Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Shettima Habib
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon
Fitaccen malamin addinin musuluncin a Najeriya Sheikh Shettima, ya ce duk da bai yi karatun boko ba amma ya taimakawa masu bincike a cibiyoyin ilimi a Ingila da Jamus, musamman kan babban aikin fassara Al Kur’ani mai tsarki zuwa harshen Kanuri.
Ya ce tafi Ingila sau uku kuma turawan ƙasar da suka yi wa Najeriya mulkin mallaka ne suka gayyace shi zuwa Landan.
Malamin ya ce ya taimaka masu kan binciken da suke yi a Kwalejin nazarin zamantakewar kasashen gabashin duniya da na Afrika wato School of Oriental and African Studies da ke tsakiyar Landan.
Ya kuma kai ziyara Jamus sau shida kan aikin fassarar Al Kur’ani mai tsarki da harshen Kanuri a Jami’ar Hamburg.