Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kuɗin masaukai ya yi tashin gwauron zabo a Makkah

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba and Mukhtar Adamu Bawa

  1. A yi sahur lafiya!

    Masu bibiyarmu a wannan shafi na kai tsaye, a nan za mu dasa aya, sai kuma gobe da safe idan Allah Ya kaimu.

    Nabeela Mukhtar Uba, amadadin Abdullahi Diginza da Haruna Kakangi da Mukhtar Adamu Bawa, ke cewa ku kasance lafiya.

  2. Mata kusan 30 na mutuwa sanadin kansar bakin mahaifa a Najeriya

    Cibiyar bincike kan ayyukan likitanci a Najeriya ta ce duk da matakan rigakafin da ake ɗauka, mata 28 na mutuwa duk rana sanadin cutar kansar mahaifa a ƙasar.

    Cibiyar ta yi magana kan buƙatar yi wa ƴan mata rigakafi da kuma tantance mata domin cike giɓin da ake da shi.

    Da yake magana a wani taro don yin ƙarin haske kan ƙaruwar annobar a tsakanin ƴan mata da mata, Daraktan cibiyar, Farfesa Oliver Ezechi, ya yi kira ga gwamnatoci a matakai daban-daban da su riƙa ɗaukar al'amuran da suka shafi lafiyar mata da muhimmanci.

    Da yake jaddada cewa ana iya kare samuwar cutar, Farfesa Ezechi ya bayyana cewa kansar bakin mahaifa ita ce nau'in kansar da ta fi ƙamari a tsakanin mata.

    Ya ce "duk shekara, ana gano mata kimanin mata 12,000 a Najeriya ɗauke da cutar kuma kusan 8,000 na mutuwa sanadiyyarta. A kowacce rana, kimanin mata 28 ne ke mutuwa sakamakon kansar mahaifa."

  3. Kuɗin masaukai ya yi tashin gwauron zabo a Makkah

    An samu ƙarin farashin ɗakunan otal-otal da ke Makkah a watan Ramadan na bana.

    Shi ne farashi mafi tsada cikin shekara uku, inda ya kai kashi 80 cikin 100 kamar yadda yake a ƙididdigar da hukumar kula da aikin hajj da umrah ta Makkah ta fitar.

    Farashin otal ɗin a azumin bana ya ƙaru saboda yawan buƙata musamman a cikin kwana 10 na ƙarshen watan.

    Wani nazari da Al-Eqtisadiah business daily ta yi game da karɓar otal a tsakiyar birnin Makkah cikin goman ƙarshe na Ramadana, farashin ya kai tsakanin SR3,000 zuwa SR9,000 a kullum, idan dakin otal ɗin za a yi amfani da shi ne a cikin goman ƙarshe.

    Shugaban hukumar, Abdullah Al-Qadi ya ce farashin ɗakunan otal ɗin ya ta'allaƙa ne a kan wasu batutuwa, da kuma ƙarin buƙata da kasancewar kusancin wajen da masallacin Harami.

    Ya ce abin da ya bambanta farashin ɗakunan otal ɗin a Makkah shi ne kasancewar ɗakunan suna tsakiyar birnin Makkah inda farashinsu kan tashi idan azumi ya gabato, sannan kuma su ninka a goman ƙarshe na watan.

  4. Gwamnatin Kaduna ta haramta taruka a unguwar da ta sa dokar hana fita

    Gwamnatin jihar Kaduna ta haramta duk wasu harkokin jama'a masu alaƙa da tashin hankalin da ya faru a daren Lahadi da Litinin wanda har mutum biyu suka mutu.

    Haka zalika, akwai ƙarin mutum shida kuma da suka jikkata a Sabon Garin-Tirkaniya da ke ƙaramar hukumar Chikun.

    An dauki matakin ne bayan nazarin da hukumomin tsaro kamar ƴan sanda da sojoji da jami'an tsaron farin kaya suka yi, da kuma wani taron gaggawa tsakanin shugabannin addinai da sarakunan yankin.

    Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna ne ya bayyana haka a sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

    Sanarwar ta ambato abubuwan da aka haramta da suka hadar da Kidan Bishi da Kidan Gala da farauta.

    Gwamnati ta kuma ba da umarnin a kama duk wani mai ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a Nasarawa da Sabon Garin Nasarawa.

    A cewar sanarwar, an kama mutum uku da ke da hannu a tashin hankalin, wanda ya yi sanadin lalata motoci da dama da dukiya.

    Gwamna Nasir El Rufai ya yaba da yadda sojoji da ƴan sanda suka yi azamar daƙile ruruwar tashin hankali a yankin.

  5. Tinubu ne zai yanke shawara kan cire tallafin man fetur

  6. Kusan tan 600,000 na nama ne ke lalacewa duk shekara a Saudiyya

    Hukumar Kula da Inganci da Tsaftar Abinci ta Saudiyya (GFSA) ta ce kusan tan 600,000 na nama ne yake lalacewa duk shekara a ƙasar.

    Hukumar ta faɗi hakan ne lokacin da take bayyana yawan nama da kajin da aka yi asara ko suka lalace a ƙasar.

    GFSA ta ce nama na ɗaya daga cikin abinci mai muhimmanci a ƙasar, to amma ta ce ana barin da yawa yana lalacewa.

    Fiye da tan 444,000 na naman kaji ne ya lalace, yayin da fiye da tan 110,000 na sauran naman dabbobi ya lalace a bana.

    Hukumar ta kuma ce ɗaya daga cikin dalilan da suke janyo lalacewar naman shi ne sayensa da ake yi da yawa, ba tare da an yi amfani da shi ba, sannan kuma da dafa abincin da ya fi ƙarfin buƙata.

  7. Babu hannun gwamnatin Yobe wajen zubar wa mata ciki - NHRC

    Hukumar kare haƙƙin bil-adama ta Najeriya ta ce babu hannun gwamnatin jihar Yobe a zargin da wai rahoto na kamfanin dillancin labaran Reuters ya yi da ke cewa gwamnatin ta haɗa baki da sojoji wajen zubarwa da wasu mata ciki a asirce.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Tuwita, hukumar ta ambato gwamnatin Yobe na cewa wannan zargi, abu ne da tunani ko hankali ma ba za su ɗauka ba.

    A watan Disamban 2022 ne, Reuters ya wallafa wani rahoto, inda ya zargi sojojin Najeriya da hannu wajen zubarwa da mata akalla 10,000 ciki a asirce.

    Kwamishinan shari’a na jihar Saleh Samanja ne ya bayyana haka ga kwamitin bincike na hukumar kare haƙƙin bil-adama a lokacin da suka ziyarci jihar.

    Don gudanar da bincike kan zarge-zargen take haƙƙin bil adama a yankin arewa maso gabashin ƙasar,

    Kwamishinan ya ƙara da cewa babu wata gwamnati da za ta yarda a haɗa baki da ita wajen kashe mata da ƙananan yara da sunan kore tsangwamar da suke fuskantar na kasancewa da ‘yan Boko Haram.

  8. MDD ta zargi Sudan ta Kudu da take haƙƙin bil-adama

    Jami'an kare haƙƙin bil-adama na Majalisar Dinkin Duniya sun zargi manyan jami'an gwamnatin Sudan ta Kudu kan laifin take haƙƙin ɗan adam a ƙasar ciki har da ƙaruwar hare-hare kan fararen hula, da kashe-kashe da yawaitar fyaɗe.

    Kusan mutum 400,000 ne suka mutu a lokacin yaƙin basasar ƙasar, kafin a cimma yarjejeniyar zaman lafiya a shekarar 2018.

    To amma rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce ƙasar ta kasa kare fararen hula tare da magance take haƙƙin ɗan adam.

    Daga cikin waɗanda aka naɗa a matsayin masu shigar da ƙara a ƙasar, har da gwamnan jihar Unity, Joseph Monytuil da kuma Laftanar Janar Thoi Chany Reat na rundunar sojin ƙasar.

    Yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a shekarar 2018 ta kawo ƙarshen yaƙin basasar ƙasar.

    To sai dai har yanzu ƙasar na fama da rashin zaman lafiya.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawaitar tashe-tashen hankali a faɗin ƙasar na kawo tarnaƙi ga zaman lafiyar ƙasar.

  9. Yau aka cika shekara 50 da fara magana ta wayar salula

    A yau ne ake cika shekara 50 da yin magana da wayar hannu ta farko a duniya.

    Martin Cooper wani Injiniya,Ba'amurke shi ne mutumin da ya fara magana da wayar hannun ranar 3 ga watan Afrilun 1973.

    Shekara 11 bayan wannan rana kamfanin Motorola ya ƙera wayar hannu ta farko ƙirar 8000X a shekarar 1984.

    Wayar farko da kamfanin ya ƙera mai nauyin giram 790, wato ninki huɗu kan nauyin wayar iPhone 14.

    Kuma kira kawai ake yi da wayar, ba ta aika rubutaccen saƙo, ko amfani da wasu abubuwa.

    Wayar Motorolar ta farko kan ɗauki sa'o'i 10 tana chajin batirinta, yayin da kuma chajin ke ƙarewa cikin mituna 30.

  10. Finland za ta shiga ƙungiyar tsaro ta NATO

    A ranar Talata ƙasar Finland za ta zama mamba a ƙungiyar tsaro ta NATO, kamar yadda sakataren ƙungiyar ya bayyana.

    A watan Mayun bara ne Finland da Sweden suka buƙaci shiga ƙungiyar bayan mamayar da Rasha -wadda suka haɗa kan iyaka da Finland- ta yi wa Ukraine.

    To sai dai Turkiyya ta riƙa jan ƙafa wajen amince wa ƙasashen shiga ƙungiyar, bayan ta yi ƙorafin cewar ƙasashen na goyon bayan 'yan ta'adda.

    Daga cikin dokokin shiga ƙungiyar dole ne kowacce mamba sai ta amince da buƙatar kowacce ƙasa da ke buƙatar shiga ƙungiyar.

    "An kammala duka matakan da suka dace domin shigar Finland ƙungiyar Nato'' in ji sakataren ƙungiyar.

    Ƙasar za ta zama ta 31 a cikin mambobin ƙungiyar tsaro ta NATO.

    An dai kafa ƙungiyar tsaro ta NATO a shekarar 1949, mai mambobi 30 daga Turai da Amurka, domin kare al'umomin ƙasashen ƙungiyar.

  11. Kotu ta bayar da belin shahararren mawakin Najeriya, Portable

    Wata kotun majistare da ke jihar Ogun ta bayar da belin shahararren mawakin Najeriya, Habeeb Okikiola, wanda aka fi sani da Portable, bayan gurfanar da shi a gabanta a yau Litinin.

    Rundunar ƴan sandan Najeriya ce ta gurfanar da shi a kotu bisa zargin sa da far ma wani.

    Sai dai wanda ake zargin ya musanta tuhumar da aka karanta masa.

    Lokacin da ya yanke shari’a, alƙalin kotun, A.S Shoneye ya ce za a iya bayar da belin wanda ake tuhuma da irin wanna laifi.

    A kan haka ne ya bayar da belin nasa kan kudi N300,000 da kuma mutum biyu da za su tsaya masa.

    Sai dai kotun ta bayar da umurnin tsare Portable a gidan gyaran hali har sai ya cika ƙa’idojin belin.

    Yanzu haka kotun ta ɗage sauraron ƙarar har sai ranar 26 ga watan Afrilu.

  12. Yadda ake yin gasasshen burodi da shayi a sauƙaƙe

  13. Farashin man fetur ya tashi a kasuwar duniya

    Farashin ɗanyen man fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan da manyan ƙasashe masu arzikin man fetur suka bayyana rage adadin man da suke fitarwa.

    Farashin ya ƙaru da fiye da kashi biyar cikin ɗari, inda ya kai sama da dala 84 a kan kowacce ganga.

    Ƙaruwar farashin na zuwa ne bayan ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta OPEC suka ayyana cewa za su rage yawan man da suke fitarwa zuwa kasuwar da fiye da ganga miliyan ɗaya a kowacce rana.

    Ko a watan Fabrairun bara ma, sai da farashin man ya tashi, bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.

    To sai dai sannu-a-hankali farashin ya ci gaba da sauka, inda har ya koma yadda yake kafin mamayar.

    Masu sharhi na cewa ƙaruwar farashin zai kawo cikas, a ƙoƙorin da duniya ke yi wajen rage hauhawar farashin kayayyaki.

  14. Mutum 19 sun mutu a zaftarewar ƙasa a DR Congo

    Jami'ai a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo sun ce zaftarewar ƙasa ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 19 a ƙasar.

    Wani jami'i a ƙauyen Bulwa na arewacin lardin Kivu ya ce akwai yiwuwar yawan mamatan zai iya ƙaruwa.

    Ya ƙara da cewa, ana fargabar ƙasa ta danne wasu gungun mata da ƙananan yara a lokacin da suke wanki a bakin wata ƙorama a yankin.

    An ci gaba da aikin ceto a yau Litinin.

    Yankin dai na fama da mamakon ruwan sama cikin watannin baya-bayan nan, lamarin da ya haifar da ambaliyar ruwa tare da zaftarewar laka.

  15. An sanya dokar hana fita a wani yanki na birnin Kaduna

    Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta sanya dokar hana fita ta s'o'i 24 a unguwannin Sabon Garin Nassarawa da Tirkaniya a yankin ƙaramar hukumar Chikun.

    A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar, ya ce an ɗauki matakin ne bayan wani rikici na 'yan sara-suka da ya kaure, da ya yi sanadin mutuwar mutum biyu.

    Sanarwar ta kuma umarci jami'an tsaro da su tabbatar da dokar a unguwar, domin maido da zaman lafiya, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano musabbabin abin da ya haddasa hargitsin.

    A domin haka ne kwamishinan ya yi kira ga mazauna yankin da su yi biyayya ga dokar hana fitar, wadda ta fara aiki nan take.

  16. Bankin Duniya ya nuna damuwa kan bashin da China ke bai wa Afirka

  17. An rufe wata makaranta a Kenya bayan mutuwar ɗalibai

    Hukumomi a Kenya run rufe wata makaranta a yammacin ƙasar bayan mutuwar ɗalibai biyu, da ake zargin cewa sun mutu ne sakamakon cin abinci da ruwan sha masu guba.

    Jami'an lafiya a ƙasar sun rufe makarantar 'yan matan da ke gundumar Kakamega, bayan da aka kai ɗalibai sama da 100 asibiti a makon da ya gabata kan ciwon ciki da kuma gudawa.

    Binciken farko ya nuna cewa ɗaliban sun ci abinci ko shan ruwan da ke da guba a ciki ne.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce an ɗauki samfurin abincin zuwa cibiyar bincike ta ƙasar domin gano abin da ke cikin

    Tun bayan mutuwar daliban biyu ne dai iyayen yara suka fara tururuwa zuwa makarantar domin kwashe 'ya'yansu.

  18. EFCC ta kama masu zamba ta intanet

    Hukumar da ke Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Najeriya Ta'annati EFCC ta kama tsohon mai aikata zamba ta intanet tare da ƙarin wasu mutum 17 bisa laifin zamba ta intanet.

    A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce ofishin hukumar reshen Ibadan ne ya gurfanar da mutanen a gaba kotu.

    Kotun dai ta same su da laifi, inda ta yanke musu hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari.

  19. A yanzu Abba Gida-gida ba shi da iko a hukumance - Masana

    Masana harkokin shari’a a Najeriya sun ce sa toka-sa-katsin da ya kunno kai tsakanin zaɓaɓɓen gwamnan Kano da gwamnan jihar mai barin gado a kan batun filaye da bai wa gwamnatin jihar rance, ba ya rasa nasaba da ƙudurin gwamnati da na siyasa.

    Masana shari’ar na da ra’ayin cewar duk da yake Injiniya Abba Kabir Yusuf na da damar ba da shawara, amma ba shi da ikon ba da duk wani umarni har sai ranar da aka rantsar da shi a matsayin gwamna.

    Barista Abba Hikima Fagge ya ce ‘’A idon doka, shi gwamna mai jiran gado ba shi da hurumi, ko wani iko da tsarin mulkin ƙasa ya ba shi’’

    ‘’Ikon da tsarin mulkin Najeriya ya ba shi yana farawa ne daga ranar da ka rantsar da shi, amma daga yanzu har zuwa ranar da za a rantsar da zaɓaɓɓen gwamnan, ba shi da iko".

    Abba Hikima ya kuma ce daga ranar da aka sanar da mutumin da ya ci zaɓen gwamna, har zuwa ranar rantsar da sabuwar gwamnati, gwamna mai barin gado yana da ikon gudanar da duk abin da ya ga damar yi da ofishinsa.

    Ya kuma ce duk yarjejeniyar da gwamnati mai ci ta shiga ko ta zartar a wannan lokaci halastacciya ce.

    Sai dai kuma, gwamnati mai jiran gado in ji shi, tana da damar da za ta warware duk yarjejeniyar da aka cimma kafin zuwanta kan mulki.

    To amma, Barista Muhammad Shu’aibu, wani lauya mai zaman kansa a Abuja ya ce duk wata yarjejeniya da gwamnati mai barin gado ta shiga, matuƙar an yi ta bisa ƙa’ida to babu abin da zai iya tayar da ita.

    ‘’Amma matuƙar ba a bi ƙa’idoji wajen aiwatar da yarjejeniyar ba, to sabuwar gwamnati, za ta iya zuwa ta ce ita wannna abin bai shafe ta ba’’ in ji shi.

    Ya kuma ce wanda yarjejeniyar ta shafa zai iya zuwa kotu don neman haƙƙinsa.

    To amma a cewar lauyan wanda zai kai ƙarar yana iya gamuwa da cikas, matuƙar yarjejeniyar da ya ƙulla da gwamantin da ta bar gado, ba a yi ta bisa ƙa’ida da doka ba.

    Tun a makon jiya ne, aka fara samun turka-turka tsakanin gwamnan Kano mai jiran gado da takwaransa gwamna mai barin gado dangane da wasu batutuwa da suka shafin tafiyar da jihar.

    Bayan wata sanarwa da gwamnan mai jiran gado ya fitar ta hannun sakataren yaɗa labaransa wadda a ciki yake shawartar mutanen da ke gine-gine a filayen gwamnatin jihar, su dakata,

    Daga baya kuma ya ƙara fitar da wata sanarwar, inda yake shawartar masu shirin bai wa gamnatin jihar bashi, su ma dakata.

    Sai dai a nasa ɓangaren gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gargadi gwamna mai jiran gado ya daina fitar da sanarwar hukuma da sunan shawara.

    Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar Mohammed Garba ya fitar, ta ce abin da Abba Kabir Yusuf ke yi riga-mallam-masallaci ne.

  20. Fiye da mutum 80,000 ne ke buƙatar tiyatar zuciya duk shekara a Najeriya- Masana

    Ƙungiyar ƙwararrun likitocin zuciya da jijiyoyin jini ta Najeriya (ACTSON) ta ce 'yan ƙasar fiye da 80,000 ne ke buƙatar tiyatar zuciya kowacce shekara.

    Shugaban ƙungiyar, Dakta Uvie Onakpoya ne ya bayyana haka a Abuja baban birnin ƙasar, lokacin taron ƙungiyar na shekara-shekara.

    Ya ce cutukan da ke da alaƙa da zuciya da jijiyoyin jini ne kan gaba wajen haddasa yawan mace-mace fiye da kowacce cuta a duniya.

    Dakta Onakpoya ya ce takwas cikin duk yara 100 da aka haifa, na ɗauke da cutukan da suka shafi zuciya.

    Ya ƙara da cewa a Najeriya fiye da yara 55,000 ake haifa da cutar zuciya duk shekara.

    Shugaban ƙungiyar likitocin zuciyar ya ce a bara, mutum 212 ne kaɗai aka yi wa tiyatar zuciya, saboda tsadar tiyatar da sauran matsaloli.

    Dakta Onakpoya ya ce ƙungiyar ta sha kira ga hukumomin Najeriya a kan su kafa dokar da za ta sauƙaƙa yin tiyatar zuciya.

    A cewarsa, ta yadda masu jinyar za su samu sauƙi wajen zuwa asibitocin gwamnati da masu zaman kansu don yi musu tiyatar.