Lafiya Zinariya: Rigakafin sankarar bakin mahaifa na ba da kariya 90 cikin 100

An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin sauraren shirin:

Kwayar cutar Human Papillomavirus ce ke haddasa kusan dukkan sankarar bakin mahaifa, kuma masu bincike sun ce rigakafinta na bayar da kariya.

Haka kuma cutar ita ce cutar kansa ta hudu da ta fi addabar mata a fadin duniya.

Cutar sankarar bakin mahaifa na yin ajalin mata 300,000 duk shekara a duniya.

Rigakafin yana bayar da kariya ne wajen hana kamuwa da kwayar cutar, amma ba ya wani tasiri ga wadda ta riga ta kamu da cutar.

Alkaluman su ne irinsu na farko da ke nuna sakamako na zahiri.

Binciken wanda aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta The Lancet, ya duba abin da ya faru bayan an bai wa wasu yara mata rigakafin a Burtaniya, a shekarar 2008.

Sakamakon binciken ya nuna cewa an samu raguwar kashi 87 cikin dari na sankarar bakin mahaifa, a tsakanin matan da a yanzu suke cikin shekarunsu na ashirin a duniya.

An dai bai wa matan 'yar kasar Ingila, rigakafin ne a lokacin suna da shekara 11 zuwa 13 duniya.

Haka kuma a kasar, an soma bai wa yara maza irin wannan rigakafin tun shekarar 2019.

Masu bincike a Burtaniya sun yi maraba da sakamakon, inda suka bayyana shi a matsayin wani abin tarihi.

Kimanin kasashe dari na duniya sun fara amfani da rigakafin, a karkashin wani shiri na hukumar lafiya ta duniya, WHO, a yunkurin neman kawar da cutar daga doron kasa.