Haruna Abdullahi Ningi: Abin da ya sa nake nadamar yi wa Buhari waka

An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Fitaccen mawakin nan da ya yi wa 'yan siyasar Najeriya waka, Haruna Ningi, ya ce ya yi nadamar yi wa Shugaba Muhamadu Buhari waƙa ne saboda bai cika alkawuran da ya ɗauka ba.

A hirarsa da BBC Hausa, mawaƙin ya ce "har ga Allah a wani wuri na yi da-na-sani, saboda ba za ka yi da-na-sani gaba daya kan al'amarin ɗan adam ba.

"A inda muka yi da-na-sanin shi ne, abubuwan da muna da tabbacin cewa shi shugaban kasa zai yi su, to sai aka samu gazawa ta wannan ɓangaren".