Ku San Malamanku tare da Sheikh Abdullahi Uwais Limanci

An wallafa

Ana daukar Sheikh Abdullhi Uwais Limanci a matsayin daya daga manyan malamai a Kano da ba a fiya jin duriyarsu ba.

Sheikh Abdullahi ya kasance malamin da manyan malmai a Kano ke zuwa wajensa domin daukar karatu.

A tsawon yini, Sheikh Abdullahi Uwais yana shafe kusan sa'a goma yana karantarwa a kowace rana.

Malamin bai yi karatun zamani ba, amma dai ya ce ya ringa bibiyar manhajoji da ake amfani da su a makarantu na zamani, har ma yana taimaka wa wadanda suke karatu a irin wadancan makakarantun.

Duk da cewa bai yi ilimin zamani ba, Sheikh Abdullahi Uwais ƙwararre ne a ilimin lissafi da tattalin arziki da wasu fannonin na ilimin zamani.

Malamin ya kasance madogara da ake tuntuɓa daga jami'o'i kan wasu mas'aloli da suka shafi darusan addinin Musulunci da harshen Larabci.