Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ƙarancin abinci ke shafar yara ƙanana a arewacin Najeriya
Latsa hoton sama domin sauraren shirin
Najeriya mutane sama da miliyan 80 ne kidididga ta nuna suna fama da matsanancin talauci a cikin kasar, wanda kuma za a iya kimantasu da kashi 40 cikin 100 na yawan al'ummar kasar.
Ranar 16 ga watan Oktoba ne Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware a matsayin ranar abinci ta duniya.
To sai dai bikin na zuwa a daidai lokacin da aka samu karuwar miliyoyin mutane da ke fuskantar rashin abinci yawanci sakamkon barin muhallansu saboda tashe-tashen hankula a sassa daban-daban na duniya.
Shiyyar arewa-maso-gabashin Najeriya na daga cikin yankunan duniya da ke da adadi mai yawa na mutanen da ke fuskantar matsalar rashin isasshen abinci sakamakon sama da shekaru 10 da yankin ya kwashe cikin rikici.
Haruna Shehu Tangaza ya duba yadda rashin abinci ke shafar mutane musamman kananan yara a shiyyar arewa-maso-gabashin Najeriya da kuma kokarin da ake na tallafa musu.