Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abis Fulani: Abin da ya sa ake yi wa masu amfani da TikTok kallon marasa tarbiyya
Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Fitaccen mai amfani da TikTok, Abubakar Bello Isma'il wanda aka fi sani Abis Fulani, ya ce manhajar tamkar hatsin-bara ne, wanda ya hada kowa da kowa.
Ya bayyana haka ne a hirarsa da BBC Hausa.
Matashin ya ce "wasu suna ganin sharrin TikTok ya fi alfaninsa yawa, amma gaskiya su suna da algorism [tsarinsu]; idan kana kallon bidiyon marasa tarbiyya, to irin wadannan bidiyon za su rika turo maka; idan kuma kana kallon bidiyon masu abin arziki, to irin wadannan bidiyon za su rika turo maka."
A cewarsa, komai ya ta'allaka ne da abin da mai amfani da manhajar ya je nema a kanta.