Sojoji sun ƙalubalanci Dokubo ya bayyana sunayen masu satar ɗanyen man fetur
Rundunar sojin ruwan Najeriya ta ƙalubalanci tsohon jagoran masu fafutika na yankin Neja Delta, Mujahid Asari Dokubo da ya bayyana sunayen jami’an da ke satar ɗanyen mai.
A ranar Juma'a ne Asari Dokubo ya yi zargin cewa akwai hannun sojojin Najeriya na ruwa a yawancin laifukan satar mai da ake samu a yankin Neja-Delta.
Dokuba ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan ganawarsa da shugaba Bola Tinubu.
Sai dai yayin da yake mayar da martani, mai magana da yawun rundunar sojin ruwan Najeriya, Commodore Adedotun Ayo-Vaughan, ya bayyana zargin a matsayin maganar da babu gaskiya a cikinta.
Ya ce ɓarayin mai sun fusata ne saboda sojojin ruwan Najeriya da ɗaukacin sojojin na ci gaba da hana su hanyoyin da za su yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta hanyar wani shiri na dakatar da ayyukan ɓarayi.
Ya ci gaba da cewa rundunar sojin ruwa tare da hadin guiwar masu ruwa da tsaki za su ci gaba da hana ɓarayin danyen mai hanyoyin yin zagon kasa ga tattalin arzikin Najeriya.
A wata hirar da ya yi da jaridar Daily Trust, Ayo-Vaughan,ya ce “Ya kamata ya kawo sunayen. Rundunar sojin ruwan Najeriya na buƙatar samun sunayen waɗanda abin ya shafa domin rundunar ba za ta ɗauki duk wani nau’in aikata laifuka ba ko da kuwa ta kai girman sata irin yadda Asari Dokubo yake zargin''.
“Saboda haka, sojojin ruwa suna yaƙar satar mai. Duk wanda zai yi irin wannan zarge-zargen, sai ya kawo sunayen. Shi (Dokubo) yana yankin Neja-Delta, ai yana da yara a yankin Neja Delta''.