayyana rashin jin dadinsa da sukar da ake yi wa ingancin jirgin Titan, inda ya rubuta a wani sakon imel cewa: "Mun ji kukan da ba shi da tushe na 'za ku kashe mutane' sau da yawa. Ina daukar wannan a matsayin babban cin mutunci a gare ni. "

    Mista Rush ya kafa kamfanin OceanGate a shekara ta 2009, kuma kamfanin yana bai wa abokan hulɗa damar zuwa shawagi can ƙasan teku, da kuma kai ziyara wurin tarkacen jirgin ruwan Titanic, a cikin jirgi mai tafiya ƙarƙashin teku da ake kira Titan kan tikiti $250,000 kwatankwacin N188m.

  8. Za mu farfaɗo da yardar 'yan Najeriya a kan 'yan sanda - Babban Sufeto na riƙo

    Sabon babban sufeton 'yan sandan Najeriya na riƙo, Olukayode Adeolu Egbetokun ya ƙaddamar da abin da ya kira tsare-tsaren aiki don farfaɗo da yardar jama'a a kan 'yan sanda.

    Babban sufeton ya ƙaddamar da sabbin manufofin ne yayin wani taron ƙaddamar da salon shugabancinsa a shalkwatar 'yan sanda ta ƙasa da ke Abuja.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ta ce a cikin manufofin babban sufeton akwai kafa jami'an kai ɗauki cikin hanzari mai taken Quick Intervention Squad wanda zai haɗar da 'yan sandan kwantar da tarzoma da za su kasance shiri don kashe wutar fitintinu da aikata laifuka.

    Ya kuma ce shugabancinsa zai tabbatar da aiki da fasahohin zamani kamar ƙididdigar alƙaluma da harkokin tattara bayanan sirri don bunƙasa ƙwazon 'yan sanda.

    Haka kuma, babban sufeton zai tabbatar da aiki da wani tsarin martabawa da ba da lada don ƙara ƙwazo da ƙarfafa gwiwar jajirtattun jai'an rundunar. Yayin taron na ranar Juma'a manyan jami'an 'yan sandan Najeriya daga faɗin ƙasar ne suka halarta.

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ne a ranar Litinin ya naɗa sabbin hafsoshin tsaron ƙasar, a ciki har da Olukayode Egbetokun a matsayin babban sufeton 'yan sanda na riƙo.

  9. Libya ta tsare 'yan China 50 kan kuɗin kirifto

    Hukumomin Libya sun tsare wasu 'yan China 50 sakamakon wani samame da suka kai kan masu sana'ar kuɗin intanet na kirifto ba bisa ƙa'ida ba.

    Hotunan da mai gabatar da ƙara a Tripoli ya wallafa, sun nuna ɗakin da aka kama mutanen a birnin Zliten cike da kwamfutoci, da suarn na'urori

    A ranar Larabar da ta gabata ma an kama wasu mutanen da ke harkar kuɗin kirifto a birnin Misrata.

    Ƙasar Libya ta haramta gudanar da harkokin kuɗin intanet a ƙasar tun 2021.

  10. Shugaban Kenya na son a rangwanta wa ƙasashen Afirka ƙa'idojin karɓar bashi

    Shugaban Kenya William Ruto ya yi kira ga Bankin Duniya da Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) su rage tsauraran matakan bayar da bashi ga ƙasashen Afirka domin tabbatar da saukaka wa ƙasashen samun bashin.

    "Ba wai muna son samun komai a kyauta ba. To amma muna buƙatar a sauƙaƙa mana matakan samun bashi'', in ji shugaba Ruto.

    Mista Ruto, wanda ke jawabi a lokacin da ya gana da shugaban Faransa Emmanuel Macron, da shugabar IMF Kristalina Georgieva, da shugaban Bankin Duniya Ajay Banga a birnin Paris ranar Alhamis, ya yi kira ga shugabanin duniya da ke halartar taron harkokin kuɗi da ke gudana a birnin Paris, da su goyi bayan kiran da ya yi.

    A shekarar 2022 ne gwamatin Mista Ruto ta karɓi bashin dala miliyan 600 daga asusun Bayar da Lamuni na Duniya IMF.

    A watan Mayun da ya gabata ne kuma gwamnatinsa ta ƙarbo bashin dala miliyan $993 daga Bankin Duniya, don yin kasafin kuɗin ƙasar.

    Ƙasashen Afirka da dama na fuskantar bashin ƙasashen waje, sakamakon samun hauhawar farashin kayayyaki da ƙaruwar bashi.

  11. Abin da ya kamata ku sani kan sabbin dokokin canjin kudi na Najeriya

  12. 'Yan bindiga sun kashe manoma uku tare da sace wasu da dama a Birnin Gwari

    'Yan bindiga sun kashe mutum uku tare da sace wasu da dama a wani hari da suka kai garin Sabo Layi a ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

    Shugaban ƙungiyar ci gaban masarautar Birnin Gwari (BEPU) Usman Kasai, wanda ya tabbatar da kai harin, ya ce yanzu haka suna ƙoƙarin tantance yawan adadin mutanen da aka yi garkuwa da su zuwa cikin daji.

    Rahotonni sun ce 'yan bindigar sun far wa ƙauyen ranar Alhamis, inda suka riƙa harbin kan-mai-uwa-da-wabi, lamarin da ya haddasa mutuwar mutum uku.

    Jihar Kaduna wadda ke arewacin Najeriya na ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren 'yan bindiga, waɗanda ke garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

    Yawaitar garkuwa da mutane da hare-haren 'yan fashin daji a yankin arewa maso yammacin Najeriya na ɗaya daga cikin ƙalubalen tsaro da ya daɗe yana ci wa ƙasar tuwa a ƙwarya.

    Baya ga rikicin Boko Haram da ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 40,000 a yankin arewa maso gabashin ƙasar, tun shekarar 2019.

    Ga kuma ayyukan 'yan bindiga a yankin kudu maso gabashin ƙasar, waɗanda ke kai wa jami'an tsaro hare-hare.

  13. Ƴan sanda sun kama 'masu ƙwacen katin ATM' a Kaduna

    Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta kama wasu mutum biyu bisa zargin kwace wa mutane katin cirar kudi na ATM.

    A cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar SP Mohammed Jalige ya fitar, ya ce rundunar ta kama mutanen ne bayan samun rahoto daga wata mata da aka ƙwace wa katin na ATM.

    Matar ta bayar da rahoton cewa a lokacin da ta je banki domin cirar kuɗi, sai wani mutum ya zo da nufin taimaka mata, daga nan ya musanya mata katin nata.

    Mintuna bayan haka, sai aka tura wa matar saƙon cirar kuɗi har naira 404,000 daga asusun ajiyar bankin nata.

    Sanarwar ta ce bayan zurfafa bincike ne jami'an sashen tattara bayanan sirri suka kama wasu mutum biyu, Paul Agu Daniel, da Mike Ogah, kuma duka sun amsa laifin da ake tuhumar su da shi.

    Binciken jami'an tsaron ya kuma gano cewa mutanen biyu sun sace wa wani mutum kuɗin da ya kai naira 948,000 ta hanyar amfani da katinsa na bankin Fidelity da suka sace.

    'Yan sandan sun ce a halin yanzu mutanen biyu na hannunsu domin ci gaba da gudanar da bincike.

    Sanarwar ta kuma ce kwamishinan 'yan sandan jihar ya yaba wa jami'an tsaron sashen tattara bayanan sirrin kan kama mutanen.

    Sannan ya yi kira ga jama'a da su riƙa lura da irin mutanen da za su bai wa katinan ATM ɗinsu domin taimaka musu.

  14. Ƙasashen yamma sun yi kiran zaman lafiya a zaɓen Saliyo

    Tawagar wakilan ƙasashen Birtaniya da Amurka da Ireland da Jamus da Faransa da ƙungiyar Tarayyar Turai ta EU a zaɓen Saliyo da za a gudanar, sun yi kira ga al'ummar ƙasar da su guje wa tashin hankali, sannan su martaba ra'ayoyin juna, tare da guje wa yin kalaman da za su tunzura juna da kawo rarrabuwar kai, a yayin da ake shirin gudanar da babban zaɓen ƙasar ranar Asabar da ke tafe.

    A wata sanarwar haɗin gwiwa da wakilan ƙasashen suka fitar, sun bayyana damuwarsu kan rahotonnin rikice-rikicen siyasa da ake samu a ƙasar da ke yammacin Afirka.

    Wakilan sun yi kira ga jam'iyyun siyasa da 'yan takara da su yi biyayya ga yarjejeniyar zaman lafiya da suka sanya wa hannu cikin watan da ya gabata.

    Yarjejeniyar dai ta buƙaci jam'iyyu da 'yan takarar da su riƙa yin kira ga zaman lafiya, tare da gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali, sannan su garzaya kotuna domin gabatar da ƙorafin da suke da shi game da zaɓen.

    Tawagar wakilan manyan ƙasashen yamman sun jaddada goyon bayansu kan gudanar da ingantacce kuma sahihin zaɓe cikin kwanciyar hankali, kamar yadda al'ummar ƙasar ke buƙata.

    Ana samun ƙaruwar zaman ɗar-ɗar a fadin ƙasar, yayin da mazauna Freetown babban birnin ƙasar ke tururuwar sayen abinci da sauran kayayyaki a kasuwanni, sakamakon fargabar ɓarkewar rikici a ƙasar.

    Hakan na zuwa ne bayan da aka samu wata arangama tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan babbar jam'iyyar adawar ƙasar ranar Laraba, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda.

    Ƙasar Saliyo na fuskantar matsin tatalin arziki, da tsadar rayuwa, inda talauci da rashin aikin yi tsakanin al'umma ke ci gaba da ƙaruwa, baya ga hauhawar farashin kayayyaki.

    'Yan takara 13 ne za su fafata a zaɓen, to sai sai masu hasashe na ganin zaɓen zai fi zafi tsakanin manyan 'yan takar biyu, wato shugaban ƙasar Julius Maada Bio da ke neman wa'adin mulki na biyu, sai kuma Samura Kamara na babbar jam'iyyar adawa ta All People's Congress wato APC.

  15. Kun san farashin ragunan layya a Abuja?

  16. DSS ta bankaɗo barazanar kai hare-hare lokacin bukukuwan salla a Najeriya

    Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya - DSS ta ce 'yan ta'adda na shirin kai hare-hare a wuraren ibada da wuraren wasannin yara a lokutan bukukuwan babbar salla a ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na Twitter, ta shawarci masu kula da wuraren da al'umma ke zuwa ciki har da kasuwanni da manyan kantuna, da su riƙa lura da kai-komon mutane.

    Hukumar ta kuma yi kira ga jama'a da su kai rahoton duk wani abu da suke ganin ba su amince da shi ba, zuwa ga jami'an taro.

    Ya ce a wani samamen haɗin gwiwa da jami'an hukumar suka kai tare da sauran jami'an tsaro, sun ƙwato abubuwan fashewa daga hannu wasu 'yan ta'adda.

    Mista Afunanya ya ce sun samu nasarar kama wani mai safarar makamai a lokacin wani samame a kan babbar hanyar Abuja zuwa Keffi.

    Haka kuma sanarwar ta ce hukumar za ta ci gaba da aiki tare da sauran jami'an taro domin fatattakar ayyukan 'yan ta'adda a fadin ƙasar

  17. Mutum 31 sun mutu a mahaƙar ma'adinan Afirka ta Kudu

    Hukumomin Afirka ta Kudu sun ce sun samu labarin mutuwar akalla mutum 31 da ake zargi 'yan ƙasar Lesotho ne masu haƙar zinare ba bisa ƙa'ida ba, a tsohuwar mahaƙar ma'aidan ƙasar.

    Ma'aikatar ma'adinan kasar ta bayyana cikin wata sanarwa cewa gwamnatin Lesotho ce ta sanar da ita batun mutuwar mahaƙan ranar 18 ga watan Mayu a wani yankin da ake haƙar ma'adinai a ƙasar.

    Mahaƙar da ke garin Welkom a jihar Free ta daina aiki tun a shekarun 1990, in ji sanarwar.

    Ma'aikatar ta ce wasu masu haƙar ma'adinan ba bisa ƙa'ida ba, sun gano gawarwakin wasu mutum uku a mahaƙar.

    Inda ta ce tana aiki da masu ruwa da tsaki don kuɓutar da gawarwakin.

    Mummunan hatsari a mahaƙar ma'adinai ba sabon abu ba ne a Afirka ta Kudu, inda masu haƙar ba bisa ƙa'ida ba, ciki har da 'yan cirani ke sanya rayuwarsu cikin hatsari.

  18. Masu zanga-zanga kan audugar mata sun dakatar da zaman majalisa a Ghana

    Masu zanga-zangar da ke buatar cire haraji kan audugar mata a Ghana sun yi yunƙurin kutsawa majalisar dokokin ƙasar Alhamis.

    Jami'an tsaron sun tsayar da masu zanga-zangar, waɗanda ke sanye da jajayen tufafi riƙe da allunan da ke dauke da sakonnin bukatar cire haraji kan audugar matan, inda aka tara su a ƙofar shiga majalisar dokokin.

    Mutanen - waɗanda ke rera waƙoƙin ''Muna buƙatar yin al'adarmu cikin nutsuwa'', ''A cire haraji kan audugar mata'' - sun dakatar da zaman majaliar na ɗan lokaci.

    Masu zanga-zangar sun ce suna buƙatar gwamnati ta cire haraje-harajen da ake sanya wa audugar, lamarin da ke haddasa tsadarta a ƙasar.

    Masu rajin kare mata a ƙasar sun ce tsadar audugar na haifar da rashin zuwa makaranta ga 'yan mata, tare da ƙara ta'azzara rashin tsafta ga talakawan da ke zaune a yankunan karkara.

    To sai dai ƙungiyar masana'antun ƙasar (AGI)ta gargaɗi gwamnatin ƙasar da kada ta cire harajin.

    Tana mai nuni da cewa cire haraji kan shigo da audugar zai karya wa masana'antun cikin gida gwiwa wajen sarrafa audugar.

    Hukumar da ke kula da haraji ta ƙasar ta ce ana ɗaukar audugar mata a matsayin abubuwan da aka sarrafa, don haka ne ake dora mata haraji.

  19. NLC ta gargaɗi gwamnatin Najeriya kan ƙarin farashin lantarki

    Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta jingine shirinta na yin ƙarin kuɗin wutar lantarki da kashi 40 cikin 100 cikin wata mai zuwa.

    Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Joe Ajaero, ya fitar, ya ce matakin zai ƙara wa 'yan ƙasar musamman talakawa ''wahalhalu da matsin da suke ciki''.

    Kafofin yaɗa labaran Najeriya sun ruwaito hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta kasar NERC na shirin ƙara kuɗin wutar daga ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa.

    A wani mataki na janye tallafin da gwamnatin ƙasar ke biya kan kudin wutar lantarkin.

    BBC ta tuntuɓi hukumar ta NERC, don jin bahasinta kan matakin, to amma jami'in hulɗa da jama'a na hukumar Michael Faloseyi ya ce ba a ba shi izinin yin magana kan batun ba.

    'Yan ƙasar da dama sun bayyana kaɗuwarsu kan matakin ƙarin kuɗin wutar lantarkin, suna masu fargabar cewar zai haifar musu da ƙarin matsin tatalin arziki.

    A watan da ya gabata ne gwamnatin ƙasar ta sanar da matakin janye tallafin man fetur, lamarin da ya haddasa ƙaruwar farashin man fetur da na kayan abinci a faɗin ƙasar.

  20. Alaƙa na kyautata tsakanin Indiya da Amurka

    Firaminitan Indiya, Narendra Modi ya nuna gamsuwarsa, kan alaƙar ƙasarsa da Amurka.

    Mista Modi ya bayyana hakan ne yayin wani jawabi da ya gabatar wa haɗakar zaurukan majalisun ƙasar a birnin Washington DC.

    Ya ce a yanzu ƙasashen biyu na son kyautata alaƙar haɗin gwiwa tsakaninsu.

    Jami'an gwamnatin Amurkan sun yi ta yi masa tafi da jinjina yayin gabatar da jawabin, wani abu da ba a saba gani ba yayin da aka karɓi baƙuncin wani babban baƙo.

    Shugaban na Indiyan, ya ce a yanzu zamanin zaman doya da manja tsakanin ƙasashen biyu ya zama tarihi, wani abu da ake kallo tamkar koma-baya ne ga ƙasar China.

    Da yawa daga cikin mambobin jam'iyyar Democrat sun ƙaurace wa jawabin nasa, don nuna damuwa kan take hakƙin ɗan adam da suke zargin ana samu ƙarƙashin mulkinsa a Indiya.