Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zamantakewa: Me ya sa ake tsangwamar zawarawa a cikin al'umma?
Latsa hoton sama domin kallon shirin
Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.
A wannan kashi na 17, shirin ya yi duba ne kan yadda mu'amala take tsakanin zawarawa da al'umma.
Gyaran zamantakewa a cikin al'umma ya shafi dukkan fannonin rayuwa, ba sai na gidan aure da kawance da surukuta ba kawai.
Muzantawa ko bai wa kalmar bazawara wata ma'ana mara kyau ita ce tsangwama ta farko da 'ya mace da aurenta ya mutu ke fama da shi.
Kamar yadda na yi alkawari, wannan makon ma ci gaban na makon da ya gabata ne wato batun zawarci.
Wannan makon mun tattauna ne da Dr Maikano, masanin halayyar dan adam kuma malami a Jami’ar Bayero da Hajiya Maryam Dahira.
Sannan mun yi waiwaye kan wata hira da muka taba yi da Laymah Ali Othman da ta ce zawarci ba karshen rayuwar mace ba ne.
“Ni kwarin gwiwa ma ya kara min da kuma iya tsayuwa da kafafuna,” kamar yadda ta ce.
Dr Maikano ya ce ya zama wajibi a kan al’umma ta kula da rayuwar bazawara da bukatunta da kare mutuncinta.
Ita kuwa Hajiya Dahira cewa ta yi iyaye ya kamata a ce sun ajiye jin zafin mutuwar auren ‘ya’yansu sun taimaki ‘ya’yan da kaddarar ta fada musu wajen nuna tausayawa da jan su a jiki da tallafa musu.