Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gwamnatin Zamfara ta sanya dokar hana zirga-zirga a jihar

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Shugaba Buhari ya ce ya matsu ya sauƙa daga mulki

    Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya ƙagara ya sauƙa daga mulkin Najeriya, kamar yadda ya sha nunawa a baya cewa ya matsu ya ga ranar 29 ga watan Mayu domin ya miƙa mulki ga magajinsa.

    Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a ganawar ban-kwana da jakadiyar Amurka mai barin-gado, a Najeriya, Mary Beth Leonard, a fadar shugaban, da ke Abuja a yau Talata.

    Buhari ya furta hakan ne yayin mayar da jawabi ga jakadiyar kan tambaya da ta yi masa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Shugaban shi ma mai barin-gado ya ƙara da cewa yana son ya koma ya mayar da hankalinsa kan kula da gonakinsa da kuma dabbobinsa sama da 300 a Daura idan ya sauƙa daga mulki.

    Buhari, wanda ya nuna gamsuwa da irin sha'awar da 'yan Najeriya suka nuna kan dumukuraɗiyya ta hanyar waɗanda suka zaɓa a zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisun dokoki na tarayya da zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisun dokoki na jihohi da aka kammala, ya ce lalle dumukuraɗiyyar ƙasar ta bunƙasa.

    Ya ce mutane sun fahimci ƙarfi da ikon da suke da shi, waɗanda idan aka ba su damar zaɓe cikin walwala da adalci ba wanda zai gaya musu abin da za su yi.

    ''Na yi farin ciki da yadda wasu ƴan takara suka faɗi a zaɓen, '' in ji Buhari.

    Ya ce sakamakon canjin kuɗi da gwamnatinsa ta yi ba a samu kuɗin da za a ba masu zaɓe ba, wanda kuma duk da hakan ma ya ce mutane su karɓi kuɗin amma su zaɓi wanda ya kwanta musu a rai, in ji shi.

    Shugaban ya ce ya ji daɗi yadda bai yi katsa-landan a harkar zaɓen ba.

  2. Tauraron fim ya janyo ce-ce-ku-ce a Masar da cewa zaman gida ne ya dace da mata

    Kafofin watsa labarai da shafukan intanet da dama sun ruwaito wani tauraron fim a Masar na cewa shi bai yarda a ce mata na zuwa aiki ba, kamata ya yi su zauna a gida su kula da yara.

    Kalaman nasa sun janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta da muhawara musamman ma a tsakanin fitattun masu fashin baƙi.

    Daga cikinsu wani marubuci Ibrahim Eissa, ya mayar da martani inda ya ce ba aiki ba ma, mata sun cancanci jagorantar ƙasa.

    Kafofin watsa labarai sun riƙa nuni da irin kalaman da shugaban ƙasar Abdul Fattah al-Sisi, ya yi a lokacin bikin ranar mata ta duniya da aka yi kwanan nan dangane da muhawarar da kalaman tauraron fin ɗin suka janyo.

    Al-Sisi ya ce mata sun cancanci samun ƙarin wakilci sosai a dukkanin ɓangarorin rayuwar jama'a da kuma samun ci gaba da zai kai ga albashi dai-dai da maza.

  3. Ina aka kwana game da zaben gwamna a Adamawa da Abia da Kebbi da Enugu?

  4. Eritrea da Ethiopia sun yi watsi da zargin laifin yaƙi da Amurka ta yi musu a Tigray

    Eritrea ta bi sahun Ethiopia wajen sukar Amurka kan ɗora musu laifin yaƙi da ta ce an aikata lokacin yaƙin basasa na shekara biyu a yankin Tigray.

    A jiya Litinin ne Sakataren harkokin Wajen Amurka Antony Blinken, ya ce dakarun Ethiopia da na Eritrea tare da na Amahara sun aikata laifukan cin zarafin dan'Adam.

    Amma kuma bai ambaci mayaƙan ƴan tawaye na Tigray da wasu da suka mara musu baya ba wajen aikata laifin yaƙin.

    Eritrea ta ce kalaman Mista Blinken ɓata suna ne, yayin da ma'aikatar harkokin wajen Ethiopia ta bayyana zargin na Amurka a matsayin nuna ɓangaranci, wanda ta ce bai dace ba kuma bai kamata ba.

    A makon da ya gabata ne Anthony Blinken ya kai ziyararsa ta farko Ethiopia, tun bayan da aka ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya a watan Nuwamba na bara tsakanin gwamnatin tarayya ta habasha da ƴan tawaye na yankin Tigray.

  5. EFCC ta kama mutum 21 kan zargin zamba ta intanet

    Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin Najeriya zagon-ƙasa, EFCC, ta ce ta kama mutum 21 a babban birnin jihar Edo, Benin a yau Talata 21 ga watan Maris, 2023.

    A sanarwar da ta sanya a shafinta na Twitter, hukumar ta ce jami'anta sun yi wa mutanen dirar mikiya ne da sanyin safiyar yau Talata bayan wasu bayanai da ta samu na sirri.

    Ta bayyana sunayen mutanen kamar haka Alakpa Marvelous da Hoghomhen Jude Moses da Christopher Odion da Azanuwna Joseph da Godfirst Christopher da Eghosa Osaretin da Onus Honda da Barnabas Alakpa.

    Sauran su ne, Junior Azanuwna da Ehis Inegbinebor Francis da Godbless Eriugo da Imokhai Dickson da Epama Francis da Ekuma Austin da kuma Sunday Stanley.

    Ragowar su ne Kelly Alakpa da Amiole Paul da Iweriebor Raphael da Sunday Christian da Imozemhe Raymond da kuma Agbonghae Anthony.

    Kayan da aka ƙwace a hannunsa sun haɗa da motoci ƙirar Marsandi biyu da Lexus ES 350 biyu da wata Lexus RX 330 guda ɗaya da Toyota Camry guda ɗaya da kuma kwamfyutoci samfurin HP tare da wayoyin hannu.

    EFCC ta ce mutanen sun bayar da bayanai masu muhimmanci kuma nan da wani ɗan lokaci za ta gurfanar da su a gaban kotu.

  6. Gwamnatin Zamfara ta sanya dokar hana zirga-zirga daga dare zuwa safiya

    Gwamnatin jihar Zamfara ta sanya dokar hana zirga-zirga ta dare da rana bayan bayyana sakamakon zaɓen gwamnan jihar.

    Gwamnan jihar mai ci Bello Matawalle na APC ya sha kaye a ƙoƙarinsa na neman wa'adi na biyu a hannun abokin hamayyarsa na PDP, Dauda Lawal Dare.

    A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai Ibrahim Dosara ya fitar ya ce an ɗauki wannan mataki na sanya dokar ne domin daƙile duk wani tashin hankali.

    A sanarwar ya ce gwamnati ta lura tare da nuna takaici da damuwa kan yadda wasu suka lalata kaya da dukiyar gwamnati da kuma jikkata wasu mutane da sunan murnar cin zaɓe a jiya Litinin.

    Kwamishinan ya ce domin kare ci gaban hakan gwamnati ta ga ya zama dole ta sanya dokar hana fita daga ƙarfe 8 na dare zuwa 6 na safe har sai zaman lafiya ya dawo.

  7. Ya kamata Najeriya ta hukunta wadanda suka yi wa masu zabe barazana - Amurka

    Amurka ta yi kira ga hukumomi a Najeriya su gurfanar da mutanen da suka yi wa masu zabe barazana inda suka yi yunkurin hana su jefa kuri'a a zaben gwamna da yan majalisar dokoki na jihohi da aka yi ranar Asabar.

    Ofishin jakadancin Amurka ta ce an samu irin wannan matsala a Legas da Kano da wasu jihohin da aka gudanar da zaben.

    Ita ma tawagar Tarayyar Turai da ta sa ido kan zaben ta ce jihar Legas na daga cikin jihohin da aka samu tashin hankali da satar akwatin zabe da kuma yi wa masu zabe da ma'aikatan zabe da masu sa ido da kuma yan jarida barazana.

    Kimanin mutum 21 tawagar ta EU ta ce an kashe sakamakon tashin hankalin da aka yi a lokacin zaben.

    Karanta karin bayani a nan

  8. Ba mu yarda da sakamakon zaɓen Kano ba – APC

  9. Habasha ta zargi Amurka da ɗora mata laifukan yaƙi

    Gwamnatin Habasha ta zargi Amurka da rashin yi mata adalci ta hanyar ɗora mata zargin aikata laifukan yaki a yaƙin basasar da aka shafe shekaru biyu ana gudanarwa.

    A ranar Litinin ne sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya zargi sojojin gwamnatocin ƙasashen Habasha da Eritrea da mayakan yankin Amhara da laifukan yaƙi.

    To amma bai zargi mayaƙan TPLF na yankin Tigray da aikata laifukan yaƙin ba.

    Ma’aikatar harkokin wajen Habasha ta bayyana abinda Amurkar ta yi da cewa rashin adalci ne, kuma abu ne da ba za a taɓa amincewa da shi ba.

  10. Saudiyya ta fara duba jinjirin watan Ramadan

  11. An ci gaba da harkoki bayan ɗage dokar hana fita a Kano, Daga Zaharaddeen Lawan

    A jihar Kano da ke arewa maso yammcin Najeriya al'umma sun ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, bayan da gwamnatin jihar ta ɗage dokar hana zirga-zirga da ta sanya a wasu sassan jihar.

    A ranar Litinin ne gwamnatin jihar ta sanya dokar a wani mataki na kauce wa tashin hankali bayan da aka sanar da sakamakon zaɓen gwamna jihar ta Kano.

    Bayan bayyana sakamakon zaɓen ne kuma matasa suka fantsama kan tituna don nuna murna game da sakamakon da INEC ta ce Abba Kabir Yusuf ne ya samu nasara.

    Kwamishinan yaɗa labaran na jihar Muhammad Garba ya ce dama an sanya dokar ne domin kare ɓarnar da masu murnar lashe zaɓe za su aikata, dan haka a cewarsa dama an sanya dokar ne na ɗan lokaci.

    Ya ƙara da cewa gwamnati ta ɗage dokar ne bayan da ta yi tuntuɓa da masu ruwa da tsaki a harkar tsaron jihar, sannan kuma ta fahimci cewa al'amura sun lafa.

    A cewarsa ɗage dokar zai bayar da dama ga mutane su fito dan yin sayayya kasancewar watan azumi ya kusa kamawa.

    Wakilin BBC da ya zagaya birnin na Kano ya ce tuni al'ummar jihar suka fito don ci gaba da harkokin yau da kullum, ‘yan kasuwa da ma’aikatan gwamnati da gidajen mai da sauran masu sana'o'i sun ci gaba da harkokinsu.

  12. Kenya ta karɓi ton 30,000 na alkama daga Ukraine

    Ƙasar Kenya ta karɓi kusan tan 30,000 na alkama daga ƙasar Ukraine domin taimaka wa iyalan da tsananin fari da yunwa suka tagayyara a ƙasar.

    Kayan na daga cikin tallafin da Ukraine ta alƙawarta bai wa ƙasar.

    Mataimakin shugaban ƙasar Kenya Rigathi Gachagua, wanda ya karɓi kayan a lokacin da suka isa ƙasar, ya ce za a rabar da tallafin zuwa ga aƙalla mutum miliyan 5.4 da ke fama da tsananin yunwa.

    Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ce ta taimaka wajen isar da kayan zuwa ƙasar.

    Ƙasashe da dama ne suka ɗauki nauyin shirya tallafin ciki har da Norway da Belgium da Italiya da jamhuriyar Czech da kuma Birtaniya.

    Shirin ya samar da fiye da tan 140,000 na alkama zuwa ƙasashen Afirka tun watan Nuwamban 2022.

  13. Yadda matan PDP suka yi zanga-zangar adawa da sakamakon zaɓen jihar Nasarawa

    Mata 'yan jam'iyyar PDP mai hamayya a jihar Nasarawa sun gudanar da zanga-zanga kan sakamakon zaɓe.

    Suna zanga-zangar ne don nuna rashin jin daɗinsu kan yadda hukumar INEC a jihar ta ayyana AA Sule na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

    Matan na gudanar da zanga-zangar ce ƙarƙashin jagorancin shugaban mata ta jam'iyyar jihar Stella I Oboshi.

    Matan sun ce za su yi tattaki zuwa ofishin hukumar zaɓen jihar don nuna ɓacin ransu dangane da sakamakon zaɓen jihar.

    Matan dai na buƙatar INEC ta bayyana sakamakon zaɓen gwamnan jihar a matsayin wanda bai kammala ba saboda mazabun mazaɓun Gayan da Chiroma a ƙaramar hukumar Awe

  14. Lokaci ya yi da zan zama shugaban majalisar dattawa - Kalu

    Mai tsawatarwa na zauren majalisar dattawan Najeriya, Orji Kalu ya ce lokaci ya yi da zai zama shugaban majalisar dattawan ƙasar.

    Yayin da yake magana da manema labarai a harabar majalisar dokokin ƙasar, ɗan majalisar dattawan mai wakiltar mazaɓar Abia ta Arewa ya buƙaci jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar da ta ware wa yankinsa kujerar shugaban majalisar dattawan ƙasar.

    A matsayinsa na mai tsawatarwa na majalisar dattawan ƙasar a ƙunshin majalisa ta tara, Mista Kalu ya ce shi ne sanata mafi girman matsayi daga yankin kudu maso gabashin ƙasar, dan haka shi ne ya dace da muƙamin.

    Kawo yanzu dai jam'iyyar APC ba ta sanar da shiyyoyin da za ta ware wa muƙaman shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilan ƙasar ba.

    To sai dai tuni wasu zaɓaɓɓun 'yan majalisun suka fara bayyana sha'awarsu ta ɗarewa waɗannan muƙamai masu matuƙar muhimmanci a tsarin mulkin ƙasar.

  15. Peter Obi ya shigar da ƙara don ƙalubalantar zaɓen Tinubu

    Ɗan takarar shugaban ƙasa a Najeriya da aka kammala a watan jiya a ƙarƙashin jam'iyyar Labour Peter Obi, ya shigar da ƙara a hukumance, inda yake ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC nasara.

    Mista Obi ya shigar da ƙarar ne a kotun sauraron korafe-korafen zaɓen shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin.

    Hukumar zaɓen ƙasar dai ta sanar da Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka gudanar.

    Masu sa ido kan zaɓen na cikin da wajen ƙasar dai sun ce zaɓen na cike da kura-kurai.

    Hukumar INEC ta tabbatar da cewa an samu matsala wajen amfani da na'urorinta, wanda kuma ya shafi aikewa da sakamakon zaɓen zuwa shafinta na yanar gizo.

    Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar ta Labour, Yunusa Tanko, ya shaida wa BBC a ranar Talata cewa cikin abubuwan da suke ƙalubalanta dangane da zaɓen sun haɗa da rashin cancantar shiga zaɓe na ɗan takarar jam'iyyar APC.

    “Ɗan takararmu ya gabatar da ƙorafe-ƙorafe da dama gaban lauyoyi. Abu na farko shi ne rashin cancantar tsayawa zaɓe na ɗan takarar jam'iyyar APC. Kundin tsarin mulki ya yi tanadin cewa sai mutum yana da takardun makaranta kafin ya tsaya takara. Akwai kuma tuhumar da ake masa a Amurka,'' in ji mista Yunusa.

    Ya kuma ce ana aza ayar tambaya kan yadda aka gudanar da zaɓen da kuma sanar da wanda ya yi nasara da INEC ta yi.

    Peter Obi shi ya zo na uku a zaɓen da aka gudanar yayin da ɗan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya zo na biyu.

    Dukkansu dai suna kalubalantar sakamakon zaɓen saboda zargin da suka yi na cewa yana cike da kura-kurai.

  16. An gurfanar da Tukur Mamu a gaban kotu

    An gurfanar da tsohon mai shiga tsakani da 'yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna Tukur mamu a gaban kotu, kan zarge-zarge 10 da suke da alaƙa da ɗaukar nauyin ta'addanci.

    An dai kama Tukur Mamu ranar 6 ga watan Satumban 2022 a filin jirgin saman birnin Alqahira na ƙasar Masar a kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya, inda aka mayar da shi Najeriya.

    Gwamantin Najeriya dai na zargin Tukur Mamu da taimaka wa 'yan Boko Haram wajen shirya tare da ƙaddamar da hare-harensu kan 'yan ƙasar da ba su ji ba, ba su gani ba..

    Ana kuma zarginsa da karɓar maƙudan kuɗaɗe daga hannun iyalan fasinjojin jirgin ƙasan da ƙungiyar Boko Harama ta yi garkuwa da su.

    An zarge shi karɓar dala 420,000 da kuma naira miliyan 21 daga hannun iyalan fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna.

    An kuma zarge shi da ɓoye kuɗin da ake shirya ta'addanci a gidansa na jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar

    To sai dai Tukur Mamu ya musanta duka zarge-zargen da aka karanto masa a gaban kotun.

    Lauyan Tukur Mamu ya nemi da a bayar da belinsa saboda a cewarsa wanda yake karewar na fama da wani rashin lafiya da ke buƙatar tiyatar gaggawa.

    To sai dai lauyan gwamnati ya nuna rashin amincewa da belin Mamu, yana mai cewa duk ciwon da ke damun wanda ake zargin ana iya magance shi a asibitin jami'an tsaron DSS inda yake tsare.

    Haka kuma bayan doguwar muhawara alƙalin kotun mai shari'a Inyang Ekwo ya ce Tukur Mamu zai ci gaba da kasancewa a hannun jami'an DSS ɗin har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan bukatar belin nasa.

  17. Gwamnoni huɗu da zaɓe bai musu daɗi ba

    An kammala zaukan shugaban ƙasa da na gwamnoni da kuma ƴan majalisar Dokoki na tarraya da kuma jihohi a fadin Najeriya.

    Zaben ya bar wadansu ƴan siyasa cike da murna yayin da wadansu ƴan siyasar suke cike da bakin ciki, saboda yadda sakamakon ya kasance.

    A waɗansu jihohin ƙasar an samu sauyi a jam’iyyar da ke mulki inda ƴan adawa suka samu nasara a yayin da a waɗansu kuma masu mulkin ne suka samu dama domin ci gaba da jan ragama.

    Bari mu duba jihohi huɗu da suka fi jan hankali, watau Kano da Zamfara da Sokoto da kuma Plateau.

  18. Mummunar guguwa ta yi sanadiyyar ɓatan mutum fiye da 400 a Malawi

    Hukumomi a Malawi sun ce alkaluman mutanen da suka ɓata sakamakon mahaukaciyar guguwa sun kai 427, yayin da ake ci gaba da aika kayan agaji zuwa yankunan da abin ya shafa.

    Ma'aikatar kula da afkuwar bala'oi ta ƙasar, ta ce ta karɓi wani rahoto kan yankuna 15 da abin ya fi shafa a faɗin ƙasar.

    "Ya zuwa ranar Litinin, 20 ga watan Maris 2023, alkaluman mutanen da guguwar ta ɗaiɗaita sun kai 508, 244. Alkaluman waɗanda suka mutu ya kai 499, inda 1,332 kuma suka jikkata,'' in ji hukumar a cikin wata sanarwa da ta fitar.

    Ƙasashe da dama ciki har da Birtaniya da Tanzaniya da Zambiya ne suka aika tawagogin ceto domin zuwa su taimaka wa ƙasar.

    Mahaukaciyar guguwar ta afkawa Mozambique da Malawi a makon da ya gabata, karo na biyu cikin wata guda, inda ta lalata gidaje da dama da janyo ambaliya.

    Gwamnatin Malawi ta kafa tantuna sama da 500 a kudancin ƙasar, inda guguwar ta shafi larduna goma a yankin.

  19. Jihohin da jam'iyyar APC da PDP suka samu kawo yanzu

    Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta samu nasarar cinye kujerun gwamna 15 a sakamakon da aka bayyana kawo yanzu a zaɓen ranar Asabar 18 ga wata da aka gudanar a faɗin jihohin ƙasar 28.

    Yayin da jam'iyyar PDP mai hamayya ta samu kujerun gwamna takwas, sai kuma Jam'iyyar NNPP wadda ta samu kujerar gwamna ɗaya.

    Jam'iyyar APC ta samu nasara a jihohin Sokoto da Katsina da Jigawa da Gombe da Lagos da Kwara da Niger da Yobe da Nasarawa da Cross Rivers da Ebonyi da Ogun da Benue da Kaduna da kuma jihar Borno.

    Sai kuma jam'iyyar PDP da ta samu nasara a jihohin Plateau da Bauchi da Oyo da Delta da Rivers da Akwa Ibom da Zamfara da kuma jihar Taraba.

    Sai jam'iyyar NNPP da ta samu nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar Kano.

    Haka kuma hukumar zaɓen ta dakarar karɓar sakamakon jihohin Abia da Enugu, saboda rashin jituwa da aka samu tsakanin wakilan jam'iyyu a wasu ƙananan hukumomi.

    Sannan kuma hukumar ta INEC ta ayyana sakamakon jihohin Kebbi da Adamawa a matsayin wanda bai kammala ba.

    Gwamnoni a Najeriya dai na da tasiri tare da ƙarfin faɗa-a-ji a siyasar ƙasar, inda suke juya kasafin kuɗin jihohinsu.

  20. MDD za ta binciki laifukan take haƙƙin bil-adama da aka gudanar a yankin Tigray

    Nan gaba kaɗan ne a yau Hukumar kula da 'yancin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya ke shirin yin wata ganawa don duba laifukan keta haƙƙin bil-adama da aka gudanar a yankin Tigray

    Tattaunawar na zuwa ne kwana guda bayan da Amurka ta ce dukkan ɓangarori sun aikata lafin take 'yancin bil'adama a yaƙin da aka shafe tsawon shekara biyu ana gwaɓzawa

    Inda hukumar ta bukaci a gudanar da bincike da nufin hukunta waɗanda aka samu da laifi.

    Ana sa ran kwamitin masana kan harkokin bil'adama a Habasha, wadda aka ɗora wa alhakin gudanar da bincike kan laifukan cin zarafin bil'adama, zai yi wa kwamitin jawabi a taron da za a yi a birnin Geneva.

    Kwamitin ya ziyarci Addis Ababa babban birnin ƙasar a watan Yunin 2022, sai dai gwamnatin ƙasar ta ki ba su damar zuwa yankunan da rikicin ya shafa.

    Daga baya ne, hukumar ta yi kira ga ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi da su gabatar da bayanansu kan zarge-zargen cin zarafi da aka tafka a Habasha tun ɓarkewar rikicin a watan Nuwamban 2020.