Abin da ya sa ba za a ga watan Shawwal ba sai ranar Laraba - Masani

An wallafa

Al'ummar Musulmi a Najeriya za su fara duban watan Shawwal ne daga gobe Talata a cewar Majalisar Koli kan harkokin addinin Musulunci ta kasar.

Kodayake, a bana azumin na iya kasancewa tsawon kwana 30.

Simwal Usman Jibril, mamba a kwamitin duban wata a Najeriya, ya yi mana bayani kan dalilan da suka sanya da wahala a ga wata ranar Talata.