Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tarihin yadda Hausawa suka tare a Ibadan
An wallafa
Latsa hoton sama homin sauraren hirar
Hausawa na daya daga cikin al’ummar Afirka ta yamma da ke da yawan yawo a sassan duniya musamman sakamakon fatauci.
Wani yanki da Hausawa suka yi wa tsinke shi ne kudancin Najeriya musamman kudu maso yammaci wato yankin Yarabawa.
Birnin Badin na jihar Oyo na daya daga cikin wurare na farko-farko da Hausawan suka yi wa tsinke.
A hirarsa da Yusuf Ibrahim Yakasai, Alhaji Hassan Isiyaka wanda shi ne Sarkin Hausawan Sabo da ke birnin na Badin ya ce Hausawa sun je birnin ne shekaru kusan 200.