Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Farouk Adamu Aliyu: Ina goyon bayan yin maslaha wajen fitar da dan takarar gwamnan Jigawa
An wallafa
Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Daya daga cikin masu neman tsayawa takarar gwamna a Jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya ya ce yana goyon bayan yin maslaha yayin fitar da 'yan takara.
Honorabul Farouk Adamu Aliyu ya shaida wa BBC cewa a matsayinsa na Musulmi bai ga laifin yin maslaha ba amma idan hakan ya gagara ya kamata a gudanar da zaben fitar da gwani "domin hakan shi ne dimokuradiyya."
Ya ce babban burninsa na zama gwamnan Jihar Jigawa shi ne sauya yadda ake gudanar da harkokin noma inda za a zamanantar da shi.