Hira da tsohon Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Farfesa Attahiru Muhammad Jega

An wallafa

Latsa nan domin sauraren hirar:

Tsohon Shugaban Hukumar Zaben Najeriya,wato INEC, Farfesa Attahiru Muhammad Jega, ya ce duka manyan jam'iyyun kasar na APC da PDP ba su cancanci ci gaba da jagorancin kasar mafi yawan jama'a a Nahiyar Africa bayan zaben 2023 ba; saboda abin da ya kira muguwar rawar da suka taka cikin shekaru 20 din da suka wuce.

A cikin wata kebantaciyyar hira da sashen Hausa na BBC, fitaccen malamin jami'ar, ya ce kasar na bukatar wani zubin shugabanni na daban da akidunsu suka yi hannun riga da na jam'iyyun biyu, kafin ta fita daga cikin matsalolin da take ciki. Sai dai duka jam'iyyun biyu sun musanta kalaman nasa.

A hirar da ya yi da Haruna Shehu Tangaza, Farfesa Attahiru Muhammad Jega ya fara da bayyana dalilansa na rikidewa zuwa dan siyasa: