Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyon auren Sulaiman Panshekara da Ba'amurkiya a Kano
An ɗaura auren matashin nan ɗan asalin Jihar Kano Isa Sulaiman Panshekara mai shekara 26 da sahibarsa Ba'amurkiya.
Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta Tsakiya, shi ne waliyyin amarya Janine Sanchez.
Ɗumbin mutane ne suka taru a masallacin Jumma'a na Gasau da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso, domin shaida ɗaurin auren da aka jima ana dako, bayan shafe tsawon lokaci suna shan soyayya.
Matashin ya biya zunzurutun kuɗi har Naira Dubu 50 a matsayin sadaki lakadan ba ajalan ba.
Mahaifin ango Mallam Sulaiman, ya shaida wa BBC cewa ya amince a ɗaura auren ne bayan amincewa da dukkanin sharuɗɗan da ya gindaya kafin ya bayar da ɗansa.
Daga cikin manyan baƙin da suka halarci ɗaurin auren har da Sanata Shehu Sani, tsohon Sanata mai wakilar jihar Kaduna a Majalisar Dattawa ta Najeriya, da kuma shugaban ƙaramar hukumar ta Kumbotso.
Abin jira a gani shi ne lokacin da Ango zai bi Amarya, duba da cewa jim kaɗan bayan ɗaura aure uban ango ya ce ɗansa zai ci gaba da zama da shi, sai dai kuma shi angon ya ce za a jira ne zuwa lokacin da za a kammala tattara takardun bizarsa,