Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matsalar tsaro: Ƴan bindiga sun hallaka mutum 1,031 a jihohi uku a Najeriya
Wani sabon rahoto da kamfanin Beacon Consulting mai lura da al'amuran tsaro da bayanan sirri a Najeriya ya fitar ya nuna cewa jihohin Kebbi da Zamfara da Neja ke kan gaba a matsalolin tsaro da hare-haren ƴan bindiga, inda aka bayar da rahoton hallaka mutane 1,031 a cikin watan Yunin shekarar 2021.
Rahoton ya bayyana cewa a jihar Zamfara an hallaka akalla mutane 275, yayin da a jihar Kebbi aka hallaka 93, sai kuma jihar Neja inda aka hallaka mutane 91.
An kuma samu ƙaruwar sace-sace jama'a sau 205 a bayanan da aka tattara daga jihohi 34 na ƙasar a cikin watan na Yuni.
A tattaunawarsa da BBC, Shugaban kamfanin na Beacon wanda ya fitar da wadannan alkaluma a cikin rahoton, Dakta Kabir Adamu ya bayyana cewa a ƙarƙashin rahoton sun nuna muhimmancin tabbatar da tsaro a bisa tsari na tafiyar da tsaron, wanda abu ne mai matuƙar muhimmanci.
Alkaluman watan Yuni sun nuna cewa Arewa Maso Yamma ya fi fama da matsalar tsaro, sai kuma Kudu maso Yamma, daga kuma Arewa ta Tsakiya ta zo ta uku,'' in ji Dakta Kabir.
''A takaice kusan matsalolin na tsaro sun fi yawa a waɗannan yankuna uku, sai daga baya aka zo kuma Kudu Maso Gabas da yankin Neja Delta da kuma Arewa Maso Gabas wanda shi ne ya bai wa mutane mamaki saboda Boko Haram, amma dai alkaluman sun nuna ba haka bane''.
Rahoto dai in ji masanin ya yi amfani da alƙaluma da aka wallafa a shafukan jaridu da na sada zumunta, wanda kuma suka yi amfani da hanyoyi sahihai na kimiyyar laifuka wato 'Criminology' wurin tantance su kafin su saka cikin rumbun alƙaluma don fitar da bayanai a ko wane wata.
''Matsalar tsaro na shafar tattalin arziki, kamfanoni da dama da ke son zuwa zuba jari ba sa samun irin wadannan bayanai da kuma tsari na tsaro wanda zai taimaka musu, shi yasa muka fara wallafa wannan don taimaka wa jama'a da kamfanonin da ke bukatar tsaron,'' Dakta Kabir ya kara jaddadawa.
Shawarwarin da ke kunshe cikin rahoton
Rahoton dai ya kunshi shawarwari da dama game da yadda za a shawo kan matsalolin tsaro a kowane ɓangare na Najeriya, kamar yadda Dakta Kabir Adamu ya yi karin bayani.
Ya ce, shawarwarin da suka bayar na tattare da matsalolin tsaron da ake fama da su, don haka ya kamata gwamnatin tarayya ta dube su da idon basira, amma ba amfani da karfin soja bane kaɗai hanyar magance matsalolin.
''Mun kawo shawarar amfani da tattaunawa wadda mun fahimci cewa gwamnatin tarayya ta fara yi a cikin watan Yuni, baya ga hakan mun shawarci gwamnoni cewa su ma su ci gaba da wannan tattaunawar tare da ƙungiyoyin matasa a cikin tsarin da ake da shi, don yawanci waɗannan ƙungiyoyi da ke aikata laifuka matasa ne ake amfani da su, in ji shi .
''Idan ana tattaunawa ba a saka su a ciki ba hakan na nufin an ware su kenan, kuma an bai wa wadannan ƙungiyoyin dama su janyo hankulansu su rika amfani da su wurin biyan bukatarsu na matsalar tsaron kasa''.
Akwai kuma bukatar su kan su gwamnonin na jihohin Arewa Maso yamma, da Arewa Ta Tsakiya su hada kawunansu saboda matsalar ƴan bundiga da suke cikin daji - dazukan da duk sun ratsa ta cikin yankin Arewa Maso Yamma da kuma tsakiyar Najeriya, don haka in ji masanin sai gwamnonin sun hada kawunansu sun fito da tsari na bai ɗaya kafin a cimma nasara,.
''Ita kan ta gwamnatin tarayar tana da hakki a kan wannan, ganin cewa gwamnonin ba su da jami'an gwamnati masu makamai, don haka duk tsarin da gwamnonin za su yi dole sai gwamnatin tarayya ta tsaya musu,'' Dakta Kabir ya jaddada.
Batun tabarbarewar tattalin arziki da rashin aikin yi da talauci da ya yi katutu a jihohin Najeriyar, na daga cikin abubuwan da wannan rahoto ya kunsa in ji masananin, da hakan ya bai wa gwamnonin shawara cewa su fito da tsare-tsare kan yadda za su rage waɗannan matsaloli da yawancin al'ummarsu ke fama da shi.
''Idan aka yi haka zai rage duk wata dama da irin waɗannna ƙungiyoui masu rike da makamai ke da shi na haɗa kai da tabbatar da cewa suna samun damar amfani da matasa su shiga cikinsu,'' in ji Kabir.
Jihohin Gombe da Bauchi sun fita zakka?
Rahoton dai ya bayyana karara cewa akwai matsalolin tsaro a jihohi 34 na Najeriya ne wanda hakan ke nufin akwai wasu johohi biyu har ba babban birnin tarayya Abuja da suka fita zakka a cikin jerin masu fama da waɗannan matsalolin
Sai dai Dakta Kabir ya yi karin bayanin cewa, jihohin Gombe da Bauchi ne rahoton bai samu wasu matsaloli na tsaro a rumbun tattara bayanan na su ba, amma ba haka yana nufin babu wata matsala ba ne.
''Ba mu ga matsaloli na tsaro ya shafe jihohin Bauchi da Gombe daga watan na Yuni ba, abubuwan da muke nazarta guda biyar da hanyoyi da muke bi na tabbatar da cewa matsalar tsaro ta shiga cikin rumbun ajiye alkaluma bai samu wani labari daga jihohin da suka shiga cikin rumbun bayanan da muke amfani da su a ko wane wata ba.''
Ya kuma ce da dama za su yi mamaki cewa rahoton bai ambato yankin arewa maso gabashin Najeriya ba, musamman jihar Borno wacce ta yi ƙaurin suna wajen ba da matsalolin hare-haren ƙungiyar Boko Haram, wanda ya ce duka batun haka yake idan aka duba hanyoyin da rahoton ya bi wajen bincika da kuma gano matsalolin tsaron kowane yankin daga cikin watan Yuni.
Yawan makamai a hannun ƴan bindiga
Wata babbar matsala da masanin ya bayyana ke kunshe cikin wannan rahoto ita ce batun makamai da yanzu suka yi matuƙar yawa a hannun ƴan bindiga, wanda ya ce ƙarin wata babbar barazana ce da kuma cikas a ƙoƙarin shawo ka matsalar.
''Hakan bai kamata ba, shi yasa muka kawo shawarwari a inganta hanyoyin da ake bi na janye wadannan makamai daga hannun ɓata-gari, ciki har da kokarin haɗin-kai tsakanin gwamnatin Najeriya da na ƙasashen da ke kewaye da ita, kan yadda za a inganta tsaron kan iyakokin ƙasashen,'' in ji Dakta Kabir.
''Kana akwai bukatar a lura da jin dadi da kyautata aikin jami'an hukumar lura da shige da fice ta ƙasa, don tabbatar da sun sa ido kan yadda ake shigowa da irin wadannan makaman cikin ƙasa''.
Samun haɗin-kan mazauna yankunan da ke fama da matsalar tsaro da ya kamata jami'an tsaro su yi na da matukar muhimmanci wajen tattara bayan sirri da za su iya taimakawa wajen yadda za a gano bakin zaren, in ji masanin.
Ya kuma ce hakan zai taimaka matuka wajen rage karuwar kalubalen da ake fuskanta a kusan ko ina a faɗin ƙasar.