Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kano: Yadda ɗaliban sakandare a Najeriya suka koma makarantu
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon
Bayan shafe kusan wata bakwai ɗalibai na zaune a gida ba tare da zuwa makarantu ba sakamakon ɓarkewar annobar cutar korona, a yanzu an sake buɗe su a faɗin Najeriya.
Wakilimmu a Jihar Kano, Khalifa Shehu Dokaji ya ziyarci wata makaranta domin ganin yadda abubuwa ke tafiya musamman na bin matakan daƙile yaɗuwar cutar tsakanin ɗalibai.