Lafiya Zinariya: Halin da masu fama da larurar ciwon suga suke shiga

An wallafa

A wannan makon filinmu na Lafiya Zinariya ya tattauna da wasu mata da suke fama da larurar ciwon suga.

Matan sun shaida wa BBC shekarun da suka kwashe suna fama da cutar da kuma shawarwarin da likitoci suka ba su kan yadda za su takaita tasirin larurar.

Kazalika wata likita ta yi karin haske kan nau'ukan abincin da ya kamata masu fama da lurarar ta ciwon suga su rika ci.