Gwamnatin Nijar ta gargaɗi sarakunan gargajiya kan auren ƙananan 'yan mata

An wallafa

Shugaba Mohamed Bazoum na Jamhuriyar Nijar ya ƙalubalanci sarakunan gargajiya su ɗauki alƙawarin daina auren ƙananan 'yan mata, a yunƙurin da ƙasar ke yi na kawo ƙarshen al'adar auren wuri.

Shugaba Bazoum ya yi wannan kira ne a taron kwanaki biyu da gwamnatin Nijar ke gudanarwa da haɗin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya kan inganta zamantakewar al'umma.

Taron wani ɓangare ne a kokarin yaƙi da auren wuri da kuma auren dole ga 'ya'ya mata.

Sannan taron zai lalubo hanyoyin bunƙasa ilimin 'yan mata da nufin kyautata matsayin rayuwarsu.

Mohamed Bazoum ya ce a kowace al'ummah sarakunan gargajiya da sauran masu rike da mukaman gargajiya suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen kawo sauyi a cikin al'umma.

Shugaban ya ce babu shakka kowa ya san tsarin gidan masarautu, don haka a wannan lokaci da ake kokarin kawar da wannan dabi'a dole gyara ya soma daga cikin gida.

Ya kuma bayar da misali da matakin shaharar sarakuna da kuma nauyin da ya rataya a wuyansu wajen taimaka wa zamantakewar al'umma.

Hakkin 'ya'ya mata

Nijar ta kasance cikin jerin kasahen duniya da yanzu haka ta shiga sahun laluben hanyoyin kawar da matsalar auren wuri da inganta rayuwar 'ya'ya mata.

Wannan dalili ne ya sa take ta kirkirar shirye-shiryen da za su inganta rayuwar 'ya'ya mata masu dorewa.

Wata matashiya da ke cikin mahalarta taron ta shaida wa BBC cewa burinta shi ne ganin rayuwar yara mata ta inganta, kuma su kasance suna samun ilimi cikin kwanciyar hankali.

Matsahiyar ta kuma jaddada kira ga inganta rayuwar mata da kare hakkokinsu a kowanne bangare na rayuwa.

Alfannu gina mata

Sarkin Damagaram, Mai martaba Abubakar Umaru Sanda na daga cikin mahalarta taron, kuma ya shaida wa BBC cewa suna kan kokari kuma za su ci gaba da yin haka don kare rayuwar 'ya'ya mata.

Ya kuma shaida cewa wasu mutane sun fahimci alfanu kuma sun aminta da haka, amma wasu na nuna turjiya.

Sannan Mai Martaba Abubakar Umaru Sanda ya ce, irin wannan taro da yake an hada mutane daga bangarori da dama zai taimaka wajen kawo karshen matsalar.

A Nijar wakilan al'umma da sarakuna na sahun gaba wajen yaki da wannan dabi'a, dalilan da ya sa Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin ƙasar shirya irin wannan taro domin isar da sakonni zuwa ga al'umomi.