Mai shekaru kusan 73 da ya kammala karatun digiri na biyu a fannin adabin Larabci

An wallafa

Wani mutum mai shekaru kusan saba’in ya kammala karatun digiri na biyu a fannin adabin Larabci.

Mallam Yusha'u Yusuf ya shaida wa BBC cewar ya fara karatun zamani a lokacin yana da shekara 20 sannan bai fara karatun digirinsa na farko ba sai a 2012 bayan ya yi ritaya daga aiki.

Duk da wadannan shekaru na Mallam Yusha'u Yusuf da kuma aikin limanci a masallacin Juma'a na Bompai, har yanzu bai fitar da rai cewar zai koma makaranta don digiri na uku ba.