Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyo: Mece ce makomar siyasar ubangida a Najeriya?
An wallafa
Ku latsa hoton da ke ƙasa don kallon bidiyon:
A wannan bidiyon BBC ta yi duba kan siyasar ubangida a Najeriya wadda aka shafe shekara da shekaru ana yin ta a ƙasar.
Masana harkokin siyasa na ganin siyasar ubangida ce take tarnaƙi game da gudanar da mulki na gari a ƙasar.
Siyasar ubangida dai ba sabuwar aba ba ce a Najeriya, sai dai galibin lokuta ba a wanyewa lafiya idan muradun ubangidan da na yaronsa suka ci karo da juna, lamarin da kan yi mummunan tasiri kan yadda ake tafiyar da mulki da kuma samar da abubuwan more rayuwa ga talaka.