Yadda aka aike da miliyoyin kudin al'umma ga iyalai da abokan tsohon shugaban Kongo

An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon

Wani babban bincike da aka gudanar a Afirka ya nuna cewa kamfanonin da iyalai da abokan tsohon shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo Joseph Kabila suka mallaka sun yi wadaka da miliyoyin dalolin 'yan kasar ta hanyar amfani da asusan bankunansu.

An tura kudaden ne a asusan bankunan kamfanonin da ke reshen Kongo na bankin BGFI.

Daga nan ne aka cire miliyoyin dala na tsabar kudin daga asusan bankunan.

Mr Kabila ne shugaban kasar a lokacin da aka cire kudaden daga bankin.

Ya ki cewa komai game da tambayoyin da muka yi masa a kan cire kudaden.

Takardun da aka kwarmata sun zarta miliyan uku kuma suna dauke da miliyoyin bayanai na fitar da kudidaga bankin BGFI (Banque Gabonaise et Française Internationale), wanda yake da rassa a kasashen Afirka da dama da kuma Faransa. Wata mujallar shafin intanet ta Faransa da ke gudanar da bincike mai suna Mediapart da kuma kungiyar Platform to Protect Whistleblowers in Africa (PPLAAF) su ne suka samo wadannan bayanai.

Shirin BBC Africa Eye ya samu wadannan shaidu, a wani bangare na hadin gwiwa da ake kira Congo Hold-up, wanda kungiyar 'yan jarida ta European Investigative Collaborations (EIC) take jagoranta.

Bincike ya aza alamomin tambaya a kan su wane ne suka ci moriyar kudaden da aka cire daga bankin da kuma ko hakan ya saba da ka'idodjin aiki.