Coronavirus variant: 'Akwai yiwuwar ɓullar sabon nau'in cutar a Najeriya

An wallafa

Shugaban hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa ta Afrika, John Nkengasong, ya bayyana cewa akwai yiwuwar an samu ɓullar sabon nau'in cutar korona a Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ne ya ruwaito shugaban inda yake cewa akwai buƙatar a ƙara zurfafa bincike kan lamarin.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Birtaniya da Afrika Ta Kudu suka bayar da rahoton cewa an samu sabuwar nau'in cutar korona da ake wa laƙabi da SARS-Cov-2- virus, cutar da ake ganin ta fi saurin yaɗuwa, wanda hakan ya ja aka ƙara saka dokoki masu tsauri na tafiye-tafiye da kuma kawo cikas a kasuwannin duniya.

"Nau'in ta Afrika Ta Kudu ya sha bam-ban da na Birtaniya," kamar yadda John Nkengasong ya shaida a taron manema labarai a birnin Addis Ababa na Ethiopia.

"Irin wanda muke gani a Najeriya, ba mu da cikakkun bayanai a kansa, kuma yana kama da 501.V2," inda yake alaƙantasa da sabon nau'in da aka gani a Afrika Ta Kudu a ranar 18 ga watan Disamba.

Mista Nkengasong ya bayyana cewa hukumomin daƙile cututtuka masu yaɗuwa na Afrika da Najeriya za su ƙara yin gwajin samfari daban-daban na cutar domin zurfafa bincike.

A Najeriya, adadin mutanen da suka kamu da cutar tun bayan ɓullarta zuwa ranar Laraba ya kai 80,922, yayin da 69,274 suka warke aka kuma samu asarar rayuka 1,236.

Jihohi da dama na ƙasar na ɗaukar sabbin matakai domin daƙile yaɗuwar cutar, inda ko a farkon makon nan sai da gwamnatin tarayyar ƙasar ta sanar da rufe wuraren shaƙatawa da makarantu da na sayar da abinci da kuma ƙayyade ma'aikatan da za su je wuraren aiki.