Matashin da ke bayar da hayar kaya a Kano

An wallafa

Latsa hoton da ke don kallon yadda samari da 'yan mata ke zaɓar kayan sakawa na haya

Matashi Ibrahim Bature Yakubu ya shaida wa BBC cewa ya fara harkar bayar da hayar tufafin sakawa ne saboda abokansa.

Haifaffe kuma mazaunin birnin Kano a arewacin Najeriya, Ibrahim ya ce ya fara harkar ne da kaya guda uku kacal.

Ya zuwa yanzu, yana da kayan mata da na maza masu yawa da ake karɓa haya kuma a ba shi kuɗi.

Za ku ga yadda samari da 'yan mata ke zaɓa su darje.

Daukar bidiyo: Yusuf Yakasai

Tacewa: Fatima Othman